KalKal Hausa

KalKal Hausa KalKal Hausa shafi ne na yada sahihan labarai cikin harshen Hausa.

Muna kawo muku labarau, cikin sauri, sahihanci da cikakken bayani.
- Siyasa
- Ilimi
- Addini
- Tattalin Arziki
- Labaran Arewa
Ku biyo mu domin samun ingantattun labarai a kowane lokaci.

LABARAI Da Dumi Dumi: 🚨Rahotanni daga Germany na cewa ɗan wasan gefe na Paris Saint-Germain yana jan hankalin Bayern Mun...
08/05/2026

LABARAI Da Dumi Dumi: 🚨

Rahotanni daga Germany na cewa ɗan wasan gefe na Paris Saint-Germain yana jan hankalin Bayern Munich sosai, yayin da FC Barcelona ma ake cewa na cikin kungiyoyin da suke bibiyarsa a kusa.

Rahotanni ya kara da cewa kungiyoyi irin su Arsenal F.C. da Liverpool F.C. suma ke nuna sha’awa gare shi.
Kalkalhausa

LABARAI Da Dumi Dumi:Wasu daga cikin ‘yan wasan Real Madrid sun kasance suna kiran Álvaro Arbeloa da “CONE” (wato kamar ...
08/05/2026

LABARAI Da Dumi Dumi:
Wasu daga cikin ‘yan wasan Real Madrid sun kasance suna kiran Álvaro Arbeloa da “CONE” (wato kamar mutum mara tasiri ko wanda ba ya da wani amfani) a tsakaninsu yayin da suke zaune a benci a wasanni da dama.

An ce ya gano hakan, kuma saboda haka ya yanke shawarar daina saka su a wasa.
Hausa

LABARAI DA DUMI-DUMI 🚨Real Madrid sun yanke shawarar cewa ba za su kori Álvaro Arbeloa ba.Suna da cikakken imani da tsar...
17/04/2026

LABARAI DA DUMI-DUMI 🚨

Real Madrid sun yanke shawarar cewa ba za su kori Álvaro Arbeloa ba.

Suna da cikakken imani da tsarin aikin sa, kuma suna shirin ci gaba da rike shi a kakar wasa mai zuwa

🚨 LABARAI DA DUMI-DUMI: BERNARDO SILVA ZAI BAR MANCHESTER CITY 🔵⚽Kungiyar Manchester City ta tabbatar da cewa tauraron d...
06/04/2026

🚨 LABARAI DA DUMI-DUMI: BERNARDO SILVA ZAI BAR MANCHESTER CITY 🔵⚽

Kungiyar Manchester City ta tabbatar da cewa tauraron dan tsakiyarta, Bernardo Silva, zai bar kungiyar a matsayin ɗan wasa mai ‘yanci (free agent) a watan Yuni mai zuwa.

Bayan da rahotanni s**a bayyana tun a makon da ya gabata.

Bernardo ya sanar da kulob din shirinsa na neman sabuwar kungiya kafin fara gasar Kofin Duniya.

A tsawon zamansa a Manchester City, Bernardo Silva ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da kungiyar ta samu, inda ya lashe:

🏆 Champions League – sau 1
🏆 Premier League – sau 6
🏆 League Cup – sau 4
🏆 FA Cup – sau 2

Tarihi mai girma, gudunmawa mai yawa, da kuma tunawa mai dadi daga magoya baya — yanzu sabon babi ne zai fara a rayuwar Bernardo Silva.

Wace kungiya kuke ganin zai koma? 👀🔥

Abdullahi Saidu

Iran na da gurbin fafatawa a gasar kofin duniya wadda kasashe guda 48 zasu jagoranta.Har yanzu babu tabbacin ficewar Ira...
12/03/2026

Iran na da gurbin fafatawa a gasar kofin duniya wadda kasashe guda 48 zasu jagoranta.

Har yanzu babu tabbacin ficewar Iran din daga kofin duniya amma a kalkal hausa ta jiyo shugaban hukumar kwallon kafar Iran din Mehdi Taj na cewa babu wani mutun mai tunani da zai tura tawagar sa Amurika saboda gujewa irin abin da ya faru a Australia.

Ministan Wasannin Iran din Ahmad Donyamali yace a ranar laraba Iran ba zata fafata a wasannin da za a fafata a Amurika ba saboda baman-baman da Amurika din ke jefawa kasar su.

Za a cigaba da wasan zagayen yan sha shida (Round of 16) a gasar Zakarun Nahiyar Turai.A inda za a fafata wasa guda 4 wa...
10/03/2026

Za a cigaba da wasan zagayen yan sha shida (Round of 16) a gasar Zakarun Nahiyar Turai.

A inda za a fafata wasa guda 4 wanda ya hada
1. Galatasray da Liverpool
2. Atalanta da Bayer Munich
3. Atletico Madrid da Tottenham
4. Newcastle da Barcelona

Wasannin dai za a buga su ne gida da waje, inda Liverpool za ta kay ziyara kasar Turkey, Bayern Munich kuwa birnin Atalanta za ta je, Ateletico Madrid kuma bakuncin Tottenham zata karba a kasar sifaniya, Barcelona kuwa tattaki za ta yi har kasar Ingila domin ta kece raini tsakanin ta da Newcastke.

A mako daya Boko Haram da ISWAP sun kashewa Najeria dakaru masu yawa cikin har da manyan kwamandojin ta guda 3.ISAWP dai...
10/03/2026

A mako daya Boko Haram da ISWAP sun kashewa Najeria dakaru masu yawa cikin har da manyan kwamandojin ta guda 3.

ISAWP dai ta dauki alhakin kai hare hare kan sansanonin sojin Najeriya a jihar Borno, hare haren dai sun rutsa da fararen hula.

Sanarwar ta zo ne ta hanyar Kamfanin dillancin labarai na Amaq.

Dubban Iraniyawa ne s**a taru domin jaddada muba`ya`ar su ga sabon Shugaban Addini na Iran Mojtaba Khamenei.Mojtaba wand...
09/03/2026

Dubban Iraniyawa ne s**a taru domin jaddada muba`ya`ar su ga sabon Shugaban Addini na Iran Mojtaba Khamenei.

Mojtaba wanda da ne ga tsohon shugaban Addini na Iran wanda aka kashe ya gaji mahaifin na sa ne bayan da hukumar koli ta addini ta zabe shi.

Shugabannin kasashe nata taya sa murna ciki da Shugaba Putin na Russia.

Matatar Man feturn ta Dangote ta kara farshin Man Fetir zuwa N1,175
09/03/2026

Matatar Man feturn ta Dangote ta kara farshin Man Fetir zuwa N1,175

A yau 9/3/2026 a fadar gwamnatin Jihar Zamfar aka sauke tutar Jam`iyyar PDP tare da fitar da ita daga fadar.Daga baya Gw...
09/03/2026

A yau 9/3/2026 a fadar gwamnatin Jihar Zamfar aka sauke tutar Jam`iyyar PDP tare da fitar da ita daga fadar.

Daga baya Gwamnan ya sanar da fitar tashi a shafin sa na X (Twitter a baya).

A kwanakin nan dai gwamnoni na ta canza sheka kafin zuwan babban zaben 2027.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KalKal Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share