GCHN Updates24

  • Home
  • GCHN Updates24

GCHN Updates24 Mu na kawo muku sahihan labarai, kuma da zafi zafin su, domin sanin halin da duniya take ciki.a Yau

Yadda matasa a jahar sokoto suke gudanar da zanga zanga akan asake Dahiru Mai barewa da akakai gidan yari saboda yayi ba...
25/08/2026

Yadda matasa a jahar sokoto suke gudanar da zanga zanga akan asake Dahiru Mai barewa da akakai gidan yari saboda yayi barazanar kashe malam addini murtala asada dakuma sheikh Musa lukuwa bisa zargin su da zagin mahaifan Annabi Muhammad s a w a jihar sakoto

An yanka raƙuma 1,538 don taimakawa marasa ƙarfi a Somalia albarkacin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W
25/08/2026

An yanka raƙuma 1,538 don taimakawa marasa ƙarfi a Somalia albarkacin Maulidin Annabi Muhammad S.A.W

DA DUMI DUMI: Wani abun al ajabi yafaru a jahar Abia state a Tarayyar Najeriya anyi Aure wani mutum da ya aure hassana d...
25/08/2026

DA DUMI DUMI: Wani abun al ajabi yafaru a jahar Abia state a Tarayyar Najeriya anyi Aure wani mutum da ya aure hassana da usaina uwa daya uba daya

Mai Zaku Ce?

Amnesty ta buƙaci ceto masu ibada da aka sace a masallacin NejaMinna – Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty Interna...
25/08/2026

Amnesty ta buƙaci ceto masu ibada da aka sace a masallacin Neja

Minna – Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gaggauta ceto masu ibada da aka yi garkuwa da su yayin sallar Juma'a a wani masallaci da ke ƙauyen Kpenya, a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda hare-hare da garkuwa da mutane ke ƙara ƙamari a yankin Borgu-Kainji, tare da buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da tsaron rayuka da kuma ceto waɗanda aka sace.

DA DUMI DUMI: Karo na biyu: Ansake Sumar Da Liman Malam Sadi Ginau A Jihar Sokoto Bayan Sallar Magaribar Wannan Rana Sak...
25/08/2026

DA DUMI DUMI: Karo na biyu: Ansake Sumar Da Liman Malam Sadi Ginau A Jihar Sokoto Bayan Sallar Magaribar Wannan Rana Sakamakon Tallar Takarar Muslims Muslims Daya Fara Ana Idar Da Salla, Acewa Ganau Sunce Kafin Yafara Maganar Zaben Muslims Ticket Din Ya Fara Dacewa Wannan Zaben Na 2027 Sun Samu Umurni Daga Shugaban Izala Na Plato Cewa Ayi APC Daga Sama Har Kasa, Nan Take Matasa S**a Fara Ihun Karyane,Daga Bisani Sai Jifa Da Duka, Babu Jimawa Jami an Tsaro S**a Kawo Dauki.

Mai Zaku Ce?

Gwamnatin Tarayya na Shirin Dawo da Aikin Hako Danyen Mai a KolmaniBAUCHI, NIGERIA — Gwamnatin Tarayya na shirin dawo da...
25/08/2026

Gwamnatin Tarayya na Shirin Dawo da Aikin Hako Danyen Mai a Kolmani

BAUCHI, NIGERIA — Gwamnatin Tarayya na shirin dawo da ci gaba da aikin hako danyen man fetur a rijiyar Kolmani, da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe.

Shugaban Hukumar Rarraba Kudaden Tarayya (RMAFC), Dr. Mohammed Bello Shehu, ya kai ziyarar gani da ido a wurin da ake gudanar da aikin, tare da rakiyar Kwamishinan Albarkatun Kasa na Jihar Bauchi, Barr. Ahmad Bello Maiwada (Geo Barrister).

A yayin ziyarar, Dr. Mohammed Bello Shehu ya bayyana cewa ana sa ran dawo da ci gaba da aikin hako danyen man fetur a Kolmani nan ba da jimawa ba.

Ya ce wannan na daga cikin manyan dalilan da s**a sanya s**a kai ziyarar domin duba halin da wurin yake ciki da kuma ci gaban aikin.

Aikin Kolmani na daga cikin manyan ayyukan neman albarkatun man fetur da ake sa ran za su kara bunkasa tattalin arziki da samar da karin damammakin aiki a yankin Arewa.

Rahoton ya zo ne a matsayin wani sabon fata ga al'ummar Arewa, musamman masu fatan ganin an fara amfani da albarkatun man fetur na yankin wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban al'umma.

Wannan rahoto ba shi da alaka da siyasa; bayani ne kan ci gaban aikin da kuma fata na ganin an kammala aikin cikin nasara.

Muna fatan Allah Ya tabbatar da wannan aiki

Sai dai mutane da yawa na ganin wannan a matsayin yaudara saboda ganin lokacin zabe yagabato

Ku menene raayinku

— GCHNUPADATES24

Barista Abba Hikima Ya Yi Maraba da Sakin Maryam ShehuKANO, — Barista Abba Hikima ya bayyana farin cikinsa kan sakin Mar...
25/08/2026

Barista Abba Hikima Ya Yi Maraba da Sakin Maryam Shehu

KANO, — Barista Abba Hikima ya bayyana farin cikinsa kan sakin Maryam Shehu, tare da miƙa godiya ga dukkan waɗanda s**a taka rawa wajen ganin an tabbatar da ’yancinta.

Barista Hikima ya nuna godiya ta musamman ga Omoyele Sowore, tare da yaba wa Malam Hamza Nuhu Dantani da Deji Adeyanju, da lauyoyi, ’yan jarida, masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam da sauran ’yan Najeriya da s**a ɗaga murya wajen neman a saki Maryam.

A cewarsa, sakin Maryam Shehu wata nasara ce da ta samu sakamakon haɗin kai da jajircewar mutane da dama waɗanda s**a tsaya tsayin daka wajen neman ’yancinta.

Ya bayyana fatan cewa wannan mataki zai ƙara ƙarfafa gwiwar masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam da kuma tabbatar da muhimmancin bin doka da adalci.

GCHN UPDAT 24

TAYA AL’UMMAR MUSULMI MURNAR MAULUDI ﷺ Kafin aiko da Manzon Allah ﷺ, aljanu sun kasance suna neman jin labaran sama. Amm...
25/08/2026

TAYA AL’UMMAR MUSULMI MURNAR MAULUDI ﷺ

Kafin aiko da Manzon Allah ﷺ, aljanu sun kasance suna neman jin labaran sama. Amma da Allah Ya so a kare abin da ke cikin sama, sai aka sanya masu gadi da shauhun wuta domin kada su sake samun damar satar jin labarin.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

﴿وَأَنَّا لَا نَدْرِي أَشَرٌّ أُرِيدَ بِمَن فِي الْأَرْضِ أَمْ أَرَادَ بِهِمْ رَبُّهُمْ رَشَدًا﴾

Ma’ana: “Ba mu sani ba, shin an nufi waɗanda suke cikin ƙasa da sharri ne, ko kuwa Ubangijinsu Ya nufe su da shiriya.”
(Suratul Jinn: 10)

Wannan yana tunatar da mu girman alherin da Allah Ya kawo wa duniya ta hanyar aiko da Annabin rahama, Muhammad ﷺ, wanda Allah Ya aiko shi da shiriya da haske.

Kamar yadda mawaƙin Larabci Ahmad Shawqi ya bayyana:

«وُلِدَ الهُدَى فَالكَائِنَاتُ ضِيَاءُ»

“An haifi shiriya, sai halittu s**a haskaka.

Allah Ya aiko ManzonSa ﷺ domin ya fitar da mutane daga duhun jahilci zuwa hasken imani, ya koyar da su gaskiya, adalci, tausayi da kyawawan ɗabi’u.

Allahumma salli wa sallim wa baarik ‘ala Sayyidina Muhammadin wa ‘ala alihi wa sahbihi ajma’in.

Muna taya daukacin al’ummar Musulmi murnar Mauludin Annabi Muhammad ﷺ.

Allah Ya ƙara mana ƙaunarsa, Ya sanya mu cikin waɗanda za su bi Sunnarsa, Ya kuma haɗa mu da shi a Aljannar Firdausi. Amin.

Dan majalisar Umaisha/Ugya daga jihar Nasarawa ya bayar da tallafin Tukwanen girki na mata a mazabarsa shin Wane fata za...
24/08/2026

Dan majalisar Umaisha/Ugya daga jihar Nasarawa ya bayar da tallafin Tukwanen girki na mata a mazabarsa shin Wane fata zaku yi masa?

24/08/2026

Da ɗumi-ɗumi: Bayan tallan Muslim-Muslim ta Shugaba Bola tinubu Sheikh Jingir Ya samu Kyautar Milyan ɗari uku 300m daga fadar shugaban ƙasa ya kuma samu Wata kyautar milyan ɗari uku 300m dai daga Gwamnan Jihar Yobe idan an haɗa Milyan ɗari shida kenan 600m

Mai Zaku Ce?

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GCHN Updates24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to GCHN Updates24:

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share