13/08/2026
YANZU-YANZU: Musulmi da Kirista Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Abuja
Musulmi da mabiya addinin Kirista sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da fahimtar juna, domin karfafa zaman tare da mutunta juna a tsakanin al’ummomin addinai biyu.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a yayin wani babban taron kasa da kasa da aka gudanar a Abuja, wanda ya hada da kungiyar , tare da halartar manyan malamai da wakilan addinai daga kasashe daban-daban na Afirka da Turai.
Jagororin Musulmi da wakilan kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) sun sanya hannu kan yarjejeniyar, wadda ke da nufin tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna da mutunta addinan juna.
A cewar rahoton Jibwis Nigeria, yarjejeniyar ba ta nufin Musulmi da Kirista su hade addinai ko su zama mabiya addini guda ba. Maimakon haka, manufarta ita ce kusantar juna, fahimtar koyarwar addinin juna da kuma girmama abin da kowane bangare ya yi imani da shi.
A yayin taron, jagororin bangarorin biyu sun kawo hujjoji daga Alkur’ani da Baibul, inda s**a bayyana abubuwan da ke karfafa fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista.
Shawarwarin da aka cimma a taron za a mika su ga gwamnati domin duba hanyoyin da za a karfafa su, musamman wajen magance wasu al’adu da dabi’un da ke haddasa rashin fahimta da rikici tsakanin Musulmi da Kirista.
Haka kuma, an wallafa wani kundin da aka tsara domin ya zama abin koyi da jagora wajen taimakawa wajen dakile duk wata arangama, kiyayya ko rashin fahimta tsakanin bangarorin biyu.
Taron ya kuma jaddada cewa ba alheri ba ne Musulmi ya tsangwami Kirista, ko kuma Kirista ya tsangwami Musulmi, musamman ganin cewa dukkansu ‘yan kasa daya ne kuma suna zaune tare a kasa guda.