23/09/2026
NAMIJIN ZUMA BA YA TARA ABINCI KO YIN ZUMA? 🤔
Wasu mutane idan s**a ga drone bee sai su ce:
“Wannan ai malalaci ne! 😅 Baya tara zuma, ba ya ciyar da colony, sai dai ya zauna yana jiran abinci!”
Amma abin mamaki shine: ba malalaci bane!
Allah ya halicce shi da wani aiki na musamman.
Babban aikin drone bee shine haihuwa.
Drones maza ne, kuma basa aikin tattara nectar ko pollen k**ar yadda worker bees mata suke yi.
Worker bees sune suke fita neman abinci, suna kawo nectar da pollen, suna sarrafa shi kuma suna kula da sauran abubuwan da colony ke buƙata.
Drone kuwa yana da muhimmiyar rawa:
Yana fita daga hive domin neman queen da take cikin mating flight (Lokacin saduwa)
Idan ya yi nasarar saduwa da queen, tsarin jikinsa yana sa sashen haihuwarsa ya fita daga jikinsa, kuma drone ɗin ya mutu bayan mating.
Amma fa akwai wani abu mai ban mamaki!
Drone da bai samu damar saduwa da queen ba, zai iya ci gaba da rayuwa na wani lokaci yana cin abincin da worker bees s**a tanada, kenan dai mijin hajia ne...🤣
Idan lokacin sanyi ya shigo matan zuma suna korar duk wani drone Bee daga colony ɗinsu inda yake fita yunwa ta kashe shi
Saboda haka, baza mu iya kiranshi “malalaci” ba kawai sai dai muce mijin hajia. 😄
Kowane mazauni a gidan zuma yana da aikin da aka tsara masa.
Worker bee _tattara abinci da kula da colony
Drone _ aikin (saduwa)
Queen _ samar da ƙwai da ci gaba da zuriyar colony
Darasin da za mu koya:
Abin da yake k**a da “rashin aiki” a idanun mu, wani lokaci yana iya kasancewa wani muhimmin aiki da aka tsara shi domin yin sa.
LAMARIN UBANGIJI SAI KALLO! 🐝
© Sir Wisdom