24/08/2026
NELFUND TA YABAWA SHUGABA TINUBU KAN DOREWAR TALLAFIN LAMUNIN DALIBAI
Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ƙudirin tabbatar da dorewar tsarin ba da lamunin karatu ga ɗaliban Najeriya.
NELFUND ta ce Shugaban Ƙasar ya bayar da umarnin karkatar da kuɗaden da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifukan Tattalin Arziƙi (EFCC) ta kwato zuwa asusun NELFUND, domin ƙarfafa shirin ba da lamunin karatu ga ɗalibai.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Sadarwa ta NELFUND, Mrs Oseyemi Oluwatuyi, ta fitar a ranar 19 ga Agusta, 2026, asusun ya kuma yi maraba da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) kan tura ribar da ba a karɓa ba daga Capital Market Trust Fund da Dormant Account Trust Fund zuwa NELFUND.
NELFUND ta ce waɗannan matakai za su taimaka wajen samar da ingantaccen tushen kuɗaɗen da za su ci gaba da tallafa wa shirin lamunin ɗalibai, musamman yayin da yawan masu neman tallafin ke ƙaruwa.
A cewar asusun, zuwa watan Agustan 2026, NELFUND ta riga ta fitar da sama da Naira biliyan 322 ga ɗalibai, daga cikin sama da miliyan 1.6 na buƙatun lamunin karatu da aka gabatar.
Shugaban Hukumar Gudanarwar NELFUND, Jim Ovia, ya bayyana godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa ci gaba da goyon baya da amincewar da yake bai wa asusun. Ya ce hakan ya ƙara ƙarfafa ƙudirin gwamnati na tabbatar da cewa rashin kuɗi bai zama dalilin hana wani ɗan Najeriya samun ilimi mai zurfi ba.
Shi ma Manajan Daraktan NELFUND, Akintunde Sawyer, ya ce sabon ƙudurin Shugaban Ƙasar ya nuna irin muhimmancin da gwamnati ke bai wa ilimi, tare da ƙoƙarin gina tsarin ba da lamunin karatu mai ɗorewa.
Sawyer ya tabbatar da cewa NELFUND za ta ci gaba da amfani da dukkan kuɗaɗen da aka damƙa mata cikin gaskiya da riƙon amana, domin amfanin ɗaliban Najeriya.
NELFUND ta ce sabon tsarin samar da kuɗaɗen zai ƙara wa Gwamnatin Tarayya ƙarfin faɗaɗa shirin, tare da kai lamunin karatu ga ƙarin ɗaliban Najeriya da s**a cancanta.