Fatima Inuwa

Fatima Inuwa Allhammadulillah ala kulla hallin

11/10/2025
Bismillah
10/10/2025

Bismillah

YANZU-YANZU: Bello Turji ya ƙuduri niyyar ajiye makamai kuma ya saki mutane 32 - Asadus-Sunnah Kasurgumin jagoran ƴan ta...
05/08/2025

YANZU-YANZU: Bello Turji ya ƙuduri niyyar ajiye makamai kuma ya saki mutane 32 - Asadus-Sunnah

Kasurgumin jagoran ƴan ta’adda a jihar Zamfara, Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su tare da amincewa da ya dena kaiwa manoma hari, bayan ganawa da malaman addinin Musulunci a dajin Fakai, karamar hukumar Shinkafi.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Malamin addini Musulunci, Musa Yusuf, wanda ya fi shahara da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan a wani taron addini a Kaduna, inda ya ce al’ummar Shinkafi ne s**a bukaci a shiga tsakani domin su samu damar komawa gonakinsu.

A cewar Yusuf, ganawar ta gudana sau uku a watan Yuli, kuma Turji da wasu fitattun mayaka kamar Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya, ciki har da ajiye makamai da barin manoma su koma gonaki ba tare da fargaba ba.

Yusuf ya ce wadanda aka sako sun hada da mata da yara, kuma sun shafe kusan watanni hudu a hannun Turji.

Wasu daga cikinsu sun haifi yara a daji, yayin da daya daga cikinsu ta kamu da cizon maciji.

Ya ce tun bayan yarjejeniyar, zaman lafiya ya fara dawowa a yankin Shinkafi, inda manoma ke ci gaba da aikin gona cikin kwanciyar hankali.

Malamin ya gargadi wasu malamai da ke s**ar Turji a kafafen sada zumunta da su daina, yana mai cewa hakan na iya tayar da zaune tsaye.

Ya yabawa Shugaba Bola Tinubu, Nuhu Ribadu, Gwamna Dauda Lawal da Sanata Shehu Buba saboda goyon bayan hanyar zaman lafiya wajen magance matsalar tsaro a Zamfara.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da nadin tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat a ma...
05/08/2025

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da nadin tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Lantarki ta Nijeriya NERC.

A tafawa Nafisa 👏 👏 👏 Matashiya daga Yobe ta doke ƙasashe 69 ta lashe gasar Ingilishi ta duniyaNafisa Abdullah Aminu, ya...
05/08/2025

A tafawa Nafisa 👏 👏 👏

Matashiya daga Yobe ta doke ƙasashe 69 ta lashe gasar Ingilishi ta duniya

Nafisa Abdullah Aminu, yarinya mai shekaru 17 daga Jihar Yobe, Najeriya, ta zama ta ɗaya a duniya wajen ƙwarewar harshe na Ingilishi a gasar TeenEagle Global Finals ta 2025 da aka gudanar a birnin London, ƙasar Birtaniya.

Nafisa, wadda ta wakilci Najeriya daga makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC) da ke Yobe, ta doke sama da ɗalibai 20,000 daga ƙasashe 69 ciki har da waɗanda harshen su na asali Ingilishi shi ne.

Wasan Al'adu: Kabilar Fulani tazamo Gwarzon shekara a Wani wasan Al'adu da ya gudana a makarantar jeka kadawo DSS BEJI.K...
05/08/2025

Wasan Al'adu: Kabilar Fulani tazamo Gwarzon shekara a Wani wasan Al'adu da ya gudana a makarantar jeka kadawo DSS BEJI.

Kabilar Fulanin tazamo na daya biyo bayan wasannin Al'adu da ya gudana a harabar Makarantar, kabilun da s**a gabatar da nasu sun hada da Hausa, Zuru, Yorba, Fulani, Igbo, Gwari, Nupe dadi sauran kabilu.

Idan za'a iya tunawa Kabilar Fulanin su s**a zamo zakara a Shekarar da ta gabata 2024 a makarantar dake Beji Karamar hukumar Bosso Jahar Naija.

A Tarihin Nijeriya Ba A Taba Yin Adalin Shugaban Kasa Irin Marigayi Muhammadu Buhari Ba, Cewar Ruhailat JB
05/08/2025

A Tarihin Nijeriya Ba A Taba Yin Adalin Shugaban Kasa Irin Marigayi Muhammadu Buhari Ba, Cewar Ruhailat JB

BABU GWAMNATIN DA ZATA IYA WARWARE MATSALOLIN 'YAN NIJERIYA CIKIN SHEKARU 20-neyson wike
05/08/2025

BABU GWAMNATIN DA ZATA IYA WARWARE MATSALOLIN 'YAN NIJERIYA CIKIN SHEKARU 20-neyson wike

Wasu sabbin hotunan Hadiza Gabon, waɗanda su ke nuni da cewa da yanayin surar jikinta ta canja sun sake haifar da ceceku...
04/08/2025

Wasu sabbin hotunan Hadiza Gabon, waɗanda su ke nuni da cewa da yanayin surar jikinta ta canja sun sake haifar da cecekuce a kafafen sadarwa.

Macen da bata taɓa saduwa da namiji ba kawai ya kamata a riƙa baiwa sadaki - Omokri Tsohon mai bai wa shugaban kasa shaw...
04/08/2025

Macen da bata taɓa saduwa da namiji ba kawai ya kamata a riƙa baiwa sadaki - Omokri

Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Reno Omokri, ya ce ya kamata a daina biyan sadaki ga matar da ta taɓa saduwa da namiji, yana mai bayyana cewa hakan ya zama wata hanya ta tilastawa mutane biyan kudi ba bisa ka’ida ba.

A wani dogon sakonsa da ya wallafa a shafinsa na X, Omokri ya bayyana cewa a al’adun Afirka da Yahudawa, sadaki na nufin kudin da namiji ke biya wa iyayen budurwa, kuma hakan na da tushe a cikin Littafi Mai Tsarki, musamman a Fitowa 22:17.

Ya bayyana bambanci tsakanin "kayan Aure" da "sadaki", inda ya ce kayan daki dukiyar iyaye ne ke bai wa ’yarsu a ranar aurenta, amma sadaki na nufin kudi ko dukiya da ango ke biya don auren budurwa.

Omokri ya soki yadda wasu kabilun Afirka ke bukatar sadaki mai yawa ga mata da ba budurwa ba, yana mai cewa hakan ya zama cin zarafi da kuskuren al’ada.

Ya kuma ce a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "amarya" tana nufin budurwa ne kawai, yana ba da misalai da dama don kare wannan matsayi.

A karshe, Omokri ya ce aure irin na fararen fata ba al’adar Afirka ba ce kuma ba addinin Kirista ba ne, yana mai bukatar mutane su fahimci asalin al’adunsu domin hana rugujewar tarbiyya.

Address

Kano

Telephone

+2349068641665

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fatima Inuwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Fatima Inuwa:

Share