Platinum Hausa

Platinum Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Platinum Hausa, Kano Outlying.

Taken mu, "Binciko Sahihan Labarai"Gidan Jaridar Hausa wata kafa ce ta zamani da aka kafa, domin kawo sahihan labarai, nazari, bincike da fassarar al’amura cikin sauƙin fahimta ga masu karatu a harshen Hausa.

🚨⚽ Tawagar ƴan wasan ƙasar Bosnia sun ƙi gaisa wa da ƴan wasan Isra’ila bisa yaƙin IranƳan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar B...
03/04/2026

🚨⚽ Tawagar ƴan wasan ƙasar Bosnia sun ƙi gaisa wa da ƴan wasan Isra’ila bisa yaƙin Iran

Ƴan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Bosnia and Herzegovina ƴan ƙasa da shekaru 21, sun ja hankalin duniya kafin wasansu na neman tikitin shiga gasar Turai da s**a fafata da Isra'ila, bayan da yawancinsu s**a ƙi yin musabaha da abokan karawarsu.

Wasan, wanda aka buga a wajen birnin Budapest na ƙasar Hungary, an tashi babu ci (0-0). Sai dai abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne abin da ya faru kafin fara wasan.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Bosnia and Herzegovina, sun ce, matakin da ƴan wasan s**a ɗauka ya na da alaƙa da hare-haren soji da ƙasar Isra'ila ke yi a kan Falasɗinawa da kuma Iran.

Lamarin ya faru ne a lokacin al’adar gaisuwar kafin wasa, inda ƴan wasan Bosnia s**a wuce ba tare da sun yi musabaha ba, sannan s**a bar filin ba tare da wani ƙarin bayani ko alama ba.

Rahotanni sun ce, hakan ya bai wa ƴan wasan Isra'ila mamaki, tare da ƙara ɗora yanayi mai ɗauke da damuwa a wasan da tuni yake da matuƙar sarƙaƙiya.

Ko a baya ma dai, an sha samun irin waɗannan lokuta inda wasu ƴan wasa ko ƙungiyoyi ke ƙin yin wasu al’adu na girmamawa ga ƙungiyoyin Isra'ila a wasanni daban-daban.

31/03/2026

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ganawa ta musamman da jiga-jigan ƴan majalisun Kano, da masu ruwa da tsaki na APC, ta yadda gwamnatin sa ta tafi dai-dai, bisa tunkarar ƙalubalen dake gaban su a yanzu.

Hoto daga Gwamnatin Kano.

31/03/2026

Siyasar Kano Sai Ɗan Kano: Cikakken jawabin Kwankwaso, yayin da Gawuna ya yanki ƙarin jam'iyyar ADC a Kano

31/03/2026

Don Allah don Annabi mu guji gulma, mu guji annamimici, muguji tsegumi, saboda wasu makusantan Kwankwaso ne s**a shirya min mugunta a lokacin da ina Kwamishina, s**a hadani da Kwankwaso - Gawuna

Sabon salon Yamal ya ɗauki hankalin duniyar ƙwalloSabon salo ga Lamine Yamal, yayin da ya sanya farin zare ya ɗaure gash...
27/03/2026

Sabon salon Yamal ya ɗauki hankalin duniyar ƙwallo

Sabon salo ga Lamine Yamal, yayin da ya sanya farin zare ya ɗaure gashin sa a wasan sada zumunci da Spain ta fafata da Serbia 🔥

💔🇳🇬 Osimhen: Darasi Kan Godiya da Rayuwa 💰👊Tauraron Najeriya, Victor Osimhen, ya bayyana wani labari mai ɗauke da darasi...
27/03/2026

💔🇳🇬 Osimhen: Darasi Kan Godiya da Rayuwa 💰👊

Tauraron Najeriya, Victor Osimhen, ya bayyana wani labari mai ɗauke da darasi daga rayuwarsa:

Ya ce, 🗣️ “Na taɓa tura wa wani abokina €5,000 don ya fara kasuwanci… amma bai nuna godiya ba.”

Ya ce, "Ya na tsammanin €50,000, saboda ya ji ina samun miliyan €1 a kowane mako.” 😳

📌 Abin da Osimhen ya jaddada, 👉 €5,000 a Turai kaɗan ne, amma Najeriya kuɗi ne mai yawa sosai.

👉 Ya ƙara da cewa, bai samu taimako daga kowa ba kafin ya yi nasara, ya yi wahala sosai, har ya sayar da ruwan roba a t**i 💪

🔥 Babban Darasi:

✔ Ka koyi godiya da abin da aka baka
✔ Kada ka kasance da ra’ayin “ya kamata a bani ƙari”
✔ Nasara ta na zuwa ne da wahala da juriya.

👀 Kammalawa:
👉 Maganar Osimhen ta na koya mana cewa:
Godiya ita ce mabuɗin albarka. 🙏






🚨 Ƴan wasan Iran sun fito da jakunkunan makaranta a wasan su da Najeriya don alhini ga yara ƴan makaranta da s**a rasa r...
27/03/2026

🚨 Ƴan wasan Iran sun fito da jakunkunan makaranta a wasan su da Najeriya don alhini ga yara ƴan makaranta da s**a rasa ransu matakin da ya girgiza duniya ❤️

Ƴan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Iran, sun fito da jakunkunan makaranta kafin su kara da Super Eagles ta Najeriya, domin nuna alhini da girmamawa ga yara da malamai da s**a mutu a wani hari da ya shafi makaranta a ƙasarsu.

Rahotanni sun bayyana cewa, sama da yara da malamai fiye da 160 ne s**a rasa rayukansu a harin, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami.

’Ƴan wasan sun ɗauki wannan mataki ne a matsayin alamar goyon baya da tunawa da waɗanda abin ya shafa, inda s**a kuma sanya baƙaƙen bandeji a hannu yayin rera taken ƙasar Iran.😭

Duk da yaƙin da Iran take, wannan shi ne wasa na farko da ɓangaren maza s**a buga wasan, amma sun yi rashin nasara a wasan da ci 2 da 1.

Tuna baya....Ga Kwankwaso ga Abba 💪
15/03/2026

Tuna baya....

Ga Kwankwaso ga Abba 💪

Saura ƙiris ya tsallake......
15/03/2026

Saura ƙiris ya tsallake......

Isra'ila ta shafe tsawon shekaru ta na bibiyar Ayatullah KhameneiRahotanni daga manyan kafafen yaɗa labarai sun bayyana ...
04/03/2026

Isra'ila ta shafe tsawon shekaru ta na bibiyar Ayatullah Khamenei

Rahotanni daga manyan kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa, hukumomin leƙen asirin Isra'ila, sun shafe shekaru suna kutsawa cikin tsarin kyamarorin zirga-zirga da hanyoyin sadarwa a birnin Tehran, domin bibiyar motsin jagoran addini na Iran, wato Ali Khamenei, da kuma jami’an tsaronsa.

An ce an yi amfani da bayanan da aka tattara na tsawon lokaci wajen gano yadda yake tafiya, lokutan fitarsa da dawowarsa, da hanyoyin da yake bi. Rahotannin kamfanin labarai na Tasnim ya ƙara da cewa, wannan bayanan sun taimaka wajen tsara farmakin da aka kai masa.

Sai dai har yanzu ɓangarorin da abin ya shafa ba su tabbatar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya gudana ba, kuma ana ci gaba da samun muhawara da saɓanin ra’ayi a kan gaskiyar wasu daga cikin rahotannin.

Address

Kano Outlying

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Platinum Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share