
24/06/2025
WATA SABUWA: Jigo A Jam’iyyar APC Ya Gargadi Nasiru El-Rufa’i Kan Ya Rage Shan Kwaya, Domin Ta Fara Sashi Sambatu — Dakta Sani Ahmad Zangina
Mai Fashin Baki kan Lamuran Siyasa Dakta. Sani Ahmad Zangina ya shawarci tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, da ya daina shan kayan maye, yana mai cewa alamu sun nuna hakan ya fara yin tasiri ga hankalinsa.
Dakta Zangina ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa kwayar da El-Rufa’i ke sha ita ce ke haddasa masa haukace-haukace, har ta kai ga ya fara zagin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, shugaban da ke da ƙaunar Nijeriya da al'ummar ƙasa, musamman talakawa.
A cikin zazzafan martanin da ya fitar, Zangina ya caccaki El-Rufa’i bisa sukar mulkin Tinubu, yana mai cewa hakan ya nuna ba don gyara ba ne yake zage zage, sai don wata manufa ta kashin kansa.
Idan da gaske ne El-Rufa’i na son cigaban Nijeriya, da bai bijire wa gaskiya ba. Amma yau sai ga shi yana ƙoƙarin ɓata sunan shugaba Tinubu da gwamnatin sa, saboda kawai ba a sake damƙa masa mukami ba,” in ji Zangina.
Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da El-Rufa’i zai koma ya gyara kansa, “domin duk wanda ke zagin wanda ya fi shi tausayi da adalci, to tabbas akwai matsala a tattare da shi.