Tambihi da Tunatarwa

  • Home
  • Tambihi da Tunatarwa

Tambihi da Tunatarwa Manufar wannan Shafi itace yaɗa Sunnar Manzon Allah (S.A.W) gwargwadon fahimtar magabata na ƙwarai.

TSOKACI AKAN QUR'AN DAY DA AMARE SUKE SHIRYAWA 1. A yayin shagulgulan biki, abubuwa da dama sun halatta musamman ga mata...
25/01/2025

TSOKACI AKAN QUR'AN DAY DA AMARE SUKE SHIRYAWA

1. A yayin shagulgulan biki, abubuwa da dama sun halatta musamman ga mata da yara matuƙar dai ba'a ƙetare iyaka wajen aikatasu ba. Babbar matsalar da muke fuskanta itace rashin kiyaye ladubban shari'a tareda koyi da yahudawa a yayin shagulgulan bukukuwan mu.

2. "Qur'an day" yini ne da ake shiryawa a yayin shagulgulan biki, amarya da ƙawayenta suna yin shiga ta kamala. Suna rarraba Alƙur'ani (juz'i- juz'i) a wajen domin a karanta, ko kuma asamu waɗansu da s**a iya karatun Alkur'ani su rera shi da kyakkyawan sauti. Wannan babu laifi.

3. Galibi matan da suke shirya wannan yini basa rasa alaƙa da karatun islamiyya ko na Tahfeez. Kuma babu shakka shi wannan yini yafi taron kaɗe-kaɗe (Dj) da raye-raye, Arabian Night da sauran nau'ukan ƙetare iyaka.

4. Shi a karan kansa "Qur'an day" ɗin al'ada ce mai kyau amma baya daga cikin karantarwar sunnah don haka babu wani lada na musamman da za'a baiwa mutum don ya halarci "QUR'AN DAY" face ladan karatun Alkur'ani idan anyi da ikhlasi. Duk Amaryar da take son dacewa da karantarwar sunnah a yayin shagalin bikinta sai ta shirya walima daidai gwargwadon ikonta.

5. Akwai wasu abubuwa goma (10) marasa kyau da a tareda wannan sabuwar al'ada ta "QUR'AN DAY". Sun haɗarda:

i. Maye gurbin walima da "Qur'an Day" ma'ana ɗaukar "QUR'AN DAY" a matsayin ibada.
ii. Shigar maza wurin wannan taro koda kuwa mahaifin amaryar ne.
iii. Cire shigar kamala yayin da aka tashi za'a tafi gida. Mace tazo da hijabi ta koma gida da gyale.
iv. Mayar da hankali akan ɗaukar hoto amadadin karatun.
v. Ɓarnatar da kuɗi masu yawa don ƙayatar da taron.
vi. K**a Event hall domin yin wannan yini wanda hakan zai buɗe ƙofofin fitina.
vii. Kunna kiɗa da raye-raye a ƙarshen karatun.
viii. Kallafawa kai da ɗaukarsa a matsayin wajibi.
ix. Wasa, ihu, ko surutu a yayin gudanar da karatun.
x. Zargi ko aibata wacce bata yi ba ko bata halarta ba.

6. Allah yayi riƙo da hannayenmu.

✍️
Umar Sa'ad Abdullahi
25/01/25

طوبى لمن أصلح نفسه قبل رمضان
22/01/2025

طوبى لمن أصلح نفسه قبل رمضان

15/12/2024

'Yar uwa mace: ki sani cewa duk duniya babu wanda zai tsare miki mutuncinki kamar yadda zaki tsare wa kanki da kanki.

DOMIN KYAUTATA AMFANI DA SOCIAL MEDIA Assalamu alaikum warahmatulLah, barkan mu da wannan yini na Juma'a mai albarka. In...
22/11/2024

DOMIN KYAUTATA AMFANI DA SOCIAL MEDIA

Assalamu alaikum warahmatulLah, barkan mu da wannan yini na Juma'a mai albarka. Ina farin cikin gabatar muku da wani ɗan takaitaccen nazari domin masu amfani da kafofin sadarwa na zamani wato "Social Media".

Wannan nazarin yana ƙunshe da muhimman batutuwa da yakamata mu kiyaye game da alfanu, illoli, sirrika, ladubba, da shawarwari domin kyautata amfani da wannan saha ta zamani tareda cin moriyarta.

Inshaa Allah, wannan aiki zai kammala nan da ranar Juma'a mai zuwa, duk mai sha'awar karantawa zai sami softcopy a ranar.

Allah ya bamu sa'a!

✍️
Umar Sa'ad Abdullahi
Fri, 22 Nov. 24

20/11/2024
26/10/2024

Riƙo da Sunnah:

Mataki na farko sai ka fara ƙundurcewa a ranka cewa koyarwar manzon Allah (ﷺ) itace mafificiya.

Duk aninda yake bugarwa sunansa "GIYA" kuma haramun ne a musulunci koda kuwa ba sunansa "GIYA" ba, dole ne ya amsa sunan...
21/10/2024

Duk aninda yake bugarwa sunansa "GIYA" kuma haramun ne a musulunci koda kuwa ba sunansa "GIYA" ba, dole ne ya amsa sunan "GIYA" saboda bugarwa da yake yi.

20/10/2024

Lafazin iƙāmar Sallah:

- ƙad ƙāmatis-Sallātu ❌
- ƙad ƙāmatis-Salātu ✅
(Ba'a cewa SALLATU)

Ƙwarai kuwa! Shaiɗan ne kaɗai yake baƙin ciki da samuwar fiyayyen halitta, daga shi sai kafirai 'yan fadarsa.Amma batun ...
15/09/2024

Ƙwarai kuwa! Shaiɗan ne kaɗai yake baƙin ciki da samuwar fiyayyen halitta, daga shi sai kafirai 'yan fadarsa.

Amma batun dai har ila yau shine, bikin Mauludi daban murna da samuwar fiyayyen halitta daban.

Idan da bikin mauludi shine hanyar murna da samuwar fiyayyen halitta, da Sahabbai, Ahalul baiti da tabi'ai da malaman Musulunci Magabata su za'a fara tuhuma da ƙiyayya ga manzon Allah (S.A.W).

Yadda Al'amarin yake, sun fimu tsananin murna da samuwar fiyayyen halitta, amma basa Mauludi saboda Maulidin ba addini bane.

✍️
Umar Sa'ad Abdullahi

14/09/2024

Idan da Alkhairi ne da Sahabbai sun rigaye mu wajen aikata.

Yau (Juma'a) rana ce da sunnah ta koyar da riɓanya salati ga Manzon Allah (S.A.W) a cikinta.
13/09/2024

Yau (Juma'a) rana ce da sunnah ta koyar da riɓanya salati ga Manzon Allah (S.A.W) a cikinta.

07/09/2024

Hukuncin tafiye-tafiye domin wa'azi ko da'awah ga Mata.

Address


Telephone

+2349060264806

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tambihi da Tunatarwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Tambihi da Tunatarwa:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share