YMC Hausa

YMC Hausa Muryar Al’umma, hasken gaskiya, Labarai sahihai da shirye shiryen al’umma.

24/09/2026

Yadda kotu ta bukaci a sake zaben da ya samar da Sheikh Isa Ali Pantami a matsayin dan takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar PDP

24/09/2026

Fasarar Jawabin Shugaban Kasar Iran a wajan taron Majalisar dinkin Duniya.

24/09/2026
Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa a rumfar mai shayi
24/09/2026

Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa a rumfar mai shayi

Atiku Abubakar Ya Ziyarci Maiduguri Domin Jajanta Wa Al’ummar BornoƊan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji At...
24/09/2026

Atiku Abubakar Ya Ziyarci Maiduguri Domin Jajanta Wa Al’ummar Borno

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya ziyarci Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin jajanta wa al’ummar jihar kan ibtila’in ambaliyar ruwa da ya shafi wasu sassan jihar.

A yayin ziyarar, Atiku ya nuna alhininsa ga waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa, tare da miƙa sakon ta’aziyya da goyon baya ga al’ummar Borno.

Ma’aikatar Inganta Lafiyar Dabbobi da Bunƙasa Albarkatun Dabbobi ta Jihar Yobe ta kai ziyarar ban-girma ga Kwamishinan H...
24/09/2026

Ma’aikatar Inganta Lafiyar Dabbobi da Bunƙasa Albarkatun Dabbobi ta Jihar Yobe ta kai ziyarar ban-girma ga Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Yobe, Hon. Abdullahi Bego, domin neman ƙarfafa haɗin gwiwa wajen wayar da kan jama’a kan harkokin kiwo da lafiyar dabbobi.

Shugaban Shirin, Dr. Bulama Maina Yaro, wanda ya jagoranci tawagar, ya yaba wa Kwamishina Bego bisa ƙoƙarin ma’aikatar wajen wayar da kan jama’a kan shirye-shiryen gwamnati da ayyukan ci gaba.

Dr. Yaro ya bayyana cewa ana neman ƙarin haɗin gwiwa domin wayar da kan jama’a kan lafiyar dabbobi, inganta kiwo, jin daɗin dabbobi da kuma rigakafin cututtukan da ke iya yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane, ciki har da cutar hauka (rabies).

Ya kuma jaddada muhimmancin masu kiwon karnuka su kula da su yadda ya kamata tare da yi musu allurar rigakafi.

A nasa martanin, Kwamishina Abdullahi Bego ya tabbatar da goyon bayan ma’aikatar wajen wayar da kan jama’a, hulɗa da kafafen yaɗa labarai da kuma inganta sadarwa.

Bego ya kuma jaddada muhimmancin amfani da damar da Jihar Yobe ke da ita a fannin kiwo, ta hanyar inganta samarwa, sarrafawa da tallace-tallacen dabbobi.

Kwamishinan ya kuma yi kira da a yi amfani da Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na Yobe wajen bunƙasa kasuwancin dabbobi, da kuma haɗa masu kiwo da kasuwanni a cikin gida da ƙasashen waje.

13/09/2026

Tattaunawa ta Musamman tare da Shugaban Kungiyar Masu Sauraro da Sada Zumunci ta Jihar Yobe.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when YMC Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to YMC Hausa:

Shortcuts

Share