
11/10/2025
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yafewa Maryam Sanda, wadda aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2020, bayan samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello.
Maryam Sanda, mai shekaru 37, ta shafe shekaru 6 da watanni 8 a gidan gyaran hali na Suleja, kafin wannan lokaci da ta samu afuwa daga shugaba Tinubu.
A cewar mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga matakin ya biyo bayan shawarar kwamitin da shugaban kasa kan yafewa masu laifi ya bayar.