03/06/2025
RAYUWA LISSAFI CE
kamar kamawar Damina ce,
1. akwai loƙacin Shuka
2. akwai loƙacin Dashe,
3. akwai loƙacin Girbi,
duk wanda loƙacin sa ya wuce daga cikin waɗancan abubuwa guda uku to saidai Daminar baɗi.
Matasa ayi amfani da loƙaci domin shi loƙaci ba ya jira, yau ce ta ke gina gobe. Kada ka yi lalaci ka ƙi yin aiki sai loƙacin girbi ya zo Manoma su na ɗaure Dami kai kuma ka na ɗaure fuska,
KA DA KA ZAMO DAGA CIKIN MASU ƘOƘARIN CI DA GUMIN WASU,
Aiki Aiki Aiki أهل الفيضة.
Shaikh M Aminu Mai Diwani tudun wada