17/08/2026
Gwamnatin Kano Ta HaÉ—a Kai da Makarantun Gaba da Sakandare Wajen Shuka Bishiyoyi.
Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon shiri na haɗa gwiwa da manyan makarantun gaba da sakandare domin faɗaɗa dashen bishiyoyi da ƙarfafa kiyaye muhalli a faɗin jihar.
Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya ƙaddamar da shirin a Kwalejin Musulunci da Ilimin Shari’a ta Mallam Aminu Kano, wato Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies.
Mahukuntan makarantar da wakilan ɗalibai sun nuna goyon bayansu ga shirin, tare da alƙawarin kula da bishiyoyin da aka dasa da kuma kare su daga lalacewa.
A ƙarƙashin shirin, kowace bishiya da za a dasa za ta samu lambar tantancewa ta musamman, yayin da za a ware wasu jami’an makarantu domin kula da bishiyoyin, bibiyar yadda suke girma da kuma tabbatar da cewa an kare su.
Kwamishinan ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na babban shirin dashen bishiyoyi da gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya ce gwamnatin ta aiwatar da shirye-shiryen dashen bishiyoyi miliyan ɗaya da kuma miliyan uku, yayin da yanzu take faɗaɗa ƙoƙarin zuwa babban shirin dashen bishiyoyi miliyan goma a wannan shekara.
Dakta Dahiru ya bayyana dashen bishiyoyi a matsayin jari na dogon lokaci da ke da muhimmiyar gudummawa wajen kare muhalli. Ya ce bishiyoyi na taimakawa wajen tsaftace iska, rage zafin yanayi, yaƙi da zaizayar ƙasa, samar da inuwa da kuma kare halittu.
Ya kuma ƙarfafa gwiwar ɗalibai da su zama jakadun kare muhalli ta hanyar shiga ayyukan dashen bishiyoyi, kula da wuraren renon tsirrai da kuma kare bishiyoyin da aka dasa.
Makarantar Ta Nemi Tallafin Gwamnati
A yayin taron, mahukuntan makarantar sun gabatar da wasu buƙatu ga kwamishinan, ciki har da samar da ingantaccen ruwan sha.
Sun bayyana cewa samun isasshen ruwa na da matuƙar muhimmanci wajen tsafta, kiwon lafiya da kuma ayyukan lambu da ake gudanarwa a makarantar, musamman ganin yadda ɗalibai ke samun horo na aikace-aikacen noma.
Makarantar ta kuma nemi taimakon gwamnati wajen samar da katafaren É—akin noman zamani, wato greenhouse, domin inganta koyar da aikin gona, gudanar da bincike da kuma noman amfanin gona bisa hanyoyin da s**a dace da sauyin yanayi.
Haka kuma, an nemi tallafin magungunan kashe ƙwari, kayan yaƙi da cututtukan amfanin gona da kuma shawarwarin ƙwararru domin magance matsalolin ƙwari da cututtuka da ke lalata amfanin gonar makarantar.
Gwamnati Ta Jaddada Ƙudirin Inganta Ruwa da Muhalli
Da yake mayar da martani, Kwamishinan ya sake tabbatar da ƙudirin ma’aikatar na tallafa wa cibiyoyin ilimi da kuma magance ƙalubalen da s**a shafi muhalli da albarkatun ruwa a jihar.
Ya amince da cewa akwai ƙalubale wajen samar da ruwa da ababen more rayuwa, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da gyara da inganta manyan masana’antun sarrafa ruwa da tsarin samar da ruwa a sassa daban-daban na jihar.
Ya bayyana cewa ana sa ran ruwa zai fara samun ingantaccen yanayi a cikin birnin Kano cikin watanni biyu masu zuwa.
Domin magance matsalar ruwa a makarantar cikin gaggawa, Kwamishinan ya bayar da umarnin a hako mata rijiyar burtsatse domin samar da ruwa.
An kammala taron da dashen bishiyoyi, inda ɗalibai da shugabannin makarantar s**a shiga aikin tare da Kwamishinan, a matsayin wata alama ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da cibiyoyin ilimi wajen kare muhalli.