NASAD TV

NASAD TV Shafi Ne Dazai Dunga Kawo Muku Abubuwan Dasuka Shafi Rayuwarmu Na Yau da Kullum✅

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard!Sale Umar Dandume, Bala Balancy, Nura Abdukarim, Yahaya Za...
06/08/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard!

Sale Umar Dandume, Bala Balancy, Nura Abdukarim, Yahaya Zayyanu, Abba Musa

06/08/2025

Gumin Jikinsa Yafi Turare Qamshi, Fuskarsa Tafi Kyau Kyawu,

Idan Yayi Magana Ba'a Mantawa Sabida Dadinta Habibi Rasulullah ﷺ 💖

05/08/2025

Allah ka jikan Sheak Jafar

Adam Kano 🤲

RUKUNNAN HALAYE NAGARI DA MUNANA. -"Kyawawan halaye suna ginuwa a kan rukuni guda huɗu. Ba za a iya samun nagartattun ha...
05/08/2025

RUKUNNAN HALAYE NAGARI DA MUNANA.
-
"Kyawawan halaye suna ginuwa a kan rukuni guda huɗu. Ba za a iya samun nagartattun halaye ba sai da waɗannan rukunan:
-
Haƙuri.
Kunya.
Jarumta.
Adalci.
-
RUKUNNAN KYAWAWAN HALAYE:
-
1. Haƙuri (الصبر):
Yana ɗauke da jimrewa, da iya daure zuciya da hakuri akan cuta da wahala da kunci, da kaucewa fushi da gaggawa.
-
2. Kunya (العفة):
Yana ɗauke da nisantar alfasha da ɓatanci a maganganu da ayyuka, da tsoron Allah, da tsaftace zuciya da abinci da sha da sha’awa.
-
3. Jarumta (الشجاعة):
Yana ɗauke da ƙarfin zuciya da ƙima, da yin abin da ya dace, da juriya, da tsayawa da gaskiya, da jin tsoron Allah, da amana.
-
4. Adalci (العدل):
Yana ɗauke da daidaito a cikin halaye da ayyuka, ba tare da kaucewa ga ɓangare ɗaya ba. Daidai ne tsakanin ƙarancin aiki da yawan aiki.
-
RUKUNNAN HALAYE MUNANA:
-
"Wannan kuwa shi ne tushen dukkan munanan halaye, kuma su ma suna ginuwa a kan rukuni huɗu:
-
Jahilci.
Zalunci.
Sha'awa.
Fushi.
-
1. Jahilci (الجهل):
Yana kore gaskiya, da son bin ra’ayin kai, da kaucewa ilimi da hikima da daidaito.
-
2. Zalunci (الظلم):
Yana ɗauke da cin zarafin mutane, da cin haƙƙin su, da rashin adalci a cikin ayyuka.
-
3. Sha’awa (الشهوة):
Yana ɗauke da son jin daɗi da bin zuciya da jiki, da lalata da alfasha da ƙazantar hali.
-
4. Fushi (الغضب):
Yana ɗauke da girman kai da zagi da tsanantawa da cin mutunci da saurin jin haushi.

A Izala babu shirka. A izala babu dan tsibbu.A Izala babu boka. A Izala babu masu shan giya. A Izala babu masu cewa kowa...
03/08/2025

A Izala babu shirka.
A izala babu dan tsibbu.
A Izala babu boka.
A Izala babu masu shan giya.
A Izala babu masu cewa kowa Allah ne.
A Izala babu masu zagin sahabbai.
A Izala babu masu bautar kabari.
A Izala babu karyata maganar Annabi s.a.w
A Izala babu masu wakar nanaye.
A Izala babu cakuda maza da mata.

KUCE ALHAMDULILLAH. 🙏 Sunnah sak 💯

03/08/2025

El-Basheer Haruna Sumaila

ZIKIRAI GUDA BAKWAI (7) MAFI TSADA A RAYUWAR MUSLIMI1- MAFIFICHIN AMBATON ALLAH_Laa ilaha illallaahu  wahdahu lā shariyk...
02/08/2025

ZIKIRAI GUDA BAKWAI (7) MAFI TSADA A RAYUWAR MUSLIMI

1- MAFIFICHIN AMBATON ALLAH

_Laa ilaha illallaahu wahdahu lā shariyka lahu lahul-mulku wa lahul hamdu wa huwa alā kulli shay'en Qadiyr_

2- MAFIFICIN TASBIHI

_Subhanallaahi wabihamdihi adada khalQihi waridā nafsihi wazinata arshihi wa midāda kalimatihi_

3- MAFIFICIYAR ADDUA

_rabbana ātina fiy-dduniyā hasanataw-wafil akhirati Hasanah, waQinā azabanNār_

4- MAFIFICIN ISTIGHFARI

_Allaahumma anta rabbiy lā ilaha illā anta khalaQ-taniy, wa'ana abduka, wa'ana alā aHdika, wa-wa' dika masta-'da at, a-uzubika min sharri ma sana'ata, abū Ula-ika bini'-matika ãlayya, wa-abu'u bizambiy, Fagfirliy fa-innahu Lā yagfiruz-Zunuba illa ant_

5- MAFIFICIN NEMAN KARIYA DA TSARI

_Bismillaahilladziy Lā yadurru ma-asmihi shay'un fiyl-ardhi walā fiys-Samā' , wa huwassamiy'un alaiym_

6- MAFIFICIN ZIKIRIN NEMAN YAYE DAMUWA DA BAKIN CIKI

_Lā ilaHa illa anta subhānaka inniy kuntu minaz-Zālimiyn_

7- MAFI ZIKIRIN DOGARO GA ALLAH DA SALLAMAWA A GARESHI

_Lā haula wala Quwwata Illa billaahil aliyyil aziym_

ALLAH KA BAMU IKON DAUWAMA AKAN YAWAITA AMBATON KA A KOWANE
LOKACI.

Allahumma Ameen.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NASAD TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to NASAD TV:

Share

Category