10/06/2025
Ya ce, bayan ɗaura aure Sirikarsa ta kira shi ta ce masa, Ka yi ƙoƙari matuƙa wajen ganin ka kula da yarinyar nan sosai, kar ka yadda ka bari ta yi fushi ko kuma ranta ya baci.....
Ya ce, wannan ba wani abin mamaki bane, domin irin wannan wasiyar alherin kowace uwa take yi......
Bayan shekara 3, muka samu ƴar jayayya kan abin da yake ni ne ba a kan gaskiya ba. Ya kamata da na fuskanci haka, na bata haƙuri don samun maslaha amma ban aikata ba....!
Ya ce, bayan na dawo daga aiki sai naga tana bina da wani irin kallo, wanda bata taba yi mini irinsa ba
Wani lokacin sai ta zauna a bakin ƙofa, ta zuba min na mujiya ko ƙiftawa bata yi.....
Na shiga wanka, bayan na fito sai na ganta a tsaye a ƙofar banɗaki tana ta kallona kallo mai ban tsoro
Sbda gajiya, ina kwanciya sai barci, yunwa ta sanya na kwanta barci. Ina farkawa sai na ganta a tsaye a kaina a gefen Gado ta ƙura mini Ido...... Wannan ya tsoratani sosai...
Cikin hali na firgici da jin tsoro na kira Mahaifiyarta a waya, na fara bata labarin ɗan sabanin da muka samu, kafin na gaya mata abubuwan da suke bani tsoro sai ta buɗe baki ta ce: "Ba na gaya maka kar ka bari ta yi fushi ko ranta ya baci ba.."!?
Cikin mamaki da firgita ya ce, ta ya ya kika san da wannan matsalar...!?
Mahaifiyar ta ce, yau kwanan Matarka biyu a gurina me yasa baka zo neman sulhu ba....!!!