05/05/2023
DAKTA NA’IMA IDRIS LIKITA ABAR ALFARIN ARÈWA DAMA NAHÍYAR AFRIKA GABA DAYÀ
Addinin Musulunci wayayyen addini ne wanda ya ba wa dukkan al'umma maza da mata damar neman ilimi da gudanar da ayyukan cigaban rayuwar al'umma.
Tun farkon zuwan Addinin Musulunci, mata sun samu damar sanin ilimin likitanci da kuma yi wa marasa lafiya maza da mata magani musamman ma a wurin yaƙi.
A zamanin Manzon Allah SAW an samu mace likita mai suna Rufayda Bint Sa'ad Al-Aslamiyya. A lokacin yaƙin Badar ranar 13 Ga Watan Mach, 624 CE ita ce ta yi wa musulmai mayaƙa magani kan raunukan da su ka samu. Rufaida ta samu mafi yawan iliminta na likitanci a wurin mahaifinta Sa'ad Al-Aslami wanda masanin kiwon lafiya ne.
Sai kuma Al-Shifa Bint Al-Quraishiyya Al-Adawiyah, ta kasance ɗaya daga cikin wayayyun mata a wancan lokacin wacce ta ke da ilimin magunguna. Sunanta na asali Layla, amma ta samu laƙabin suna "Shifa" (Waraka).
Bayan ita sai kuma Nusayba Bint Ka'ab Al-Mazneya wacce ta gudanar da aikinta na Likitanci a lokacin yaƙin Uhud. Da kuma Ummu Sinan Al-Islami wacce ita ma ta nemi izinin Manzon Allah SAW ta je wurin yaƙi ta gudanar da aikin yin magani ga waɗanda aka ji wa raunuka da kuma ba da ruwan sha ga mayaƙa.
Sai Ummu Warƙa Bint Harith wacce ta ba da gudunmawa wajen haɗa alqur'ani wuri guda, ita ma ta yi aikin likitanci a lokacin yaƙin Badar.
Daɗi da ƙari, akwai Nusayba Bint Al-Harith wacce aka fi sani da Ummu Al-Athia, ita ma likita ce har kaciya ta ke yi sannan kuma ta ba da gudunmawa wajen ba da agajin gaggawa ga mayaƙa a filin daga da kuma tallafa musu da ruwan sha.
Bayan fannin ilimin lafiya, sauran fannonin ilimi ma ba a bar mata a baya ba. Sutayta Al-Mahamili gogaggiyar masaniyar ilimin lissafi ce da adabin Larabci da hadisi da sanin hukunce-hukuncen shari'a.
Sutayta ta taso a gida na ilimi a birnin Baghadad ta rayuwa a tsakiyar ƙarni na 10. Ta samu yabo daga manyan malaman tarihi kamar su: Ibn al-Jawzi, Ibn al-Khatib Baghdadi da kuma Ibn Kathir.
Ayesha ƴa ce ga Prince Ahmed na Andulus wacce ta rayuwa a ƙarni na 11 gwana ce a fannin Ilimin Rhyme da Oratory. Sannan Labirare ɗinta ya kasance ɗaya daga cikin ƙayatattun labirare cikakku a masarautar Andulus.
A fannin fasaha da zane mai kyau akwai Thana, baiwa a gidan Ibn Qayyum. Sai kuma Rasa a ƙasar Indiya wacce ta wallafa littafi kan magunguna da kulawa da mata. Sai kuma Mariyah Al-Qibtiyya ƴar ƙasar Masar wacce ita ma ta yi wallafa a ƙarni na bakwai. Wata ƙwararriyar a fannin ilimin kimiyya ita ce Al-Ijiliyyah Bint Al-Ijili Al-Asturlabi wacce ta bi sahun aikin mahaifinta na kimiyya a birnin Aleppo a Arewacin Siriya a ƙarni na 10. Kaɗan kenan daga cikin manyan mata masana da aka taɓa yi a tarihin Duniya.
A wannan zamanin a kasa irin Nígeria Allah ya azurta mu da hazikan mata irin su Dr. Dr. Dr. Naima Idris Usman likita abar alfaharin Arewa dama Nahiyar Africa gaba daya.