13/02/2025
07
Fassarar Littafin Ahkamunnisa'i (Hukunce-hukuncen Mata) Na Mal. Abdurrahman Ibnul Jauzi (597) Rahimahullah.
Babi Na Bakwai (07): Ladubban Shiga Bayangida Da Sifar Tsarkin Dutse
1. Duk wanda ya yi nufin shiga bayan gida, to ya nisanci duk abunda ke da ambaton Allah, k**ar zobe da mak**antansa, sannan ya gabatar da ƙafar hagu yayin shiga sannan ya ce: "اللهم إني أعوذ بك من الخبث والخبائث", "ya Allah ina neman tsarinka daga Sheɗanu da dukkan ƙazanta" (Bukhari:6322, Muslim: 375)
2. Kar ya ɗaga tufafinsa har sai ya kusa kaiwa ƙasa, kar ya fuskanci alƙibla kuma kar ya juya mata baya/kar ya fuskanci rana ko wata, kar ya yi fitsari a rami ko kwatami, ko ƙarƙashin bishiya mai ƴaƴa, ko a inuwar gini, ko a tsakiyar hanya, kar ya daɗe a tsugune sama da buƙata ko ƙasa da buƙata, kar ya yi magana yayin biyan buƙata, idan ya yi atishawa ya yi hamdala a zuci, idan ya idar, sai ya bar wajen da ya biya buƙatar zuwa gefe don yin tsarki.
3. Yin tsarki wajibi ne a kan duk abun da yake fita daga gaba ko baya ban da tusa, kuma idan ƙazantar da aka fitar bata ɓata jiki ba (ta tsaya a iya mafitarta), to ana iya wadatuwa da Tsarkin Dutse.
4. Sifar abun da za a yi tsarki da shi shi ne ya zama daskararre, mai tsarki, ba abin ci ba, kuma ba abu mai wata alfarma ba, haka ba abun da aka ciro daga jikin mai rai ba. Ƙarƙashin wannan za a yi tsarki da dutse, ice, tsumma, ƙasa, da mak**antansu. Abubuwan da ake ci kuma za su fita daga ciki, haka kashin dabbobi da ƙashi, saboda kasancewarsu abincin Aljanu, kuma ana iya tsarki da dutse ɗaya da yake da rassa uku (a matsayin uku).
5. Malamanmu sun yi saɓani a kan sifar Tsarkin dutse, mafi yawa s**a ce: mutum zai ɗauki dutse na farko da hanunsa na hagu, ya fara da gefen ɗuwawunsa na dama daga farkonsa har ya kai ƙarshe, sannan ya dawo da shi zuwa inda ya fara, sannan ya ɗauki dutse na biyu, ya fara da gefen ɗuwawunsa na hagu, daga farkonsa har ya kai ƙarshe, sai ya ɗauki dutse na uku, ya goge kewaye duburar da shi, sannan katso da shi ta tsakiya.
-Malam Sharif Abu Ja'afar da Ibnu Aƙilu sun tafi a kan cewa, mutum zai ɗauki kowane dutse ne ya game gabaɗaya mahallin najasar da shi, domin idan bai yi haka ba, zai zama ya goge kowane gefe ne sau ɗaya, alhali ana so ne ya zama na yi cikakken tsarki da kowane dutse, sai na gaba ya zama maimaici.
6. Idan najasar ba ta gushe bayan amfani da duwatsu ukun, sai a yi ta ƙarawa har sai ta gushe gabaɗaya.
7. An so ga namiji (Idan zai yi tsarkin fitsari da bayangida) ya fara da na fitsari, saboda kar hanunsa ya ɓaci da najasa idan ya fara da baya, amma mace tana da zaɓi tsakanin farawa da baya ko gaba.
8. Abun da ya fi falala shi ne a biyo tsarkin dutse da na ruwa, amma idan mutum ya so taƙaituwa ga ɗaya, to na ruwa shi ya fi falala.
9. Idan mace budurwa ce, idan ta so za ta shafe gurbin fitsari da abun tsarkin da aka siffanta, a lamba ta (4), idan kuma ta so sai ta wanke, amma duk sanda najasar ta shafi wasu guraren daban, ruwa ne kawai yake halatta wajen kawar da ita. Idan kuma wadda ta taɓa aure ce, to idan fitsarin ya fito kaifi ɗaya, bai fantsama ba, wajibi ne ta wanke da ruwa, idan kuma ya fantsama har wani abu ya shiga farjinta, shi ma wajibi ne ta wanke shi da ruwa, amma idan ba ta sani ba shin ya shiga farjinta ko bai shiga ba? To an so ta wanke, amma bai wajaba ba. Ɓoye wannan ilimin ga mace kuwa cin ilimi ne, saboda duk san da ya wajaba a wanke wata najasa kuma ba a wanke ta ba, to za ta ɓata ingancin salla.
10. Wasu cikin mata suna ɗauka idan s**a wanke fitsarin da ya shiga cikin farjinsu, cewa hakan yana ɓata azumi, amma ba haka ba ne, saboda ruwa ba ya isa ga hanji ta farji, saboda haka wajibi ne a sa yatsu a wanke shi (fitsarin da ya shiga farji) kuma hakan ba ya ɓata azumi saboda hukuncinsa k**ar baki ne, saɓanin dubura, shi ne yake kaiwa ga hanji.
11. Idan mutum zai fito daga banɗaki, sai ya gabatar da ƙafarsa ta dama, sannan ya ce: "غفرانك،", "ya Allah ina neman gafararka" (Tirmizi:7).