Dan Bello Fans.

Dan Bello

Fans. Labarai • Faɗakarwa • Kishin Ƙasa

Ya Lalata Master Plan din Abuja, Ruwa yayi Ambaliya shi kuma gashi Nan Saman Ruwa Yana Sharholiyar shi a wata kasar.. .....
17/08/2026

Ya Lalata Master Plan din Abuja, Ruwa yayi Ambaliya shi kuma gashi Nan Saman Ruwa Yana Sharholiyar shi a wata kasar.. .. Kodai Shima Muce......?

NAN FA TSAKIYAR ABUJA NE YA CIKA DA RUWA, BISA DALILIN ZALUNCIN WIKE!!! :Ambaliyar Ruwa Ce akayi Jiya A Garin Abuja Kama...
17/08/2026

NAN FA TSAKIYAR ABUJA NE YA CIKA DA RUWA, BISA DALILIN ZALUNCIN WIKE!!! :

Ambaliyar Ruwa Ce akayi Jiya A Garin Abuja Kamar yadda kuke Gani Motoci sunyi Tsamo-Tsamo a Ciki, saboda yadda ruwan ya shafe koina. A baya-bayan Nan, tunda Wike ya zama Ministan Abuja an taƙaita hanyoyin ruwa ta hanyar rage musu fadi da wadatar da ruwa mai yawa zai wuce yadda ya kamata, da kuma yanyanka wurare/filaye Yana ba wanda yake so, Kamar Yadda kwanakin baya yaso ya kwace filin Soja mai Gidan Yerima da yayi tsayin daka ya hana a kwace filin. kuma sakamakon haka ambaliyar ruwa ta fara faruwa a Cikin garin.

Ya kamata a sake duba wasu daga cikin izinin da aka bayar na yin gine-gine a kan wuraren koren birnin (green areas), sannan idan ya zama dole, a bayar da umarnin rushe duk wani gini da ke toshe hanyar ruwan da Allah Ya halitta.

Dole ne a kare magudanan ruwa da hanyoyin ruwan Abuja kafin lamarin ya ƙara taɓarɓarewa.

WIKE YANA MULKI YADDA YAGA DAMA A ABUJA, WANDA YAKE SHINE BABBAN BIRNIN KASAR. KUMA HAKAN BABBAR BARAZANA CE GA NAJERIYA.

MUSA MAI SANA'A YASHA DAKYAR A JIHAR KATSINA : Sauran kadan Wasu Matasa a Jihar ta Katsina Su Lakadawa dan wasan na Haus...
16/08/2026

MUSA MAI SANA'A YASHA DAKYAR A JIHAR KATSINA :

Sauran kadan Wasu Matasa a Jihar ta Katsina Su Lakadawa dan wasan na Hausa Musa Mai Sana’a Duka. Yaje daidai kofar Shiga garin ne mai Suna "Welcome to Katsina" yahau saman ta da niyyar yin Bidiyo na tallar Bola Tinubu da Bada Saqon Nuhu Ribadu kamar yadda ya saba, Aikuwa Matasan s**a gargade shi daya sauko ku Su sauko dashi ba Zasu yarda ayi masu Tallar Tinubu ba a wuri.

Daga karshe dai sun samu damar shi yin Abunda yake so din, inda matasan s**a kusa lakada Mashi Dukan tsiya har saida jami’an tsaro s**a tseratar dashi.

Ance ma acan yabar hular sa wajen gudu.

Hakika Tallar Tinubu da Sauran mutanen sa zata yi Wahala a Bana!!!

16/08/2026

ALLAHU AKBAR : Kaji Aikin Addu'ah 👂🏽

Gomnonin APC Ne S**a je Osun Don Su Murde Zaben Gomnan. Amma ga Alama hakan bazai Yiwu ba In Sha Allah.Allah Ya Karya AP...
15/08/2026

Gomnonin APC Ne S**a je Osun Don Su Murde Zaben Gomnan. Amma ga Alama hakan bazai Yiwu ba In Sha Allah.

Allah Ya Karya APC!!!..

Adeleke Is Winning the Osun State Governorship Election According to His Nephew  ..This is the start of APC Failure by G...
15/08/2026

Adeleke Is Winning the Osun State Governorship Election According to His Nephew ..

This is the start of APC Failure by God's Grace!!!..

NASARA DAGA ALLAH : Sojoji a Zamfara sun hallak@ wasu ’yan ta’add@, kuma s**a cafke mai yi wa ’yan bindig@r safarar maka...
15/08/2026

NASARA DAGA ALLAH : Sojoji a Zamfara sun hallak@ wasu ’yan ta’add@, kuma s**a cafke mai yi wa ’yan bindig@r safarar makam@i tare da ƙwace abubuwan fashewa 180 da bindig0gi haɗe da harsasai....

Allah Ya Cigaba da tona Musu Asiri.

Tun Wajen karfe 5 na yammacin wannan rana ta Juma’a Wasu da ake zargin barayi ne s**a kai hari garin har zuwa lokaci da ...
14/08/2026

Tun Wajen karfe 5 na yammacin wannan rana ta Juma’a Wasu da ake zargin barayi ne s**a kai hari garin har zuwa lokaci da ake tattaunawa da Wani Mazaunin garin har zuwa wajan karfe 9 na dare basu bar yankin ba.

Yace da idonsa ya ga mashinan batagarin sama da 50, kuma sun raunata mutane da dama, inda ya bukaci mahukunta dasu taimaka musu.

Shuwagabannin Jihar kano ya Kamata a miqe ayi maganain Abun Nan tun kafin yayi karfi. Koina da haka suke farawa.

Allah Ya Mana Maganin Su.

AN BIYA SHI DOMIN YA GANO MASU TSATTSAURAN RA'AYI A MUSULMAI, AMMA DAGA KARSHE MUSULMI S**A KAI KARAR SHI A MATSAYIN MAI...
14/08/2026

AN BIYA SHI DOMIN YA GANO MASU TSATTSAURAN RA'AYI A MUSULMAI, AMMA DAGA KARSHE MUSULMI S**A KAI KARAR SHI A MATSAYIN MAI TSATTSAURAN RA'AYI A LOKACIN DA YA FARA MUSU MAGANGANUN JIH@DI DA TAYAR DA HANKALI NA MASU TSATTSAURAN RA'AYI :

A shekarar 2006, shekaru biyar bayan harin 11 ga Satumba (9/11), FBI ta bukaci wani mutum da zai iya shiga cikin al’ummomin Musulmi a Orange County, California, ba tare da tayar da musu da hankali ba. Sai s**a same shi a wani gidan motsa jiki.

Craig Monteilh malamin motsa jiki ne, kuma yana da tarihin aikata zamba, lokacin da FBI ta dauke shi aiki a matsayin mai ba da bayanan sirri. Ya fara halartar Islamic Center of Irvine, daya daga cikin manyan masallatai a Kudancin California, sannan ya bayyana Musuluntarsa a gaban daruruwan masu ibada a cikin watan Ramadan. Ya sanya wa kansa suna Farouk.

Monteilh ya shafe sama da shekara guda yana gina Mu'amula da al’ummar Musulmi. Mutane suna gayyatar sa gidajensu don cin abinci da yin sallah. Ya shiga kungiyoyin karatun addini, ya halarci sallolin asuba da dama, kuma ya zama mutum da aka saba gani kuma aka karbe shi a cikin al’ummar.

Duk tsawon wannan lokacin, a boye yake nadar kusan dukkan abubuwan da ke faruwa. Yana dauke da wata kyamara da aka boye a cikin maballin rigarsa. Ya kuma bar wasu makullan da ke dauke da na’urar daukar sauti a cikin ofishin masallaci, a wajen da ake ajiye kayayyakin da aka tsinta, domin ta rika daukar hirarrakin sirri tsakanin limamai da masu ibada, wadanda suke zaton suna magana ne cikin sirri.

FBI ta biya Monteilh dala 177,000 saboda aikin da yake yi, tare da wasu karin kudade da s**a danganta da yawan salloli da tarukan da ya halarta. A cewar shaidar da ya bayar daga baya a kotu, aikin da aka ba shi shi ne taimakawa wajen gano mutanen da ake zargin suna da ra’ayin tsattsauran ra’ayi a cikin masallacin.
Sai dai wani abu daban ya faru. Monteilh ya fara magana game da jih@di da tashin hankali ta hanyoyin da s**a fara tayar wa mutanen da ke kusa da shi hankali. Wasu daga cikin masu ibadar sun yi kokarin gyara masa fahimta, suna amfani da koyarwar Musulunci game da zaman lafiya.

Lokacin da hakan bai yi tasiri ba, al’ummar masallacin s**a fara matukar damuwa har s**a kai rahotonsa kai tsaye ga FBI (A cikin rashin Sanin ashe sune S**a tura sa), suna gargadin cewa watakila ya zama mutum mai tsattsauran ra’ayi kuma mai hatsari.

Daga karshe, Islamic Center of Irvine ta nemi kotu ta bayar da umarnin hana shi zuwa harabar masallacin, kuma aka amince da bukatar. Sai bayan kusan shekaru biyu ne al’ummar s**a gano gaskiyar lamarin: mutumin da s**a kai wa rahoto a matsayin wanda suke zargin ya zama mai tsattsauran ra’ayi, a zahiri shi ne wakilin gwamnatin Amurka da aka turo domin yi musu leken asiri.

Lamarin ya zama tushen wata babbar kara da aka shigar kan FBI, wadda daga baya ta kai har zuwa Kotun Koli ta Amurka, kan tambayoyi da s**a shafi leken asirin addini da kuma hakkokin jama’a.

SUNQI SU GANE MUSULUNCI ADDININ ZAMAN LAFIYA NE. ALLAH YA KARA KARE ADDININ MU.

Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un : Wannan Bawan Allah Mai Suna Malam Auwal, Mazaunin Hayin Babban Saura Police Quarter...
13/08/2026

Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un : Wannan Bawan Allah Mai Suna Malam Auwal, Mazaunin Hayin Babban Saura Police Quarters ne da ke Kaduna, da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane s**a kashe shi bayan iyalansa sun biya kuɗin fansa har naira miliyan 12 (₦12m).

An yi garkuwa da shi ne daga gidansa, kuma duk da an biya kuɗin fansan, ana zargin ’yan bindigar sun kashe shi tare da cewa sun binne gawarsa. Har yanzu iyalansa ba su san takamaiman lokacin da aka kashe shi ba. Ɗansa, wanda ya kai kuɗin fansan, har yanzu yana hannun ’yan bindigar duk da alkawarin da s**a yi na cewa za su sake shi.

A Jiya Laraba 12 ga Agusta, 2026, an gudanar da Sallar Jana’izar Ga’ib (Salatul Gha’ib) ga Malam Auwal a Murtala Square da ke Kaduna, inda ’yan uwa da saun Al’ummar Musulmi s**a taru domin yi masa addu’a.

ALLAH YA JIKAN SHI DA RAHAMA YASA YA HUTA AMIN

Address

Rijiyar Zaki Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Bello Fans. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share