
20/08/2024
Ambaliya na iya ta'azzara matsalar karancin abinci a Najeriya - Masana
Masana harkar noma na bayyana fargabar cewar akwai alamar fuskantar karin karancin abinci a Najeriya sakamakon fari da kuma ambaliyar da aka samu a wasu jihohin arewacin kasar. Masanan sun ce ya yin da wasu jihohin ke gudanar da addu'oin samun ruwan sama, yanzu haka an samu ambaliya a jihohi 10 wadanda ruwan saman ya yiwa matukar illa wajen wanke gonaki da kuma gidaje. Wadannan jihohi da s**a yi fice wajen noma sun hada da Kaduna da Kano da Jigawa da Nasarawa da Bauchi da Zamfara da Yobe da Sokoto da kuma Kebbi.
📷 Daily Trust