12/08/2026
Pantami, Zullum sun halarci taron Muslim World League da JIBWIS Nigeria ta Jagoranta a Abuja.
Ƙungiyar Muslim World League, tare da haɗin gwiwar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) Nigeria, ta buɗe babban taron ƙasa da ƙasa kan tsaron ƙasa da hanyoyin tabbatar da dorewar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a Abuja.
An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Muslim World League, Sheikh Dr. Muhammad bin Abdulkarim Al-Issa, inda manyan shugabannin ƙasa, malamai, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki s**a hallara domin tattauna matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Daga cikin manyan bakin da s**a halarci taron akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Haka kuma, gwamnonin Borno, Sokoto, Kaduna da Jigawa sun halarci taron, tare da Mataimakan Gwamnonin Yobe da Katsina.
Taron ya samu halartar wasu ministocin gwamnatin tarayya, ciki har da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris; Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate; da Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu.
Haka kuma, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, na daga cikin manyan baki da s**a halarci taron.
Daga cikin malaman addini da shugabannin ƙungiyoyin musulmi da s**a samu halarta akwai Hon. Ali Isah Jesy; Sheikh Dalhat Abubakar Hakimi, wanda ya wakilci Sheikh Sanni Yahaya Jingir; Sheikh Karibullah Nasiru Kabara; Dr. Khalid Aliyu, Babban Sakataren Jama’atu Nasril Islam (JNI); da Dr. Ahmed Mahmoud Gumi.
Sarakunan gargajiya ma sun samu wakilci a taron, ciki har da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Sarkin Bida, Sarkin Hadejia da Sarkin Maradun.
A yayin taron, mahalarta sun mayar da hankali kan matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta, tare da tattauna hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kan al’umma da kare tsaron ƙasa.
Masu shirya taron sun bayyana cewa ingantaccen tsaro na daga cikin muhimman ginshiƙan da za su taimaka wajen samun dorewar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a Najeriya.
Taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban domin samar da tattaunawa da shawarwari kan hanyoyin magance matsalolin tsaro da ƙarfafa zaman lafiya a ƙasar.