Amon Nasara

Amon Nasara Wannan kafar sadarwa ce mai ƙoƙarin yaɗa labarai da rahotanni masu sahihanci, tare da nishadantar

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, na daga cikin ɗaliban da aka karrama a bikin yaye ɗalibai na Jami'...
04/09/2025

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, na daga cikin ɗaliban da aka karrama a bikin yaye ɗalibai na Jami'ar SOAS dake Ingila, inda ya karɓi kwalin digirinsa na uku (PhD).

Taron ya samu halartar 'yan uwa da abokan arziƙi daga Najeriya da ƙasashen waje. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na daga cikin waɗanda s**a halarci bikin.

Me Ya Sa Littattafan Hausa S**a Gaza Gogayya Da Sauran Littattafai Na Harsunan Duniya?Bayan wani gajeren rubutu da na yi...
23/08/2025

Me Ya Sa Littattafan Hausa S**a Gaza Gogayya Da Sauran Littattafai Na Harsunan Duniya?

Bayan wani gajeren rubutu da na yi a kan gasar gajerun labarai ta Bashir Othman Tofa da aka gudanar a Kano, na samu tambayoyi a kan yanayin da littattafan Hausa suke ciki, musamman na rashin ingantattun zarurrukan labarai da kyan bugu littattafai da rashin kyakkyawan tsarin kasuwancin su a Najeriya ta yadda za a yaɗa su a duniya?

Akwai waɗanda suke ganin su kansu marubutan ba su samu gudunmawar da ta dace ba, inda sabbin marubuta ma ba sa samun kulawa da gata na horon da ya kamata, kamar yadda takwarorinsu na Turanci suke samu.

Tabbas harshen Hausa yana da miliyoyin al'umma, wanda idan aka yi amfani da ilimi da tsare-tsare masu kyau, sannan aka zuba jari a cikin harkar za a samar da dubban makaranta. Duk kuwa da barazana da ake samu daga kafofin sadarwa na zamani da na'ura mai ƙwaƙwalwa.

A halin da ake ciki a yanzu babu wani ƙasaitatcen kamfani a duniya da yake buga littattafan Hausa don kasuwanci. Ko rawar da littattafan Hausa na wancan zamani s**a taka ta samo asali ne daga gudunmawar Turawan mulkin mallaka, da kamfanonin ɗab'i na wancan lokaci.

Na yarda marubutan wannan zamani tun daga 1980 zuwa yanzu sun bada babbar gudunmawa, musamman ta tabbatar da yin rubuce-rubuce cikin harshen Hausa da yaɗa shi a duniya. Amma rashin manyan kamfanonin ɗab'i da wallafe-wallafe ya taka rawa wajen halin da rubuce-rubucen Hausar ke ciki.

Kamfanoni irin su Macmillan da Heinemann da Longman ba sa kallon marubutan Hausa. Da yawansu suna ganin ba za su samu ribar da ta kamata ba. Waɗannan kamfanoni suna da ƙarfin jari da tsarin kasuwancin zamani, ta yadda za su tura littattafansu ko'ina a faɗin duniya.

Idan da irin waɗannan kamfanoni za su rungumi marubutan Hausa, sannan a samar da abin da wasu ke kuka a kai na rashin masu bada horo (mentorship), za a samu abin da ake so. Domin shi kamfani idan yana son aikin marubuci zai tabbatar sai ya kai mizani da ake so a duniya.

Za su iya cimma haka ta hanyar shirya taron sanin makamar aiki da haɗa marubuci da edita da zai dinga bibiyar aikinsa. Kamar yadda Rupert East ya yi wa Abubakar Imam a lokacin rubutun 'Magana Jari Ce' da wasu littattafai da ya rubuta.

Amma me ake tsammani idan marubuci shi ne zai kasance mai rubutawa, mai tace kayansa, sannan ya buga shi? Bayan ya bugawa shi ne zai yaɗa shi tare yin kasuwancin kayansa.

Sannan shi ne zai shirya tarurruka tsakaninsa da makaranta don taimakawa wajen isar da abin da littafin ya ƙunsa. Sannan uwa-uba yin sharhin littafin da gabatar da tattaunawa a rubuce ko a zahiri.

Duk waɗannan ba ƙananan ayyuka ba ne dake buƙatar kuɗi da ƙwarewa a kowanne ɓangaren da na zayyano. To amma marubutan Hausa sun dogara ne wajen buga littattafansu da kansu saboda rashin waɗannan kamfanoni.

Ko ƙananan kamfanonin buga litattafai da muke da su a Arewa, yawancinsu basu da banbanci da masu aikin buge-bugen takardu. Domin ba za su iya buga littafin marubuci a tsarin da aka san shi a duniya ba. Dole sai marubuci ya sauke musu kuɗin aikin littafin, sannan da zarar sun buga za su miƙo masa kayansa.

Shi kansa ingancin bugu da ƙa'idodi rubutu akwai rauni sosai a ciki. Wannan ya sa ko makarantun mu na gida ba sa karɓar irin waɗannan littattafai, bare kuma na ƙasashen ƙetare.

Idan ana son samun cigaba mai ɗorewa sai an yi aiki tuƙuru. Dole sai masu ruwa da tsaki a cikin harkar rubutun sun haɗa kan su. Duk wani da yake da hanya ta samar da jari ko kamfanonin da za su saka jari sai ya shigo.

Ta haka ne za a iya karkato da tunanin manyan kamfanonin ɗab'i zuwa littattafan Hausa, ko kuma a samar da wasu da za su saka jari don ciyar da hankar gaba.

Akwai kasuwa sosai a cikin rubuce-rubucen Hausa. Amma harkar tana buƙatar a inganta, abin da Bature yake kira 'packaging'. A wannan zamani da ake da kafofin sadarwar zamani, akwai hanyoyi sosai na yaɗawa da tallata littattafai.

© Zaharaddeen Ibrahim Abdullahi Kallah

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya karɓi ziyarar mahaddacin Alkur'ani, Bukhari Sanusi Idris wanda ya zo na uku a gasar kar...
22/08/2025

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya karɓi ziyarar mahaddacin Alkur'ani, Bukhari Sanusi Idris wanda ya zo na uku a gasar karatun Alkur'ani ta duniya, ta Sarki Abdulaziz da aka gabatar a ƙasar Saudiyya.

Gwamnan ya karɓi zakaran gasar a gidan Gwamnatin Kano, inda ya gabatar masa da shaidar girmamawa da ya samu.

Bukhari ɗan shekara 17 ya yi nasarar samun zunzurutun kuɗi har Riyal na Saudiyya 400, 000, kwatankwacin Dalar Amurka 107, 000.

Wannan matashi ya cancanci yabo, domin wannan zai ƙara matasa himma kan karatun Alkur'ani. Allah ya sanya albarka.

Jarumi Adam A. Zango ya bi sahun Rahma Sadau, inda a wannan satin aka tashi da ɗaurin aurensa tare da amaryarsa Maimuna,...
17/08/2025

Jarumi Adam A. Zango ya bi sahun Rahma Sadau, inda a wannan satin aka tashi da ɗaurin aurensa tare da amaryarsa Maimuna, wanda ita ma jaruma ce a cikin shiri mai dogon zango na Gwarwashi.

Allah ya sanya alheri. Allah ya sa mutu ka raba.

A wannan ƙasa mai albarka, wane abu ne zai sa mu shiga hayyacinmu tare da yin nadama domin tausasawa al'ummar ƙasa?Na tu...
17/08/2025

A wannan ƙasa mai albarka, wane abu ne zai sa mu shiga hayyacinmu tare da yin nadama domin tausasawa al'ummar ƙasa?

Na tuna zamanin annobar korona (COVID 19) ne, lokacin da aka rufe duniya ba-shiga-ba fita. Lokacin da duniya ta shiga firgici da tsoron masifun da s**a danno na mace-mace da yunwa sakamakon rufe kasuwanni da harkokin yau da kullum.

A wannan lokaci ne fargaba da tsoro ya yi ajalin mutane da dama, saɓanin ainahin ita annobar. Idan ba mu manta ba har sallar Juma'a aka dakatar a wannan ƙasa, aka ce kowa ya koma yin sallah a gida.

Tsofaffi sun razana da shiga firgici, ba wai don tsoron cutar ba. A'a, sai don don sun zo masallaci don gabatar da ibadar sallah, amma aka ce musu su koma gida babu sallah. Ɗaruruwan shekaru ba su taɓa mafarkin za a hana sallah a wannan lokacin da addini ya samu gindin zama ba.

Idan ba ku manta ba, a wannan lokaci ne aka yi gidauniya domin samar da tallafi na ƙarfafar masu rauni. A wannan lokaci an tara maƙudan kuɗaɗe tare da abinci a rumbuna daban-daban a ƙasar.

Amma a ƙarshe wannan gidauniya da abincin da aka tara an yi abin da aka yi da su, domin mafi akasari wannan tallafi bai je inda ake so ba. Asali ma sai bayan annobar ne jama'a s**a fahimci akwai tarin abinci da aka tara domin rangwamawa al'umma. Amma waɗanda suke jagorancin ƙasar s**a yanke hukuncin amfani da wannan tallafi ta hanyar da su suke so.

A lokacin da aka fara fito da irin waɗannan kaya don buƙatar waɗanda ke kula da tsarin, sai jama'a s**a ankara. Hakan ya sa aka fara farwa waɗannan guraren.

Duba ga wannan tarihi na korona, shin wane abu ne zai iya taɓa zuciyar jagororin mu har su ji tsoron Allah da tuna duniya ba komai ba ce?

Tabbas idan da za a samu irin wannan nadamar da tunanin abin da ya faru na mace-mace da firgici da lalacewar jarin masu ƙaramin ƙarfi, da wataƙila ba a shiga wannan hali ba.

Anya akwai abin da zai sosa zukatan jagororin mu da masu faɗa a ji?

© Zaharaddeen Ibrahim Kallah

Jaruma Rahama Sadau ta miƙa saƙon godiyarta ga 'yan uwa da abokan arziƙi bisa taya ta murna da addu'oi kan aurenta da ak...
14/08/2025

Jaruma Rahama Sadau ta miƙa saƙon godiyarta ga 'yan uwa da abokan arziƙi bisa taya ta murna da addu'oi kan aurenta da aka yi a satin da ya gabata.

"Ina mika sakon godiya ta musamman ga dangi, ’yan uwa da abokan arziki bisa fatan alheri da addu’o’in ku a game da Auren mu. Kalmominku da addu’arku sun karfafa mana guiwa kuma sun sa ranar ta kasance ta musamman. Allah Ya saka da alkhairi. ❤️"

Rahama, Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya.

Wani zobe na zunzurutun kuɗi har dala 950, 000, wato naira biliyan ɗaya da rabi a kuɗin Najeriya. Wannan zoben mawaƙi Da...
13/08/2025

Wani zobe na zunzurutun kuɗi har dala 950, 000, wato naira biliyan ɗaya da rabi a kuɗin Najeriya. Wannan zoben mawaƙi Davido ne ya ba wa matarsa Chioma Adeleke, a matsayin zoben aurensu.

Jakadiyar Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar Hassan mai rajin tabbatar da zaman lafiya a duniya tare da mataimakin sh...
12/08/2025

Jakadiyar Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar Hassan mai rajin tabbatar da zaman lafiya a duniya tare da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Wannan dama da aka ba ta ya ƙara darajar mata da masu fasahar ƙirƙira a duniya.

11/08/2025

Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta...

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasara yin raga-raga da 'yan bindiga a jihar Zamfara, bayan da jiragen saman sojin ƙasar ya yi luguden wuta a kan su.

Sojojin sun samu nasarar ne a wasu hare-haren sama da s**a kai a wani yanki na ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda jiragen yaƙin ta s**a yi ruwan wuta kan wani sansanin 'yan bindigar a dajin Makakkari.

Dama an ce ƙarshen alewa, ƙasa.

Bayan mutuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari an fara kiraye-kiraye kan waye zai maye gurbinsa a dattawan arewa d...
17/07/2025

Bayan mutuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari an fara kiraye-kiraye kan waye zai maye gurbinsa a dattawan arewa da ake da su.

Duk da cewa irin wannan matsayi ba zaɓar mutum ake ba, aikinsa da gudunmawarsa ga Arewa ce take ba shi wannan matsayi. Wa kuke ganin zai iya hawa wannan matsayi tsakanin Atiku Abubakar da Kashim Shettima ko Rabiu Musa Kwankwaso da Nasiru El-Rufai?

An gabatar da jana'izar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, inda aka binne shi a gidansa dake Daura.
15/07/2025

An gabatar da jana'izar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, inda aka binne shi a gidansa dake Daura.

Yayin da gawar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Janar Muhammadu Buhari ta iso Katsina. Saura wucewa Daura, inda za a binn...
15/07/2025

Yayin da gawar tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Janar Muhammadu Buhari ta iso Katsina. Saura wucewa Daura, inda za a binne shi a cikin gidansa.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amon Nasara posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Amon Nasara:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share