08/08/2024
Wlh Wannan Bawan Allah n Yana kokari sosai a irin Wannan Yanayin Da Talaka Yake Ciki
Kabiru Amadu Salamu Alaikum.
Yau chikin ikon Allah mun chi gaba da ganawa da Alumma daban daban, inda muka gana da wakilan mu da ke rika muna aiki na chikin unguwanni daban daban, muka tattauna mukaji kuma minene korafe korafen Alummar yankunan su, da kuma abubuwan da zamuyi a kowa ne bangare.
Bayan mun kammala sannan kuma Muka rabamusu kayan Abinchi.
Mungana da kungiyar Head teachers na makaruntun mu na primary schools Gusau da Alumma daban daban, da kungiyoyi, da Masu neman takarkaru na karamar hukuma da na kansiloli.
Bayan nan mun fita mun kai ziyarar taaziyar rasuwar wasu bayin Allah da gaisuwar rashin lapia a gidaje kamar haka;-
1. Gidan iyalan Marigayi Dr salisu sadi tsafe a FCET Quaters inda mukayi taaziyar rasuwar shi.
2. Gidan su Sayyida Hadiza Sadauki inda mukayi taaziyar rasuwar mahaifinta.
3. Gidan Alh Musa Mallaha a Motorgage inda mukayi Taaziyar rasuwar Dansa da Barayi s**a halbe
4. Gidan Mahaifan Zayyanu Zakariya Mai Hatsi a Sabon Fegi inda mukayi taaziyar Rasuwar shi.
5. Gidan Bello Dakin Gari a Damba inda mukayi taaziyar Rasuwar Dan Dan shi.
6. Mun duba Arma a unguwar Tudun Faila daya daga chikin matasan mu da yasamu Hadarin mota ya karye a kafa
7. Mun duba Ali Maza a Tudun Faila wanda yan saresare s**a sassare har s**a chire mishi kafa.
8. Sai Majalisar Motorgage inda na tsaya muka gaisa da su kuma s**a bani shayi na sha.
Bayan mun dawo da dare kuma mun amshi bakunchi Kungiyar Dalibai ta Makarantar Sch. Of Nursing dake Gusau, da kuma gamayyar kungiyar Kansiloli na jihar Zamfara suma sun kawo mani ziyari har s**a bani award ta girmamawa.
Ina godiya ga dukkan wanda yazo, Dafatar kowa ya koma gida lapia.
Allah shi yabbamu
Allah mungode.
Hon kabiru Amadu Mai Palace
MHR Gusau/Tsafe federal constituency
Zamfara State
7th Aug 2023.