03/12/2025
SENATOR SHEHU BUBA A MIZANI NA ADALCI
A cikin satan da ya gabata, Majalisar Dattawan Nigeria ta tsige Senator Shehu Buba daga mukamin Shugaban Kwamitin tsaro na Kasa da tattara bayanan sirri
A jiya sun bashi mukamin Shugaban kwamitin kiwo da dabbobi, Senator Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi shine zai jagoranci Kwamitin tsaro da bayanan sirri na Kasa a zauren Majalisar Dattawa
Me yasa Majalisar Dattawa ta tsige Senator Shehu Buba daga mukaminsa na Shugaban Kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri?
(1) Senator Shehu Buba bafulatani ne daga jiharmu na Bauchi, shine Senator da yake wakiltar Bauchi ta kudu, tun kafin ya zama Senator yana da alaka ta sulhu tsakaninsa da barayin daji masu garkuwa da mutane bisa amincewar Gwamnatin tarayya
(2) Ya taka rawa sosai wajen hana 'yan uwansa kabilar fulani wadanda s**a dau makami suna ta'addanci da sunan daukar fansa, kuma mafi yawansu suna jin maganarsa, ya taimaka wajen kubutar da mutane, akan haka wasu s**ayi ta zarginsa bisa kuskure cewa yana tare da bandits alhali ba haka bane, duk abinda yayi da sanin masu iko da tsaro na Kasa
(3) Sai dai abinda watakila shi kansa Senator Shehu Buba bai gano ba shine kungiyoyin ta'addanci masu ikrarin kafa Gwamnatin Musulunci musamman Ansaru sun jima da yiwa fulanin daji kutse, shiyasa aka samu babbar gazawa a batun yin sulhu da 'yan ta'adda, ko da anyi sai abin ya wargaje, hakan ya haifar wa Shehu Buba matsala a aikinsa
(4) Munanan hari da garkuwa da mutane musamman daliban makarantar kwana da fulani barayin daji s**ayi bayan gargadi Amurka, faruwar haka ya sa Gwamnatin tarayya ta lura da rashin kwazon Senator Shehu Buba, wato bai taka rawa wajen hana faruwar harin ba da kuma kubutar da daliban da aka k**a ba, hakan yasa s**a saukeshi daga mukaminsa
A cikin bayanai guda biyar da na ambata a sama, zaku fahimci wasu daga cikin dalilan da yasa aka saukeshi daga mukaminsa na Shugaban Kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri na Kasa a Majalisar Dattawa
Muna fatan Allah Ya sa hakan ya zama alheri wa tsaron Nigeria