04/08/2026
GWAMNA ABBA KABIR YUSUF YA TSAYA DA KANSA YANA SA IDO KAN BIN DOKOKIN ZIRGA-ZIRGA A KANO
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci aikin sa ido kan bin dokokin zirga-zirga a mahadar Kofar Fanfo, inda ya shafe sama da awa guda yana tabbatar da cewa direbobi da masu amfani da hanya suna mutunta fitilun kula da zirga-zirga.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Talata.
A cewar sanarwar, gwamnan ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihar, kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati yayin wannan aiki, wanda aka shirya domin ƙarfafa bin doka da dawo da da’a a harkokin zirga-zirga a faɗin jihar.
Gwamna Yusuf ya yi kira ga direbobin motoci masu zaman kansu, direbobin motocin haya, masu tuka babura masu ƙafa uku (Adaidaita Sahu), da kuma masu tafiya a ƙasa da su riƙa mutunta fitilun hanya tare da bin dukkan ƙa’idojin zirga-zirga.
Ya bayyana cewa bin dokokin zirga-zirga na taka muhimmiyar rawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da rage hatsarurrukan hanya.
Hakazalika, gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jihar na shirin sake fasalin Hukumar Kula da Zirga-zirga ta Jihar Kano domin ƙara mata ƙwarewa da inganta ayyukanta wajen tabbatar da tsaro da daidaiton zirga-zirga.
Tambaya ga masu karatu:
Me za ka ji idan ka hangi gwamnan jiharka ya tsaya da kansa a kan t**i yana sa ido kan bin dokokin zirga-zirga da tabbatar da tsari?
Ka bayyana ra’ayinka a sashin sharhi.