Zakari Ya'u Salisu

Zakari Ya'u Salisu Writer | Poet | Journalist | Socialist| Advocate | Blogger| Revolutionist |

Future Pharmacist

Kawu Sumaila ya kawo karshen zaman Kabiru Gaya na shekara 16 a matsayin SanataSanatan Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya,...
27/02/2023

Kawu Sumaila ya kawo karshen zaman Kabiru Gaya na shekara 16 a matsayin Sanata

Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya, na jam'iyyar APC, ya sha kaye a hannun dan jam'iyyar NNPP, Abdulrahman Kawu Sumaila, bayan shafe shekara 16 a Majalisar Dattijai.

Kabiru Gaya ya sha kayen ne a sak**akon zaben da INEC ta sanar a Kananan Hukumomi 16 da ke shiyyar, da safiyar Litinin.

Ya sami kuri'a 192,518, yayin da Kawu Sumaila ya samu kuri'a 319,857.

Sak**akon ya nuna hatta Karamar Hukumar Gaya, wacce Kabirun ya fito, dan takarar NNPP ne ya lashe ta.

Kabiru Gaya dai shi ne Shugaban kwamitin da ke kula da INEC a Majalisar Dattawa.

Daga Salim Umar Ibrahim da Aminu Naganye.

01/02/2023

“Idan ka Shagaltu da rushe waninka koda da lafazi ne, tabbas Babu ranar da zaka Gina kanka.”

09/11/2022

Masu shan maganin gajiya, ciwon jiki, ko Mara.
Su kiyaye shan Wadannan magungunan.

Diclofenac sodium
Mefenamic acid.
Aspirin
Feldine
Ibuprofen.

Yawan shansu ko da yaushe, yana kawo cutar gyambon jiki (ulcer).
Da ciwon koda. (Kidney disease).

Yana da kyau kafin kasha su, ka tuntubi likita.

04/11/2022

Allah ka kuɓutar da talakan Najeriya daga hannun Ogan Fir'auna (Sarkin Noman Duniya)😂

GOMBE STATE POLICE COMMAND DIARY:UPDATE ON PHYSICAL AND CREDENTIAL SCREENING EXERCISE FOR THE 9TH REGULAR INTAKE OF NIGE...
28/09/2022

GOMBE STATE POLICE COMMAND DIARY:

UPDATE ON PHYSICAL AND CREDENTIAL SCREENING EXERCISE FOR THE 9TH REGULAR INTAKE OF NIGERIA POLICE ACADEMY IN GOMBE:
DAY: 3

Today 28/9/2022,the Commissioner of Police Gombe State Command CP Ishola Babatunde Babaita, Psc FDMSS paid an unscheduled visit at the venue of the ongoing police screening for the 9th Regular intake of the Nigeria Police Academy in Gombe for on the spot assessment. The CP who was also accompanied by his management team expressed satisfaction on the progress made and wished the applicants success in the ongoing screening exercise.

So far,two hundred and seventeen (217) candidates were screened from various local Local Government Areas in the State comprising of Gombe, Balanga, Nafada, Dukku, Shongom, Kwami, Akko, Biliri and Yamaltu Deba.The screening exercise commenced on the 26th September 2022 and is still ongoing.

Meanwhile,apart from the police team headed by ACP Bello Adamu, others includes representatives of Police Service Commission, police Academy, ministry of police affairs, federal character Commission and representatives of Gombe State government .The excercise is hitch free.

ASP MAHID MUAZU ABUBAKAR,
PPRO Gombe State Police Command,
For -Commissioner of Police Gombe State Command.

Breaking: Court Affirms Machina As APC's Yobe North Senatorial Candidate, Directs INEC To Publish His Name.The Federal H...
28/09/2022

Breaking: Court Affirms Machina As APC's Yobe North Senatorial Candidate, Directs INEC To Publish His Name.
The Federal High Court sitting in Damaturu, Yobe State Capital has declared Bashir Sheriff Machina as the APC's authentic senatorial candidate for Yobe North in the coming 2023 National Assembly elections and directed INEC to accept and publish his name accordingly.

The declaration was made by the presiding judge, Justice Fadima Aminu.

In her verdict today, the Judge affirmed Machina as the duly and validly elected Yobe North senatorial candidate for APC thereby upholding the May 28 primary election of the Party that produced him.

27/09/2022

You know Who a Looser is ?
A looser is Someone who's So Much afraid of winning, He Don't even try!

27/09/2022

PHARMACOLOGY.
Pharmacology is a branch of science that deal with the study of drugs, its Actions, Dosage, Forms, Route, Strength, Indication, Contra-Indications, Side-Effects, Chemical Name & Trade Name.

CLASSIFICATION OF DRUGS.
1- Analgesics.
2- Antibiotics.
3- Antihypertensive(Vasodilators).
4- Antihistamines.
5- Antifungals.
6- Antidiarrheal.
7- Anti rabies.
8- Anticoagulants.
9- Antacids.
10- Anti Pyretics(Non-narcotics).
11- Antimalarials.
12- Anti Emetics.
13- Antiinflammatory(Narcotics).
14- Anti Diuretics.
15- Anticonvulsant.
16- Anti Flarialsis.
17- Antispasmodics.
18- Antidiabetic mellitus.
19- Anti Helmentics.
20- Anesthetic Agents.
21- Broncho Dilators.
22- Disinfectant.
23- Expectorants.
24- Intravenous fluids.
25- Opthalmic Agents.
26- Seddetive.
27- Supportives...,

Sun Taru sun ha'da karfi da karfe duk domin bawa  kwankwaso matsala a zaben 2023..Atiku Abubakar a Kano.Namadi sambo a K...
30/08/2022

Sun Taru sun ha'da karfi da karfe duk domin bawa kwankwaso matsala a zaben 2023..

Atiku Abubakar a Kano.
Namadi sambo a Kano.
Gov Okowa a Kano.
Sule Lamido a Kano.
Makarfi a Kano.
Ibrahim shema a Kano.
Sanata Iyorchia Ayu a Kano.
Attahiru Bafarawa a Kano.
Rt Aminu Tambuwal a Kano.
Walid Jibrin a Kano.
Sanata Shehu Sani a Kano.
Gov Darius ishaku. A Kano.
Sanata Dino Melaye a Kano.
Sanata Baba kaita a Kano.

Da daidai sauran manyan jiga-jigan jam'iyar PDP duk domin Yaki da Sanata kwankwaso shi ka'dai.

Kuma ku zuba Ido ku gani zaku ga irin jama'ar da kwankwaso zai Tara a Jihar Adamawa mahaifar Atiku a duk lokacin da zai ziyarci Jihar na tabbata sai ta ninka jama'ar da Atiku ya tara na zuwan sa jihar Kano.

Soyayyar dake Tsakanin talakawan Nageriya da kwankwaso Daga Allah ne Kuma idan kunji haushi kawai kuyi bindiga ku fashe mudai munce Nageriya sai Mai kishin Al'umma talakawa..

M Inuwa MH...

Mutane da dama daga cikin musulman mu ko mutan Arewa na yiwa karatun boko mummanan fahimta dakuma kin yadda da komai day...
27/08/2022

Mutane da dama daga cikin musulman mu ko mutan Arewa na yiwa karatun boko mummanan fahimta dakuma kin yadda da komai daya shafi karatun boko a tunanin su sunaga k**ar karatun boko kwatakwata bashi da wata fa'ida ga musulmai shiyasa ma wasu s**an ƙi saka ya'yan su a makarantun boko.

Tabbas akwai wasu kurakurai da akeyi a makarantun boko wanda ya saɓa da koyarwa ta addinin Musulunci amma yawancin wannan kurakuren ba acikin ilimin bokon yake ba yana cikin tsarin gudanar da karatun bokonne kunga kenan a matsayin ka na Musulmi duk lokacin da kaga wani tsari da babu shi a cikin addinin ka sai ka ware kanka da yin irin wannan tsari idan kuma acikin karatu ne saika ɗauke shi a matsayin ilimi kawai amma bawai hakan na nufin kayi imani ko yadda dashi bane. Domin ko a zamanin Annabi S.A.W yakan tura sahabbai wani yanki ko gari su koyo wani ilimi don cigaban addinin Musulunci.

Sannan akwai malaman mu k**ar su Dr. Zakir Naik, Sheikh Mohammed Awal, M***i Isma'il Menk, Malam Albanin Zaria, e.t.c. Wanda s**an je su karanci wani littafi wani addinin wanda ba musulunci ba k**ar bible, Vedas da Upanishads, Bhagavad Gita, dadai sauran su amma hakan baya nufin sunyi imani dashi ko aiki dashi sunyi hakanne kawai dan samun ilimi dakuma ƙarawa addinin Musulunci daraja domin wani lokacin s**anyi amfani da hakan su wayar da kan waɗanda ke bin irin waɗannan addinan ta hanyar nuna musu kurakuren dake cikin litattafan su.

Saboda haka domin share duk wani tantama ka duba hotunan da ke ƙasa dan kara samun ƙwarin gwiwa akan yin karatun boko domin akwai manya-manyan maluman addinin musulunci da s**a bada gudumawa a ɓangaren karatun boko wanda har yanzu ana amfani da wannan ilimin saboda haka duk wanda ke ƙyamar karatun boko to yasani mu yak**ata muyi karatun boko domin kuwa karatun boko namu ne bana wasu ba janye jikinmu da muke daga ciki shiyasa wasu s**azo s**a chanja wasu tsare-tsaren.

Yi duba izuwa hotunan dake ƙasa dan kallon irin gumawar da musulmai s**ayi a ilimin kimiyya.

✍️ El-Hamza

Ranar Harshen Hausa ta Duniya!Sheikh (Dr) Muhammad Nasir Kabara ya bada gudunmawa gagaruma wajen haɓɓaka da bun ƙasa Har...
26/08/2022

Ranar Harshen Hausa ta Duniya!

Sheikh (Dr) Muhammad Nasir Kabara ya bada gudunmawa gagaruma wajen haɓɓaka da bun ƙasa Harshen Hausa a Nigeria da Africa. Yayi amfani da Harshen Hausa wajen koyar da Sunna ta Annabi (S.A.W) da kuma yaɗa aƙidar Ash'ariya, mazhabar Malikiya da kuma koyar da sufanci duk acikin Harshen Hausa don sauƙaƙawa ɗaliban ilimi. Wasu daga cikin nasarorin da ya samu cikin bunƙasa Harshen Hausa sun haɗa da:

● Shine mutum na farko a duniya da ya fara fassara Alƙur'ani zuwa Harshen Hausa acikin mujjaladai 4. Ya sawa Tafsirin suna da, " IHSANUL MANNAN" Yayi hakane don kusanto da ma'anonin Alƙurani mai girma ga ɗalibai da kuma bunƙasa Harshen Hausa.

● Yana da Diwani kala-kala na waƙoƙi daya rera cikin Harshen Hausa don koyar da ilimin Tauhidi, Fiqhu, Sufanci da ragowar ilimai cikin Harshen Hausa. Wanda ya bada gudunmawa ga al'umma musulmai inda s**a koyi rukunan musulunci cikin waƙe na Hausa, wanda Sheikh Nasir Kabara ya bada gudunmawa.

●Hakana, Yana da Diwani mai suna , " JAMI'U KANZUL MUDALSAM" wanda ya rubuta cikin Harshen Hausa.

Akwai abubuwa masu tarin yawa daga cikin gudunmawar da ya bada wajen haɓɓaka Harshen Hausa da inganta shi. Allah Ya ƙara Rahama ga Sheikh (Dr) Muhammad Nasir Kabara.

✍Sheikh Sidi Musal Qasuyuny Kabara
26th August, 2022.

08/08/2022

TARIHIN IMAM HUSAINI (AS)

Hussain Ibn Ali Bin Abutalib jikan manzon Allah ne, Allah ya yarda dashi, Dan Nana Fatima diyar manzan allah (SAW), uwargidan Aliyu dan Abutalib, dan'uwansa shi ne Alhasan dan Ali dan Abutalib. Hussain shine wanda Yan Shi'a ke darajawa a matsayin daya daga cikin Imamansu na farko.

HUSAINI Suna ne da Allah Mai girma da Daukaka ya zabar ma yaron Imam Ali (AS) na biyu, k**ar yadda ya zaba mababban yaron nashi suna Hasan (Amincin Allah Ya tabbata a garesu). An ruwaito ruwaya daga Asma’u bintu Umais (RA) dangane da haihuwar Imam Hasan (A.S), Wanda ya gudana a shekara ta 3 bayan Hijira, da haihuwar Imam Husaini (AS) wanda ya faru a
shekara ta 4 bayan hijira.

Kowannensu bayan an haife shi sai Manzon Allah (S) ya tambayi Imam Ali (A.S) shin da wane suna ka ambaci abin haihuwar? Sai Ali (A.S) yace ban gabace ka ba akan hakan. Sai Manzon Allah (S) yace: Haka nima ba zan gabaci Ubangijina ba.

Nan take sai Jibrilu (AS) ya sauko yana cewa: “Ya Muhammad (SAW), Lallai Allah yana gaishe ka, kuma yana ce maka: ‘Ali a wajenka, k**ar Haruna ne a wajen Musa, sai dai kai babu Annabi a bayanka’. Kuma Ka ambaci sunan dan nan naka da sunan yaron Haruna.” Sai Manzon Allah (SAW) yace ma Jibrilu: “Mene ne sunan yaron Haruna ya kai Jibrilu?” sai Jibril (AS) yace: “Sunanshi Shubr” sai Manzon Allah (S) yace masa: “Ni harshena Larabci ne, me hakan ke nufi?” sai Jibril (AS) yace ka ambace shi da ‘Hasan’. Yayin da shekara ta zago aka kara haifan wani jaririn kuma, Sai Jibril ya sake dawowa ya maimaita k**ar yadda akayi a baya, sannan yace Allah ya yi umurni da ka saka ma yaronka sunan yaron Haruna, wato ‘Shubair’, sai Annabi ya kara neman ma’anarsa, sai Jibrilu (AS) yace masa “Husaini”. Mai karatu yana iya duba Littafin ( Zaka’iru Ukba, shafi na 120.)

Wannan ke nuna mana cewa sunan Imam Husaini (AS) zanannen suna ne da Allah (SWT) ya ma Annabi Muhammad (SAW) wahayinsa, kuma Annabi (SAW) ya rada masa wannan sunan da Izini kuma da umarnin Allah (SWT).

Hakan kuwa ya ishe Imam Husaini (RA) da ‘Dan’uwansa Imam Hasan (RA) girman daraja da matsayi da falala. Ance sunan Imam Husaini (AS) a cikin Attaura shine ‘Shubair’ din, a yayin da
kuma a cikin Injila aka kira shi da ‘D’aba’. Kenan sunan wannan bawan Allah din, tare da sauran zababbu ‘yan’uwan Sa (AS), rubutacce ne a cikin saukakkun littafan sama tun kafin a haifesu da shekaru masu yawan gaske.

ALKUNYARSA

Ana ma Imam Husain (RA) kinaya da alkunyu daban daban, amma wanda yafi shahara shi ne “Abu Abdullah”.Baya ga shi kuma ana ce masa “Abu Ali al-Asgar”, haka kuma ana kiransa da “Abul A’immah (RA)”.

LAKABOBINSA:

Lakabobin Imam Husaini (RA) kuwa suna da yawa, amma kadan daga cikinsu, sune: Al-Mubarak, As-Sibdi, Ar-Raheed, Ad-Dayyib, As-Sayyid, Raihanatun Nabiy (S), Al-Wafiy, Al-Zakiy, Al-Waliy, Sayyidus Shuhada, Sayyadis Shababu Ahlal Janna, Al-Waliyul Kabir. Da sauran lakabobi tabbatattu a gare shi da ake kiransa da su.

ZOBEN IMAM HUSAINI (AS) Imam Husaini (RA) ya na da zobe, kasancewar sanya zobe na daga Sunnar Manzon Allah (SAW) da Ahlulbait (AS), har ma ya zamana sanya zobe a hannun dama na daga cikin alamomi ko siffofin da ake gane mabiyan Ahlulbait (AS) a duk inda s**a tsinci kansu, musamman ma a lokutan baya. Dan haka a jikin zoben Imam Husaini (AS) an rubuta “-HasbiyalLah-” ne. Imam ya kasance daga cikin Sahabban Bargo, na’am, Ma’abota bargo su biyar ne, sune; Annabi (SAW) da Imam Ali da Sayyida Fatima da Imam Hasan da kuma Shi Imam Husaini (AS). Wadanna ma’abota bargo din, sune wadanda Allah (T) ya tafi da dauda da kazanta daga garesu, kuma ya tsarkake su tsarkakewa. Wanda akwai Hadisin Bargo (Hadisul Kisa’i) wanda aka ruwaito shi daga Sayyida Fatima Azzahara (SA).

Imam Husaini (AS) ya rayu tare da kakansa Manzon Allah (SAW) tsawon shekaru bakwai ne, dan haka ya kasance rainon Annabi (SAW) ne, kuma sanyin idanuwansa, kuma ma bangaren jikinsa mai albarka (AS).

Imam Husaini (AS) kuma ya rayu tare da Mahaifinsa Imam Ali (AS) shekaru talatin da bakwai. ya kuma rayu da ‘Dan’uwansa Imam Hasan (AS) shekaru Arba’in da bakwai. kuma tsawon
lokacin Imamancinsa da Halifancinsa na Manzon Allah (SAW) a bayan Yayansa Imam Hasan (RA) shi ne, shekaru goma da watanni.

HAIHUWARSA.

Dangane da haihuwar Imam Husaini (RA) kuwa; An haife shi ne a ranar 3 ga watan Sha’aban a shekara ta bakwai bayan Hijirar Manzon Allah (SAW).

Annabi Muhammad SAW a irin wannan rana Kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi ‘Dan Abbas (RA) a cikin littafin Fara’id-as-Simdain. Imam Husaini (RA) ya rayu watanni
shida ne a cikin Mahaifiyarsa, sai aka haife shi, k**ar yadda Muhammad bin Dalha As-Shafi’I ya ambata. Kuma dangane da
shi (Imam Husain) ne Allah (SWT) ya saukar da fadinsa “Da
daukan cikinsa da shayarwarsa watanni talatin ne.” Dan haka ma ma’abocin littafin( ‘al-Kamil-az-Zi yaaraat’) ya kawo maganar Imam Jafarus Sadik (RA) dake cewa: “Ba’a haifi wani abin haihuwa a cikin watanni shida ba, in banda Isa ‘Dan Maryam (AS) da Husaini ‘Dan Ali (RA).” Dama Maryam (AS) ta dauki cikin
Annabi Isa (AS) har na tsawon watanni 6 ne ba tare da an iya fahimtar hakan ba sai daga baya ta haife shi.

Imam Husaini (AS) yafi kowa k**a da Manzon Allah (SAW), musamman ma daga kirjinsa zuwa tafin kafansa, dukkansu
k**ar na Manzon Allah (SAW) ne. k**ar yadda kuma aka bamu labarin cewa Imam Hasan (RA) kuma yana k**a da Annabi
(SAW) ne daga kirjinsa zuwa samansa. Kuma Imam Husaini (AS) ya kasance matsakaici ne wajen tsawo, ba dogo bane ba kuma gajere bane. Yana da yalwar kirji. To kuma har wala yau
Imam Husaini (AS) yana k**a da Imam Ali (AS) ta samansa (daga kirji zuwa kai). Kunga kuwa ta ko ina ya kure ma kyau kenan MANZON ALLAH (SAW) YANA CEWA:
“Husaini daga ni yake, kuma ni ma daga Husaini nake. Allah ya so wanda yake son Husaini.”

Matsayin Imam Husaini (a.s)

Hakika Abu Abdullahi al-Husain (RA) na da babban matsayi.

Bayan ayoyin Alkur'ani da s**a ambaci matsayinsa cikin matsayin Ahlulbaiti (AS), wadanda muka ambata a baya, k**ar su Ayar Tsarkakewa, Ayar Mubahala, Ayar Kauna da sauransu; akwai hadisan Annabi masu yawa da ke nuna girman matsayinsa da daukakar darajarsa. Daga cikin su akwai:

1, Abin da ya zo cikin Sahih al-Tirmizi cewa: Manzon Allah (SAW) ya ce: "Husaini daga gare ni yake, ni kuma daga gare shi nake. Allah Ya so wanda ya so Husaini. Husaini jika ne daga cikin jikoki(2).

2, An ruwaito daga Salman al-Farisi, ya ce: na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: "Hasan da Husaini 'ya'yana ne, wanda ya so su ya so ni, wanda kuma ya so ni Allah zai so su wanda kuwa Allah Ya so zai shigar da shi Aljanna. Kuma wanda ya fusata su ya fusata ni, wanda kuma ya fusata ni Allah zai yi fushi da shi, wanda kuwa Allah Ya yi fushi da shi zai shigar da shi wuta(3)"

3, An ruwaito daga Ali bin Husaini daga babansa, daga kakansa (AS.), cewa Manzon Allah (SAW) ya k**a hannun Hasan da Husaini (AS) sannan ya ce: "Wanda ya so ni ya kuma so wadannan biyun da babansu da mamansu, zai kasance tare da ni ranar kiyama(4)".

Dabi'un Imam Husaini ( RA)

Hakika kasantuwan Imam Hasan (a.s) ya tashi ne karkashin kulawar kakansa Manzo (SAW), babansa Ali da mahaifiyarsa al-Zahara (AS), ta sa dabi'unsa na misalta sakon Allah Madaukaki a tunance, aikace da halayya. A nan za mu bayar da wasu 'yan misalai.

1- Shu'aib bin Abdul-Rahman ya ruwaito cewa: "An ga wani tabo a bayan Imam Husaini (RA) a Karbala; sai aka tambayi Imam Zainul-Abidin (RA) game da shi, sai ya amsa da cewa: "Wannan ya samo asali ne daga buhunan abinci da yake dauka a bayansa yana kai wa gidajen matan da mazansu s**a mutu da marayu da miskinai".

2- Ya taba bi ta wajen wasu miskinai alhali suna cin abinci a akushi, sai s**a yi masa tayi, sai ya sauka ya ce: "Lallai Allah ba Ya son masu girman kai", sai ya ci abincin. Sai ya ce musu: "Na amsa muku, to ni ma ku amsa min." Sai s**a amsa, s**a tafi tare da shi har zuwa gidansa, sai ya ce wa matarsa: "Fito da duk abin da kika adana (5)".

3- An taba ce masa: Me ka fi tsoro daga Ubangi-jinka? Sai ya ce: "Babu mai amintuwa daga ranar kiyama sai wanda ya ji tsoron Allah a duniya".

4- A daren goma ga watan Muharram Imam Husaini (a.s.) ya bukaci rundunar Umayyawa 'yan adawa, da su jinkirta masa wannan daren yana mai cewa: "Don muna so mu yi salla ga Ubangijinmu da daddare mu kuma nemi gafarar Sa, domin Shi ya san ni ina son yin salla gare Shi da tilawar LittafinSa da yawan addu'a da istigfari".

© Saliadeen Sicey

Soaking Of Beans In Water Before Cooking..Soaking of beans is what i discover and also what i have been doing for period...
07/08/2022

Soaking Of Beans In Water Before Cooking..

Soaking of beans is what i discover and also what i have been doing for period of time now..

Some people hardly cook beans because of how it consumes gas , firewood or kerosine, some of us are economize our gas or kerosine but try this ideas and see how it works and trust me it doesn't reduce the nutrients in anyway..

Soak your white or brown bean in normal water for less than 2 hours before cooking, soaking of beans reduce the hardness of it so once you cook it , it doesn't waste more time and your beans is done. and more benefits you have,it help in reducing the gas contacts in the beans .

Illar Ajino Moto (Kafi Zabo)Illar farin maggi ga rayuwar dan adam. Kamata yai ace duk fadin duniya bana nan gida Najeriy...
26/07/2022

Illar Ajino Moto (Kafi Zabo)

Illar farin maggi ga rayuwar dan adam. Kamata yai ace duk fadin duniya bana nan gida Najeriya ba a daina amfani da farin magi.Tabbas bincike ya nuna farin magi ko kafi zabo wanda ake kira a turance (monosodium glutamate) yana da matukar illa ga dan adam, babban illarsa k**ar haka:

Yana rage karfin namiji. ta hanyar kashe sinadarin dan adam. Sannan babbar illa ta biyu shine Yana rage kaifin kwakwalwa. Saboda haka k**ata kwata-kwata muguje shi, mu daina ammani dashi. Saboda haka akwai nau'uka na magi masu dama dama k**arsu maggi dunkule, Rayco da sauransu, inaga zai kyau ace su ake amfani dasu, suma Kada a cika sawa da yawa. daddawa ta gargajiya da ake ki' "itace kan gaba a wajen Amfani Da sa lafiya.

An hana amfani da maggin Ajinomoto a kasar Pakistan - a Ranar 3 Ga watan Maris 2018. Babban alkalin Pakistan Mai shari'a Mian Saqib Nisar ya haramta sayar da gishiri Ajinomoto na kasar Sin, lura da cewa yana da hadari ga lafiya.
Babban alkalin kotun ya ce ba za su yarda a sayar da gishirin ba.

A ranar 15 ga Janairu, Hukumar Abinci ta Punjab (PFA) ta haramta Ajinomoto bayan da hukumar ta gano yana da hadari ga lafiya.

A cewar PFA, gishirin ya ƙunshi Monosodium glutamate (MSG), mai ƙara dandano da aka ce yana haifar da asma, ciwon kai, har ma da lalacewar kwakwalwa.

A cewar wasu rahotanni, yin amfani da wannan sinadari na yau da kullum na iya haifar da al'amura na dogon lokaci k**ar hawan jini, Autism, rashin daidaituwa na hormonal, farfadiya, rashin lafiyar abinci, ciwon asma, ciwon daji na mahaifar mata.

Masana sun tabbatar da cewar maggin yana da babbar ila ga kwakwalwar mutum - An haramta yin amfani da maggin a kasashe da dama ciki kuwa harda kasar Amurka.

Kasashe k**ar China da Japan sun haramta amfani da ajinomoto a cikin kayan abinci.

An sanya dokar ta hana amfani Ajinomoto a cikin abincin jarirai da basu wuce wata 3 ba a kasar turai, da kuma rage yawan sanya shi a abinci a wasu kasashe 50.

© Harisu Sani Hayatu Sharada

26/07/2022

The pyrimidine analog 5-fluorouracil (5-FU) is metabolized by ribosylation and phosphorylation to the nucleotide level (F-UMP). F-UMP is further metabolized to F-dUMP, an inhibitor of thymidylate synthase. Cells then become starved for TTP and incorporate FdUTPand dUTPin its place in DNA. 5-FU also becomes incorporated in RNA, leading to inhibition of RNAprocessing. Anastrozole (choice A) is a nonsteroidal inhibitor of aromatase, an enzyme required for synthesis of estrogens. This drug is useful against advanced estrogen or progesterone receptor-positive breast cancer. Cytarabine (cytosine arabinoside, ara-C, choice B), is an S-phase-specific antimetabolite that is metabolized to the triphosphate form, which blocks DNAsynthesis. It is used exclusively in acute myelogenous leukemia. Doxorubicin (choice C) is an anthracycline antibiotic that intercalates into DNAcausing strand breakage and blockage of both DNAand RNAsynthesis. This agent is widely used in combination regimens for breast, endometrial, ovarian, testicular, and thyroid carcinomas, and several sarcomas and lymphomas. Imatinib (choice E) is an inhibitor of the tyrosine kinase activity of the Bcr-Abl oncogene product. It is a drug of choice in chronic myelogenous leukemia with the Philadelphia chromosome translocation.

26/07/2022

Who can and cannot take paracetamol?

Most people can take paracetamol safely, including pregnant and breastfeeding women.

However, some people need to take extra care with paracetamol.

Check with your doctor or pharmacist if you:

have had an allergic reaction to paracetamol or any other medicines in the past

have liver or kidney problems

regularly drink more than the maximum recommended amount of alcohol (14 units a week)

take medicine for epilepsy

take medicine for tuberculosis (TB)

take the blood-thinner warfarin and you may need to take paracetamol on a regular basis

Address

Kano

Telephone

+2347048991245

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zakari Ya'u Salisu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share