06/06/2024
SUNAYEN DAWAKI
Bisa ga sarauta akwai jerin Dawaki da martabarsu.
1. Kili Mago. Doki ne mai farin gashi baki daya, babu ko sofane. Kili Mago yana da idanu masu bakar fata haka kwadar ma baka ce. Shine na farko a daraja.
2. Kili:- Shima kamarsa daya ce da Kili Mago saidai yana da idanu masu jar fata haka kwarar ma ja ce. Shine na biyu a daraja.
3. Akawali: Doki ne baki wuluk. Wanda ya samu fari biyar watau goshi, da kafafu hudu (kofato zuwa gwiwa) ya fi duk sauran akawali daraja. A jerin darajar Dawaki, akawali yana matsayi na ukku.
4. DANDA:- Duk doki mai fari biyar ko wacce kalar gashi ne, ana kiransa danda.
5. DUNHU:- Doki ne wanda ba shi da fari ko daya cikin fari biyar.
6. KILI KANYA:- Doki ne mai farin gashi amma ya samu wake-wake na bakin gashi.
7. FURDU:- Doki ne mai farin gashi amma ya samu feshin bakin gashi tamkar furfura a kan dan Adam.
8. BIDI:- Doki ne mai bakin gashi amma ya samu feshin farin gashi tamkar furfura a kan dan Adam.
9. GUNYA:- Doki ne mai kalar gwal (muna ce masa kwalin bansin) yana kuma da bakar isgar wuya da bakar isgar jela (bindi, wutsiya, dss, afwan ga ma'ana).
10. ALKAS:- Doki ne zubinsu daya da gunya saidai isgar wuya da ta bindi duk gwal ne. Watau kalar gashin jikin ne.
11. TANTABARA:- Duk doki, ko wacce kala ne, mai tambarin fari a ciki, kafada, hakarkari, gadon baya, ko cinyar baya. Amma ban san sunan farin doki mai tambarin baki ba.
12. JURI: Doki ne mai gashi da kalar shuri amma akwai feshin wata kalar gashin (ja, Baki, ko fari) tamkar feshin furfura.
13. SHEDI: Doki ne mai gashi ja. Muna masa kirari, Shedi dolin Fulani.
14. BIKILI: Doki ne mai kalar shuri, kasa-kasa, yana sheki. Kuma shi ne na karshe (kututu) a daraja ga sarakai. Dalili, camfi ne, domin a tarihin Sarakunan Hausa, duk basaraken da aka sauke ana dora shi kan bikili ya san inda ya nufa. Dalili ke nan aka tsani bikili.
Bakin abin da ya saukaka kenan game da sunayen Dawaki da siffofinsu ga galibin wadanda ake ma'amulla da su game da hawa. Suna