Muryar Arewa News

Muryar Arewa News 📰 Muryar Arewa News
Sahihan labarai daga Najeriya da duniya. Siyasa | Tsaro | Kasuwanci | Wasanni | Nishaɗi | Ra'ayoyi.

Gaskiya, Sahihanci da Aminci su ne ginshiƙanmu

HOUTHI SUN YI IKIRARIN KAI HARI KAN WATA CIBIYAR MAKAMASHI A SAUDI ARABIAƘungiyar Houthi ta Yemen ta yi ikirarin cewa ta...
04/10/2026

HOUTHI SUN YI IKIRARIN KAI HARI KAN WATA CIBIYAR MAKAMASHI A SAUDI ARABIA

Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta yi ikirarin cewa ta kai hari kan wata cibiyar mak**ashi da ke Saudi Arabia, yayin da faɗan da ake yi a Yemen ke ƙara tsananta.

Houthi ta ce ta yi amfani da mak**ai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa wajen kai harin.

Ƙungiyar ta kuma ce harin ya zo ne a matsayin martani ga hare-haren da ake zargin an kai kan yankunan da take iko da su a Yemen.

Sai dai hukumomin Saudi Arabia ba su tabbatar da cikakken bayanin da Houthi ta bayar game da harin ba.

Rikicin Yemen ya daɗe yana ci gaba, kuma ƙara tsanantar fadan na haifar da ƙarin damuwa kan tsaro da kuma zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin Bahar Maliya.

MURYAR AREWA NEWS

SOJOJIN SUDAN SUN KWACE CIKAKKEN IKON AL-MAZROUBRundunar sojin Sudan ta sanar da cewa ta karɓi cikakken iko da garin Al-...
02/10/2026

SOJOJIN SUDAN SUN KWACE CIKAKKEN IKON AL-MAZROUB

Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa ta karɓi cikakken iko da garin Al-Mazroub, da ke jihar North Kordofan, bayan kazamin faɗa da rundunar RSF.

Kakakin rundunar musamman ta sojin Sudan, Mohamed Deidan, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa dakarun sojin sun yi nasarar kwace garin bayan arangama mai tsanani da mayaƙan RSF.

Deidan ya bayyana cewa ƙwace Al-Mazroub wani muhimmin mataki ne ga sojojin Sudan, musamman wajen ƙoƙarin katse hanyoyin samar da kayayyaki ga RSF.

Ya ce garin yana da muhimmiyar alaƙa tsakanin North Kordofan da West Kordofan, lamarin da ya sa yake da matuƙar muhimmanci a fagen yaƙin.

A cewar kakakin, nasarar da sojojin s**a samu a Al-Mazroub ta sauya yanayin yaƙin da ake ci gaba da yi a yankin Kordofan.

SOJOJI SUN TARWATSA MABOYAR ’YAN TA’ADDA A ANAMBRA, SUN KWATO MAKAMAIRundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarunta na Operat...
02/10/2026

SOJOJI SUN TARWATSA MABOYAR ’YAN TA’ADDA A ANAMBRA, SUN KWATO MAKAMAI

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation UDO KA sun tarwatsa wata maboyar ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a jihar Anambra, inda s**a kuma ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su.

Sojojin Bataliya ta 185, tare da haɗin gwiwar Anambra Vigilante Group, sun gudanar da aikin ceto bayan da aka yi garkuwa da wasu mutane uku a yankin Osakwa da ke ƙaramar hukumar Ihiala.

A ranar 1 ga Oktoba, 2026, sojojin sun k**a wani mutum da ake zargi da hannu a cikin garkuwar, mai suna Sunday Obi.

A lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya bai wa sojojin bayanai da s**a taimaka wajen gano inda maboyar ƙungiyar take a Abator, ƙaramar hukumar Ogbaru, bayan mashigar ruwan Isieke.

Bayan samun bayanan, sojojin sun kai samame zuwa wurin da kwale-kwale, inda s**a isa maboyar s**a yi artabu da ’yan ta’addan. Rundunar ta ce ’yan ta’addan sun gudu bayan wasu daga cikinsu sun samu raunukan harbin bindiga.

MAKAMAI DA KAYAYYAKIN DA AKA KWATO

Sojojin sun ce sun kwato:

- Bindigogin AK-47 guda 2 da harsashensu
- Bindigogin Pump Action guda 3
- Bindigogin ƙera gida guda 3
- Harsasan bindiga 7.62mm NATO guda 62
- Harsasan 7.62mm Special guda 149
- Cartridges guda 2
- Kayayyakin da ake zargin za a yi amfani da su wajen ƙera bama-bamai
- Na’urar samar da wutar lantarki ta hasken rana
- Power bank
- Batirin mota guda 1
- Batirin babura guda 2
- Solar panels guda 2
- Wayoyin hannu guda 2

Rundunar ta ce waɗannan kayayyakin sun nuna irin kayan aikin da ƙungiyar ke amfani da su wajen gudanar da ayyukanta.

Sojojin sun kuma ce suna ci gaba da neman ’yan ta’addan da s**a tsere, da kuma mutanen da ke taimaka musu ko samar musu da mak**ai da sauran kayan aiki.

Rundunar Operation UDO KA ta ce za ta ci gaba da gudanar da samame da ayyukan leƙen asiri domin tarwatsa maboyar ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane tare da kare al’ummomin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
HQ Nigerian Army Nigerian Navy Nigeria Security and Civil Defence Corps

02/10/2026

WANAN SHINE VIDEO WANI MATASHI DAN ASALIN KASAR SENEGAL DAKE IYA KWAIKAWON MURYAR BABBAN LIMAMIN MASALLACIN HARAMI WATO SHEKHE ABDURAHAMN SSUDAIS

SOJOJIN OPERATION HADIN KAI SUN KASHE 'YAN TA'ADDA 16, SUN KWATO MAKAMAI A ADAMAWARundunar haɗin gwiwa ta Operation HADI...
01/10/2026

SOJOJIN OPERATION HADIN KAI SUN KASHE 'YAN TA'ADDA 16, SUN KWATO MAKAMAI A ADAMAWA

Rundunar haɗin gwiwa ta Operation HADIN KAI (OPHK) ta ce ta samu gagarumar nasara a hare-haren da ta kai kan 'yan ta'adda a sassan Sector 4 na jihar Adamawa.

Rundunar ta bayyana cewa ayyukan sojojin, waɗanda s**a gudana tsakanin 30 ga Satumba zuwa 1 ga Oktoba 2026, sun kai ga kashe wasu daga cikin 'yan ta'addan tare da kwato mak**ai da alburusai.

A yankin Boima na ƙaramar hukumar Gombi, sojojin sun yi wa wata ƙungiyar 'yan ta'adda kwanton bauna, inda s**a ce an kashe 'yan ta'adda 16.

Bayan arangamar, sojojin sun kwato bindigogin AK-47 guda uku, bindigogin pump-action guda biyu da bindigar Dane guda ɗaya, da kuma magazinan AK-47 guda shida tare da harsasan bindigar pump-action.

HARE-HAREN JIRAGEN SAMA

Rundunar ta kuma ce da sanyin safiyar 1 ga Oktoba, wani jirgin leƙen asiri ya gano wasu mutane kimanin 16 da ake zargin 'yan ta'adda ne, suna taruwa tare da babura 15 a ƙarƙashin bishiyoyi a Sector 4.

Da misalin ƙarfe 5:30 na safe, rundunar sama ta kai musu hari, inda ta ce harin ya samu nasara tare da lalata wurin da aka nufa.

'YAN TA'ADDA SUN KAI HARI KAN BARIKIN SOJOJI

A wani ɓangare kuma, 'yan ta'adda sun kai hare-hare kan sansanonin sojoji da ke Bataliya ta 226 a Garkida da Bataliya ta 232 a Garaha.

Rundunar ta ce sojojin sun mayar da martani mai ƙarfi, lamarin da ya tilasta maharan dakatar da harin tare da tserewa.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa sojoji uku sun rasa rayukansu yayin fafatawar, yayin da wasu sojojin da s**a samu raunuka aka kai su asibiti, kuma suna cikin halin kwanciyar hankali.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan share fage da bincike a yankunan da lamarin ya faru.

Rundunar Operation HADIN KAI ta ce za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri, fasaha da haɗin gwiwar rundunonin ƙasa da na sama domin hana 'yan ta'adda samun damar gudanar da hare-hare a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

A yayin da Najeriya ke bikin Ranar 'Yancin Kai, rundunar ta ce sojojinta sun ƙudiri aniyar ci gaba da kare ƙasar da kuma samar da yanayin da zai taimaka wajen samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a yankin.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama'a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai kan duk wani abu da suke zargi.
HQ Nigerian Army MTN Nigeria Nigerian Navy

30/09/2026

JAWABIN DAN TAKARAR GUMBAN JIHAR GOMBE KENAN WATO MALAM ISA ALI IBRAHIM PANTAMI BAYAN SAKE ZABARSA DA JAMIYYAR PDP TAYI A JIHAR BIYO BAYAN UMARNIN KOTU NA SAKE ZABEN FIDDA GWANI

KAMENEI YA CE IRAN TA ƘARA ƘARFI, TANA DAGA CIKIN MANYAN ƘASASHE A DUNIYAJagoran Ƙoli na Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayy...
29/09/2026

KAMENEI YA CE IRAN TA ƘARA ƘARFI, TANA DAGA CIKIN MANYAN ƘASASHE A DUNIYA

Jagoran Ƙoli na Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayyana cewa Iran ta ƙara ƙarfi bayan shekaru tana fuskantar yaƙe-yaƙe da matsin lamba daga ƙasashen duniya, yana mai cewa ƙasar tana daga cikin manyan ƙasashe masu ƙarfi a duniya.

Khamenei ya ce Iran tana samun ci gaba, mutunci da kuma 'yancin kai, tare da samun matsayi mai ƙarfi a tsakanin ƙasashen Musulmi da ma sauran ƙasashen duniya.

Ya bayyana hakan ne a wani saƙon da ya rubuta domin tunawa da ranar cikar shekarun fara yaƙin Iran da Iraki.

A cikin saƙon, Khamenei ya ce: “A yau, wasu suna ganin mu a matsayin ƙasa ta huɗu mafi ƙarfi a duniya.”

Ya ƙara da cewa, bisa abin da ya kira “ƙididdigar Allah”, Iran ita ce “ƙasa mafi ƙarfi a duniya.”

Sai dai wannan ikirari na Khamenei na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tantance ƙarfin Iran ta fuskar tattalin arziki da soji, da kuma irin tasirin da take da shi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Mojtaba Khamenei ya zama Jagoran Ƙoli na Iran sama da watanni shida da s**a gabata, amma tun bayan hawansa wannan matsayi, bai fito fili ya bayyana a gaban jama'a ba.

29/09/2026

SARKIN KANO AMINU ADO BAYERO YA YI RANGADI A CIKIN UNGUWANNIN KANO

KANO: Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gudanar da rangadi da ziyara a wasu sassa na birnin Kano, inda ya gana da al’umma tare da halartar tarukan addini.

A yayin rangadin, Sarkin ya kai ziyara cikin wasu unguwanni, inda jama’a s**a fito domin tarbar sa da kuma gabatar da gaisuwa da addu’o’i.

Daga cikin muhimman abubuwan da s**a sanya rangadin ya dauki hankali akwai halartar Sarkin wani taron saukar karatun Alƙur’ani mai girma da aka gudanar a Goron Dutse, a gidan marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu.

Rahotanni sun bayyana cewa an shirya taron ne domin gudanar da addu’a ta musamman, inda Sarkin ya isa wurin tare da rakiyar jama’a da dama. Masu halartar taron sun tarbe shi cikin girmamawa, yayin da aka gudanar da karatun Alƙur’ani da addu’o’i.

Haka kuma, a wani lokaci daban, mazauna wasu unguwanni ciki har da Sorron Dinki, Gwangwazo, Kankarofi da Kabara sun kai ziyara fadar Sarkin, inda s**a gabatar da gaisuwa tare da addu’o’i.

Rangadin ya kuma kasance wata dama ta sada zumunci tsakanin masarauta da al’umma, musamman ganin muhimmancin irin wadannan ziyara wajen karfafa alakar gargajiya da jama’ar Kano.

Muryar Arewa News

IRAN TA CE TA SHIRYA DON KOMAWAR YAKI DA AMURKA, AMMA HAR YANZU TANA SON DIFLOMASIYAMinistan Harkokin Wajen Iran, Abbas ...
27/09/2026

IRAN TA CE TA SHIRYA DON KOMAWAR YAKI DA AMURKA, AMMA HAR YANZU TANA SON DIFLOMASIYA
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce Iran ta “shirya tsaf” idan har yakin da Amurka ya sake barkewa, yana mai cewa Tehran za ta tsaya tsayin daka ko da lamarin ya kai ga abin da ya kira “yakin ranar kiyama” (doomsday war).

Araghchi ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin Meet the Press na NBC a ranar Lahadi, inda ya ce Iran a lokaci guda tana nan a shirye domin ci gaba da diflomasiyya.

“Mun shirya tsaf domin a sake komawar yakin. Za mu tsaya tsayin daka a gaban duk wani sabon hari, ko da hakan zai kai ga yakin ranar kiyama,” in ji Araghchi.

Ya kara da cewa “har yanzu muna shirye domin diflomasiyya. Ya rage ga Shugaba Trump ya zaba.”
BATUN MASHIGAR RUWAN HORMUZ
Araghchi ya ce duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya yi watsi da shawarar Iran, Tehran har yanzu tana jiran amsar Amurka a hukumance ta hannun masu shiga tsakani.
A cewarsa, shawarar Iran ta kunshi sake bude mashigar ruwan Hormuz bayan Amurka ta dauki wasu matakai, sannan a koma tattaunawa kan yarjejeniyar karshe a rana ta bakwai.

Ya ce Iran na bukatar a saki kadarorinta da aka daskarar tare da ba ta damar ci gaba da sayar da man fetur
URANIUM DIN DA AKA INGANTA ZUWA KASHI 60%
Ministan ya kuma ce tarin uranium da Iran ke da shi wanda aka inganta shi zuwa kashi 60% na iya zama wani batu a tattaunawar gaba, idan Washington ta nuna abin da ya kira “kyakkyawar niyya” da kuma “ainihin kudurin samar da zaman lafiya.”

Rahotanni sun nuna cewa, duk da tsauraran kalamai daga bangarorin biyu, har yanzu akwai yiwuwar ci gaba da tattaunawar diflomasiyya tsakanin

AMURKA TA CE SHAWARAR IRAN TA TSAGAI DA WUTA YANA DA MANUFA TA SAMUN RAGIN TAKUNKUMIJakadan Amurka a Majalisar Dinkin Du...
27/09/2026

AMURKA TA CE SHAWARAR IRAN TA TSAGAI DA WUTA YANA DA MANUFA TA SAMUN RAGIN TAKUNKUMI

Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Mike Waltz, ya ce shawarar Iran ta tsagaita wuta na tsawon kwanaki bakwai wata hanya ce da Tehran ke kokarin amfani da ita domin samun sassaucin takunkumi, kawo karshen katangewar Amurka da kuma samun damar kwato biliyoyin dalolin kadarorinta da aka daskarar.

Waltz ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da shirin Meet the Press na NBC a ranar Lahadi.

Ya ce gwamnatin Shugaba Donald Trump ba ta da cikakken yakinin cewa Iran za ta mutunta wata sabuwar yarjejeniya, musamman bayan abin da Washington ta ce ya faru a wata yarjejeniya da aka cimma a baya.

A cewarsa, Amurka na zargin Iran da karya yarjejeniyar fahimtar juna ta baya bayan da aka kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasa da kasa.

Da aka tambaye shi kan rahoton Wall Street Journal cewa Trump na shirin sake dawo da hare-haren Amurka kan Iran bayan zaben tsakiyar wa’adin majalisar dokokin Amurka na watan Nuwamba, Waltz ya ce rahoton ya dogara ne kan bayanan wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba.

Sai dai ya jaddada cewa Shugaba Trump zai bar dukkan zabukan da suke gabansa a bude.

Waltz ya kuma ce duk wata yarjejeniya da Iran za ta cimma da Amurka dole ta magance batun uranium din da Iran ta inganta zuwa mataki mai yawa, da kuma damar da Tehran ke da ita ta sake fara aikin inganta uranium.

A baya, Waltz ya ce Washington ta taba ba Tehran shawarar sayar mata da uranium, a matsayin wani bangare na kokarin warware takaddamar shirin nukiliyar Iran.

Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa batun mashigar ruwan Hormuz, takunkumin tattalin arziki da kuma shirin nukiliyar Iran na ci gaba da kasancewa cikin manyan batutuwan da ke gaban bangarorin biyu.

Address

Kano Nigeria Arewa
Kano
0157003

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Arewa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share