10/01/2026
Arewa ta fara samun zarata masu basira
Matashi ɗan Zamfara Ya Ƙera Robot Mai Gano Gobara Da Gas Domin Kare Rayuka
Wani matashi mai basira daga Jihar Zamfara, Abdulbasid Dauda, ya ƙera wani robot na tsaro da aka tsara domin kare rayuka da dukiya ta hanyar gano hayakin gas da gobara tun kafin su haddasa babbar illa.
Abdulbasid ya bayyana cewa robot ɗin na da hankali na musamman (brain) da ke ba shi damar fahimtar magana tare da ba da amsa, lamarin da ya bambanta shi da sauran na’urorin tsaro na gargajiya.
Ya ce wannan ƙirƙira ta zo ne da nufin taimakawa al’umma, musamman wajen rage asarar rayuka da dukiya da gobara ko gas ke haddasawa, tare da ƙarfafa gwiwar matasa masu sha’awar kimiyya da fasaha.
Matashin inventor ɗin ya nemi goyon baya daga jama’a da hukumomi domin duba wannan ƙirƙira tare da yaɗa labarinta, domin ta samu ci gaba da kuma amfani ga al’umma baki ɗaya.
“Ina fatan wannan ƙirƙira za ta zama abin ƙarfafawa ga matasan Arewa da Najeriya gaba ɗaya,” in ji Abdulbasid Dauda.