Hamshakiya

Hamshakiya Labarai cikin harshen Hausa da dumi-dumin su

12/08/2026
12/08/2026

Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingìr ya ce ya yi tsammànin zai sha s**a lokacin da ya yi wasu kalamai gàme da takarar Muslim-Muslim.

Jingir ya kuma ce ba ya da na sanin matsayarsa.

11/08/2026

Learn colors the fun way with "Color Farm" — a super catchy sing-al...

11/08/2026

Ma'aikatan kwana-kwana sun kwashe tsawon lokaci suna ƙoƙarin kashe wata gagarumar gobara da ta tashi a matatar mai ta Zawiya a ƙasar Libya, bayan an kai jerin hare-hare da jirage maras matuƙa a matatar da ma wasu matatun man fetur da ke birnin.
Babban Kamfanin Mai na Libya ya ce wani hari da aka kai da jìrgi maras matuƙi ya faɗa kusa da babban tànkin mai da bututan mai na Kamfanin Mai na Zawiya, kuma wànnan shi ne hari na uku da aka kai a cikin kwana biyu.
Kamfanin man ya yi gargaɗi cewa zai ayyana dokar ta-ɓaci tare da dàkatar da haƙar mai baki ɗaya idan ba a daina kai hare-haren ba, ko da yake babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai hare-haren.

Auren gata a Kano: Ƙalubalen da ake fuskanta wajen tantance masoyan gaskiya da na bogiMurnar aure ta mamaye birnin Kano ...
11/08/2026

Auren gata a Kano: Ƙalubalen da ake fuskanta wajen tantance masoyan gaskiya da na bogi

Murnar aure ta mamaye birnin Kano da ke arewacin Najeriya cikin makon da ya gabata, yayin da aka ɗaura wa mutum 3,000 aure a wani gagarumin shirin auren gata.

Tsawon kwanaki, titunan birnin sun cika da hayaniyar shagulgula, inda amare da danginsu ke shirya kayayyakin aure tare da halartar wasu tarurruka da shirye-shirye da aka tanada musu.

A ranar Juma'a, amare sanye da jajayen hijabai, yayin da angwaye ke cikin fararen riguna da jajayen huluna, s**a nufi fadar Sarkin Kano domin bàbban bikin da a cikinsa aka ɗaura auren nasu a hukumance.

A ranar Asabar ne aka kammala shagulgulan auren da wata liyafa da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shirya, inda ya yi wa sabbìn ma'auratan fatan alheri da addu'ar samun zaman lafiya da albarka a rayuwarsu ta aure.

An yanke wa tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad hukuncin kisaWata kotu a Syria ta yanke wa hambararren shugaban kasar ...
11/08/2026

An yanke wa tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad hukuncin kisa

Wata kotu a Syria ta yanke wa hambararren shugaban kasar Bashar al-Assad hukuncin kisa ba tare da ya bayyana a gaban kotu ba, bayan ta same shi da laifin aikata laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama a lokacin yaƙin basasar ƙasar.

Wannan shi ne hukunci na farko da aka yanke wa Assad, wanda ya tsere daga Damascus zuwa Moscow tare da iyalansa bayan an hamɓarar da gwamnatinsa a watan Disamban 2024, wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkin da iyalansa s**a yi tsawon shekaru biyar.

An kuma yanke wa ɗan'uwan Assad wanda kuma babban jagoran tabbatar da tsaro ne a lardin Deraa da ke kudancin ƙasar ta Siriya, Atef Najib hukuncin kisa. An gurfanar da shi a gaban kotu kuma ya bayyana sanye da kayan gidan yari mai layi-layi a cikin keji a kotun yayin da alkalin kotun ke karanta hukuncin.

Ana ganin Deraa a matsayin wurin da aka fara bore kan mulkin Assad.

Da gaske ne dora ƙanƙara kan ƴaƴan maraina na inganta maniyyi?Kowace safiya idan Simon ya tashi daga barci, yakan tafi w...
26/06/2026

Da gaske ne dora ƙanƙara kan ƴaƴan maraina na inganta maniyyi?

Kowace safiya idan Simon ya tashi daga barci, yakan tafi wani ɗakin da yake kunna tiriri domin ya tara zufa (sauna).

Simon, mai shekara 28 kan yi tattaki domin inganta ƙwayoyin haihuwarsa
Bayani kan maƙala
Marubuci,Jacqui Wakefield
Sanya sunan wanda ya rubuta labari,Global Health reporter
An wallafa
Sa'o'i 4 da s**a wuce
Lokacin karatu: Minti 6
Kowace safiya idan Simon ya tashi daga barci, ya kan tafi wani ɗakin da yake kunna tiriri domin ya tara zufa (sauna).

Zufar kan taimaka masa wajen fitar da abubuwan da jikinsa ba ya buƙata, wanda ya ce hakan na taimaka masa wajen inganta maniyyinsa - amma kuma yana buƙatar kariya daga zafin da ke sanya shi zufar.

"Nakan yi amfani da pakitin ƙanƙara, da ake kira Chill Nuts, domin ɗora shi a kan ƴaƴan maraina na, don kiyaye yawan maniyyina," kamar yadda ya shaida BBC.

Wannan ita ce hanya da yake bi domin tattalin maniyyinsa, duk kuwa da rashin hujjar hakan a kimiyyance.

ƳAN BINDIGA SUN SHIGA UKU: Bauchi Ta Yaye Rukunin Farko Na Masu Tsaron Daji Domin Karfafa TsaroGwamnatin Jihar Bauchi ta...
25/06/2026

ƳAN BINDIGA SUN SHIGA UKU: Bauchi Ta Yaye Rukunin Farko Na Masu Tsaron Daji Domin Karfafa Tsaro

Gwamnatin Jihar Bauchi ta yaye rukunin farko na jami’an Forest Guards domin ƙarfafa tsaro a yankunan karkara da dàzuka.

Hukumomi sun ce jami’an za su yi aiki tare da sàuran hukumomin tsaro wajen tattara bayanan sirri, sintiri da kuma dàkile ayyukan ’yan bìndiga da masu garkuwa da mutane.

Ana sa ran sabon shirin zai taimaka wajen ƙara tsaro da zaman lafiya a sassan jihar.

👉 Kuyi Following Hamshakiya domin samun sabbin labarai da dumi-dumi a kodayaushe.

"Ban Yi Maka Ƙage Ko Ɓata Suna Ba, Saƙon Allah Kawai Na Isar" — Primate Ayodele Ya Kalubalanci Kwankwaso Kan Barazanar Ƙ...
25/06/2026

"Ban Yi Maka Ƙage Ko Ɓata Suna Ba, Saƙon Allah Kawai Na Isar" — Primate Ayodele Ya Kalubalanci Kwankwaso Kan Barazanar Ƙarar Naira Biliyan 10

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church da ke Legas, Primate Elijah Ayodele, ya yi martani ga barazanar ƙarar da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi masa, inda ya jaddada cewa bai ɓata masa suna ba.

Ayodele ya ce kalaman da ya yi game da Kwankwaso ba ƙage ba ne, kuma ba wani yunƙuri ba ne na bata masa suna, sai dai hasashen da ya ce ya samu ta hanyar wahayi daga Allah. Ya bayyana cewa aikinsa a matsayin malamin addini shi ne isar da saƙonnin da ya yi imanin sun zo daga Ubangiji, ba tare da la'akari da wanda abin ya shafa ba.

Martanin na zuwa ne bàyan Kwankwaso ya yi barazanar kai Ayodele kotu tare da neman diyyar Naira biliyan 10, yana mai zargin cewa wasu kalaman malamin sun ɓata màsa suna da mutuncinsa a idon jama'a.

Takaddamar ta fara ɗaukar sabon salo yayin da ake sa ran ko dai bangarorin za su sàsanta ko kuma shari'ar za ta koma kotu domin yanke hukunci.

Address

Kano
730010

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00

Telephone

+2347066102221

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hamshakiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hamshakiya:

Shortcuts

Share