
14/09/2025
Zakaran Duniya A Gasar Turanci Nafisa ta Ziyarci Farfesa Isa Ali Pantami, CON (Majidadin Daular Usmaniyya)!
Jiya, daliba mai shekaru 17, Nafisa Abdullah Aminu daga Jihar Yobe, ta kai ziyara wurin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami domin nuna godiya kan jagoranci da shawarwari da yake bata tare da gabatar masa da kyautar zakaran duniya da ta samu a bara.
Wannan gagarumin lambar yabo ta samu ne bayan ta bayyana a matsayin mace ta farko daga Najeriya da ta fi kowa iya harshen Turanci a duniya a gasar TeenEagle Global Finals 2025 da aka gudanar a birnin London, ƙasar Birtaniya.
Nafisa, dalibar Nigerian Tulip International College (NTIC), ta samu nasara ne a tsakanin fiye da ‘yan takara 20,000 daga ƙasashe 69 – ciki har da ƙasashen da harshen Turanci shi ne na asali – abin da ya sa ta dauki kambun zakara. Wannan nasara ta zama shaida cewa idan ɗaliban Najeriya s**a samu dama, shawarwari, da kuma goyon baya mai kyau, suna da cikakken ƙarfin iya ficewa a duniya.
A lokacin ziyarar, Nafisa ta bayyana godiyarta ga Farfesa Pantami saboda goyon bayan da yake bata a fannin ilimi da addini. Ta kuma roƙi ci gaba da jagoranci da shawarwari a gaba.
Farfesa Pantami ya gode wa iyaye, masu kula da ita, da malamai bisa kawo Nafisa ofishinsa. A wurin, ya bata shawarwari masu daraja don samun nasarar rayuwa, ya kuma kyauta mata sabuwar kwamfutar HP mai ƙarfi tare da littattafai na ƙarin karatu da shawarwari.
Iyalan Pantami sun ƙarfafa Nafisa da ta ci gaba da tafiya a harkar ilimi har sai ta kammala digiri, ta samu digirin digirgir (master’s), da kuma PhD. Sun jaddada cewa wannan zamani yana da buƙatar fitattun mata a ilimi fiye da da.
A ƙarshe, Farfesa Pantami ya amince da roƙonta na ci gaba da kasancewa cikin jagoranci da shawarwarinsa, tare da ƙarin tsare-tsare na tallafi.