15/05/2026
Bari ku ji abinda gwamnan jihar Ogun yayi. Ranar 6 ga watan May (yau kwana 8 kenan), Gwamnan jihar wato Dapo Abiodun ya ƙaddamar da buɗe sabon gidan wutar lantarki mallakin jihar mai ƙarfin Megawatt 4 a cikin garin Abeokuta wanda zai ke amfani da iskar Gas (wato Gas-fired independent Power Plant), sannan ya sake ƙaddamar da Onijanganjangan Self-sufficient Energy Plant mai ƙarfin 34 Megawatt wanda baki ɗaya ya miƙa ragamar kula da wuraren a hannun Ogun State Electricity Regulatory Commission. Dan ka gane karatun yadda ya k**ata, a dunƙule ina nufin gwamnatin jihar Ogun ta ƙaddamar da personal wurin samar da wutar lantarki mai ƙarfin 38 Megawatt wanda zai ke samarwa da jihar wutar lantarki 24/7 kai tsaye zuwa gidajen al'ummar jihar only banda kamfanoni. Idan baka gane ya ƙarfin 38 Megawatt yake ba, to ana nufin duk 1 Megawatt zata iya ɗaukar lodin duk wani electrical appliances na a ƙalla gidaje 1,800 tun daga kan Firji, TV, AC, dutsen guga, heater, fanka da ƙwayaye💡 iri daban-daban. Chairman gidaje 1,800 fa ba mutane 1,800 ba ake nufi ya k**ata ka san wannan 😒. Duk inda ka samu gidaje 1,800, a ƙalla za ka iya samun mutane dubu 250 averagely.
Wannan wutar lantarkin fa da ya samarwa jihar sa, still yanzu haka akwai sabon Private Generation Station na wutar lantarki wanda baban Devido yake ginawa a jihar wanda a ƙarshen shekarar nan za'a buɗe shi. Still kuma daman jihar Ogun ɗin tana da Papalanto Generation Station ƙarƙashin kulawar Niger Delta Power Holdings Company wanda yake samarwa da Nigeria wutar lantarki mai ƙarfin 754 Megawatt. Dalilin waɗannan wuraren samar da wutar lantarkin ne yasa jihar Ogun yanzu haka ita ce jiha ta biyu a yawan kamfanoni a Nigeria idan ka ɗauke jihar Lagos. A dunƙule dai, a yayin da wasu jihohin suke ta gogayya wajen ganin sun samarwa kansu abubuwan dogaro da kai saboda al'ummar su su zama purely independent, mu kuwa idan ka shigo jihohin mu daga auren zawarawa sai rabon abinci da tabarmi sannan a gayyaci Rarara da su Ado Gwanja da