01/10/2025
A yau, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf (AKY), ya taya al’ummar Najeriya murnar zagayowar ranar ’yancin kai ta ƙasa.
A cikin saƙon murnar bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, gwamnan ya bayyana cewa:
“A wannan rana mai tarihi, ina taya al’ummar Najeriya murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai. A yau, muna taya juna murna tare da tuba ga Allah domin cigaba da kare hadin kan ƙasarmu. Ina yi wa kowa fatan alheri, kuma ina kira gare mu gaba ɗaya da mu ci gaba da sadaukar da kai wajen gina ƙasar da kowa zai ji daɗin rayuwa a cikinta.”
Gwamna AKY ya ƙara da cewa haɗin kai, juriya, da kishin ƙasa su ne ginshiƙai da za su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
Ya kuma roƙi al’ummar ƙasar da su ci gaba da yi wa ƙasa addu’a tare da rungumar zaman lafiya, kishin kasa da adalci.
Happy Independence Day, Nigeria! 🇳🇬