SHURA TV

SHURA TV An bude Wannan Gidan Talabijin ne domin ilmantar wa hadi da fadakarwa, zamu cigaba da wallafa muku labaran duniya a ko da yaushe.

Matatar man fetur ta Dangote da ke Nijeriya ta ja hankalin masu zuba jari inda s**a sayi hannayen-jari na fiye da naira ...
15/09/2026

Matatar man fetur ta Dangote da ke Nijeriya ta ja hankalin masu zuba jari inda s**a sayi hannayen-jari na fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan buɗe sayar da hannayen-jarin ga jama’a a karon farko a ranar Litinin, a cewar jami’ai.
👉

YANZU-YANZU: An yi wa Yari gargadi kan kusancinsa da Ali Modu SheriffYayin da babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara matsowa...
15/09/2026

YANZU-YANZU: An yi wa Yari gargadi kan kusancinsa da Ali Modu Sheriff

Yayin da babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara matsowa, wasu masu lura da harkokin siyasa sun shawarci tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, da ya yi taka-tsantsan wajen zaɓen mutanen da yake hulɗa da su a fagen siyasa, Musamman ma Masu mummunan tarihi, Kamar Yadda matasa Yan Jam’iyyar APC s**a bayyana.

Wannan gargadi ya samo asali ne daga ce-ce-kucen da ke tattare da alaƙar siyasar Yari da tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, wanda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasar Najeriya na tsawon shekaru.

Masu s**ar wannan kusanci sun ce akwai wasu daga cikin al’ummar Arewa da har yanzu suke da tambayoyi da damuwa game da tarihin siyasar Sheriff da wasu abubuwan da s**a faru a shekarun baya, Musamman batutuwan dake da alaka da tsaron Najeriya.

Sun yi gargadin cewa rashin la’akari da irin waɗannan damuwar jama’a na iya haifar da matsaloli ga duk wani ɗan siyasa da ke neman gina sabuwar tafiyar siyasa gabanin zaɓen 2027.

Da Dumi-Dumi: Dankabo Ya Yi Wa Abba Kirari, Ya Ce ‘Falle Biyu’ Ce A Kano Ko Sunki Bare Ma Sun Yadda" Jigo a siyasar Kano...
03/09/2026

Da Dumi-Dumi: Dankabo Ya Yi Wa Abba Kirari, Ya Ce ‘Falle Biyu’ Ce A Kano Ko Sunki Bare Ma Sun Yadda"

Jigo a siyasar Kano, Kuma Tsohon dan takarar majalisar tarayya ta Kabo da Gwarzo Hon. Fahad Dankabo, ya bayyana Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a matsayin “Father of Future Kano”, tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga gwamnan yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

Dankabo ya bayyana matsayinsa ne a cikin wani saƙon da ya wallafa, a Shafinsa na Facebook, inda ya yi amfani da kalaman kirari da yabo wajen bayyana salon jagorancin Gwamna Abba da kuma abin da ya kira nasarorin gwamnan wajen tafiyar da jihar.

A cikin saƙon, Dankabo ya kira Abba da “Balaraben Gwamna mai sa duhu ya zama kamar haske”, tare da bayyana shi a matsayin “Balaraben Gwamna mai sirka fire” da kuma wanda ke da “remote” na kashe wuta da ruwan sanyi.

Ya kuma yi amfani da kalmar “Abba-Gida-Gida-Abba”, yana mai cewa sunan Abba ya samu karɓuwa a tsakanin al’ummar jihar Kano.

Dangane da siyasar 2027, Dankabo ya bayyana cewa shi da magoya bayansa za su kasance tare da Gwamna Abba “duk inda ya taka”, yana mai jaddada goyon bayansa ga abin da ya kira Jahadi don “Kano First.”

“Duk inda ka taka muna tare da kai, ko da fire ko ba fire, da ruwan sanyi za mu dafa ganda,” in ji Dankabo.

Ya kuma yi hasashen samun nasarar Abba a zaɓen da ke tafe, inda ya ce da yardar Allah da kuma goyon bayan al’ummar Kano, gwamnan zai ci gaba da jagorantar jihar.

Dankabo ya kammala saƙonsa da kalaman “Falle Biyu Ce Insha Allah”, abin da ke nuni da goyon bayansa ga yiwuwar sake zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf a 2027.

TIRKASHI: Zamanka Gwamnan Katsina Bai Haifar Wa Jihar Komai Ba Face Koma Baya” Radda, “Ka Mayar Da Hankali Kan Al’ummark...
01/09/2026

TIRKASHI: Zamanka Gwamnan Katsina Bai Haifar Wa Jihar Komai Ba Face Koma Baya” Radda, “Ka Mayar Da Hankali Kan Al’ummarka, Ibrahim Masari Ba Tsaran Ka Ba Ne - S. A. Zangina

Wani ɗan asalin ƙaramar hukumar Daura a Jihar Katsina, Sani Ahmad Zangina, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, da ya gaggauta sasantawa da Alhaji Ibrahim Masari, yana mai cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu na iya yin illa ga muradun Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ci gaban jihar.

Zangina, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyyar APC kuma mai biyayya ga Shugaba Tinubu, yana mai cewa ya rubuta sanarwar ne cikin damuwa da kuma fushi kan yadda rikicin siyasa ke gudana a jihar.

Ya ce ba maƙiyin Gwamna Radda ba ne, sai dai yana ganin ya zama wajibi a faɗi gaskiya domin kare muradun jam’iyyar APC, gwamnatin Tinubu da kuma al’ummar Katsina.

A cewar Zangina, tarihi ba zai manta da irin gudunmawar da Ibrahim Masari ya bayar wajen yaɗa siyasar Tinubu a Arewa maso Yamma, musamman a Jihar Katsina, ba.

Ya ce a lokacin da ambaton sunan Tinubu a wasu sassan Arewa ke fuskantar ƙalubale, Masari ya tsaya tsayin daka wajen yaɗa saƙon siyasar Tinubu tare da taimakawa wajen ƙarfafa APC a yankin.

Zangina ya ƙara da cewa a matsayinsa na Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Sauran Al’amura, Masari na daga cikin waɗanda ke bayyana irin tallafi, ayyukan ci gaba, naɗe-naɗe da sauran abubuwan da gwamnatin Tinubu ke samarwa al’ummar Arewa.

Sai dai ya yi zargin cewa rashin zaman lafiya a fagen siyasar Katsina na iya rage tasirin waɗannan abubuwa a idon al’umma.

Zangina ya buƙaci Gwamna Radda da ya ajiye duk wani saɓani na siyasa, ya rungumi zaman lafiya domin kare muradin sake zaɓen Shugaba Tinubu a wa’adi na biyu.

Ya ce idan Ibrahim Masari yana da burin zama Gwamnan Katsina, da tuni ya samu damar cimma hakan, saboda a cewarsa, Masari na da magoya baya, tsarin siyasa da kuma karɓuwa a tsakanin al’umma.

Sai dai ya ce Masari ya zaɓi zuwa Abuja domin yi wa Shugaba Tinubu hidima da kuma kare muradun al’ummar Arewa, maimakon neman kujerar gwamna.

Zangina ya bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakanin Radda da Masari ba za a kallonta a matsayin rikicin mutane biyu kawai ba, yana mai cewa tana iya shafar burin Shugaba Tinubu na samun wa’adi na biyu da kuma ci gaban Jihar Katsina.

Ya ce yayin da ake fama da rikicin siyasa, al’ummar jihar na ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro da tattalin arziki.

Ya ambaci matsalar hare-haren ‘yan bindiga a Kankara, ƙalubalen da manoma ke fuskanta a Batsari, da kuma matsalolin talauci a Daura, Funtua da Malumfashi.

A cewarsa, abin da al’ummar Katsina ke buƙata shi ne ingantaccen shugabanci, tsaro, abinci da mafita ga matsalolin rayuwa, ba rikicin siyasa ba.

Zangina ya gabatar da shawarwari guda uku ga Gwamna Radda.Ya buƙaci Gwamnan da ya kira Ibrahim Masari su zauna su tattauna domin kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakaninsu, domin maslahar Katsina da kuma muradun Shugaba Tinubu.

Sani ya bayyana Masari a matsayin mutum mai muhimmiyar rawa a harkokin siyasar Shugaba Tinubu, yana mai cewa duk wani rikici da shi na iya yin illa ga dangantakar siyasar Katsina da Abuja.

Ya buƙaci Gwamnan da ya tabbatar da cewa abubuwan da gwamnatin Tinubu ke samarwa Arewa sun haifar da sauyi kai tsaye a rayuwar al’ummar Katsina ta fuskar abinci, tsaro, ayyukan ci gaba da samar da fata.

A ƙarshe, S.A. Zangina ya ce tarihi ba zai fi mayar da hankali kan yawan rikice-rikicen siyasar da aka yi a tsakanin Radda da Masari ba, sai dai kan yadda Jihar Katsina ta kasance wajen samun zaman lafiya, tsaro da ci gaba a ƙarƙashin mulkin Radda.

Ya kuma jaddada cewa irin rawar da Gwamnan zai taka wajen tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2027 za ta kasance wani ɓangare na abin da tarihi zai yi la’akari da shi.

Zangina ya yi kira ga Gwamna Radda da ya “ajiye takobin rikici”, yana mai cewa Katsina ta fi ƙarfin girman kai, son zuciya da rarrabuwar kai.

“Saboda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ku ajiye takobin rikici. Katsina ta fi girman kai da son zuciya. Ya isa da girman kai, ya isa da rarrabuwar kai — ku yi aiki domin al’umma,” in ji shi.

Rahoton Zuhair Ali Ibraheem

01/09/2026

YANZU-YANZU: Yadda Dubban Yan Arewa ke rera wakokin kira ga Shugaba Tunubu akan Ya dawo karo na Biyu.

Karkashin kungiyar Tinibu again ta matawalle

TIRKASHI: Dole Ku Cire Ali Modu Sheriff Ko Mu Janye Goyon Bayanmu Ga Tinubu” — Magoya Bayan TinubuWata ƙungiyar magoya b...
31/08/2026

TIRKASHI: Dole Ku Cire Ali Modu Sheriff Ko Mu Janye Goyon Bayanmu Ga Tinubu” — Magoya Bayan Tinubu

Wata ƙungiyar magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai fafutukar ganin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, ta yi barazanar dakatar da goyon Bayan da take bayarwa na son rai idan aka ci gaba da sanya tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, cikin jerin sunayen Masu yaƙin neman zaɓen APC. Ƙungiyar ta bayyana matsayinta ne a wata takardar ƙorafi mai kwanan wata 25 ga Agusta, 2026, wadda ta aika wa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, tare da aika kwafinta zuwa Fadar Shugaban Ƙasa.

Ƙungiyar ta ce babban abin da take adawa da shi shi ne naɗa Sheriff a matsayin Mai Gudanar da Yaƙin Neman Zaɓen APC na Yankin Arewa maso Gabas a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comrade Sani Ahmad Zangina, ya ce har yanzu ƙungiyar tana da cikakken goyon bayan sake zaɓen Tinubu, amma ba za ta iya ci gaba da gudanar da gangamin wayar da kan jama'a a matakin ƙasa ba a ƙarƙashin tsarin da Sheriff ke jagorantar yaƙin neman zaɓen a Arewa maso Gabas.

“Goyon bayanmu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa bai girgiza ba, amma ba za mu iya ci gaba da bayar da tallafinmu na son rai a ƙarƙashin tsarin da ya sanya Sanata Ali Modu Sheriff a sahun gaba na yaƙin neman zaɓe a Arewa maso Gabas ba,” in ji Zangina. Ƙungiyar ta ce damuwarta ta samo asali ne, a wani ɓangare, daga tsofaffin zarge-zargen da aka taɓa yi wa Sheriff na alaƙa da Boko Haram, tana mai cewa irin waɗannan zarge-zarge na iya shafar yadda jama'a ke kallonsa tare da rage amincewar wasu magoya bayan APC a yankin.

Sai dai Sheriff ya sha musanta duk wata alaƙa ko hannu wajen ɗaukar nauyin Bòkô Härám, yana bayyana zarge-zargen da ake yi masa a matsayin marasa tushe.
Zangina ya jaddada cewa ƙungiyar ba ta cewa an taɓa samun Sheriff da laifin da ya shafi waɗannan zarge-zargen ba, amma ta ce ya kamata a yi la’akari da irin zarge-zargen na baya da kuma tasirinsu a siyasa wajen zaɓen mutumin da zai jagoranci yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa a Arewa maso Gabas.

Wannan mataki ya zo ne jim kaɗan bayan Nigeria Rescue & Renewal Movement (NRRM) ta kuma nuna damuwa kan shigar da Sheriff cikin tsarin yaƙin neman zaɓen APC, inda ta yi kira da a sake duba tsarin kwamitin bisa dalilan da s**a shafi gaskiya, riƙon amana da amincewar jama'a.
Sai dai ƙungiyar Grassroots Movement ta ɗauki matakin gaba, inda ta yi barazanar dakatar da duk wani gangamin wayar da kan jama'a da take yi na son rai domin sake zaɓen Tinubu idan aka bar Sheriff a matsayinsa.

Ƙungiyar ta ce, Matukar ba a cire sunansa daga cikin jagororin tsarin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu ba, za a janye ƙuri’unmu da na dukkan mambobin ƙungiyarmu daga duk wani ƙarin aikin son rai na sake zaɓen Shugaban Ƙasa a babban zaɓen 2027.”
Duk da matsayinta, ƙungiyar ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga takarar Tinubu, tana mai cewa adawarta ta shafi rawar da aka bai wa Sheriff ne kawai, ba kuma yunƙurin Shugaban Ƙasa na neman wa’adi na biyu ba.

Ƙungiyar ta kuma ce za ta ci gaba da bibiyar duk wani sabon ci gaba da ya shafi tsarin yaƙin neman zaɓen, tare da tattaunawa da shugabannin APC kan batutuwan da take ganin za su iya shafar ingancin gangamin neman ƙuri’un jama'a a Arewa maso Gabas gabanin zaɓen 2027.

WATA SABUWA: Za mu janye goyon bayanmu ga APC idan ba ta cire Ali Modu Sherrif daga cikin kwamitin tallar Tinubu ba Wata...
27/08/2026

WATA SABUWA: Za mu janye goyon bayanmu ga APC idan ba ta cire Ali Modu Sherrif daga cikin kwamitin tallar Tinubu ba

Wata kungiyar magoya bayan APC da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi barazanar janye goyon bayan da take ba shi bisa radin kanta, idan har tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Kungiyar mai suna Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, ta bayyana wannan gargadi ne cikin wata takardar korafi mai dauke da kwanan watan 25 ga Agusta, 2026, wadda ta aika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, tare da kwafin takardar zuwa fadar shugaban kasa.

Kungiyar ta ce korafinta ya ta’allaka ne musamman kan nada Sheriff a matsayin mai kula da yakin neman zaben APC na shiyyar Arewa maso Gabas, a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar domin zaben 2027.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Sani Ahmad Zangina, ya ce kungiyar na nan daram kan kudirinta na ganin an sake zaben Tinubu, amma ba za ta iya ci gaba da gangamin neman masa goyon baya ga talakawa ba muddin wannan tsari bai sauya ba.






DA DUMI-DUMI: Zan bawa Tinubu Kuri'a Miliyan 20 daga Arewa Matawalle, Ya sake jaddada Alkawarinsa Ga Tinubu. Bayan dawow...
26/08/2026

DA DUMI-DUMI: Zan bawa Tinubu Kuri'a Miliyan 20 daga Arewa Matawalle, Ya sake jaddada Alkawarinsa Ga Tinubu. Bayan dawowa gida Najeriya.
‎
‎Dubban magoya baya sun fito domin tarbar Ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Matawalle, bayan dawowarsa gida Najeriya, lamarin da ya sake jawo zazzafar muhawara kan ƙarfin siyasar Matawalle da kuma yiwuwar samun gagarumin goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
‎
‎Hotuna da bidiyoyin taron sun nuna yadda magoya baya s**a fito cikin ɗimbin jama'a domin tarbar tsohon gwamnan jihar Zamfara. Wannan gagarumar tarba ta sa wasu masu sharhi da magoya bayan jam'iyyar APC ke cewa alkawarin tattara kuri'u miliyan 20 daga Arewa domin Tinubu na iya zama abin da za a iya cimmawa, idan aka yi la'akari da irin ƙarfin da manyan jiga-jigan siyasar Arewa ke da shi a matakin ƙasa da ƙasa.
‎
‎A kwanakin baya, wata ƙungiyar magoya bayan Tinubu mai suna Northern Vanguard for Asiwaju ta bayyana aniyarta ta taimaka wajen tattara akalla kuri'u miliyan 20 ga shugaban ƙasar a zaɓen 2027, tana mai bayyana cewa za ta dogara da tsarin siyasa da magoya bayan Matawalle da sauran jiga-jigan APC a fadin Arewa.
‎
‎Amma babbar tambayar da mutane ke yi ita ce: Shin taron dubban mutane domin tarbar Matawalle yana nufin za a iya sauya wannan taro zuwa kuri'u miliyan 20?
‎
‎Amsar ita ce, yana yiwuwa a siyasance, amma ba abu ne mai sauƙi ba.
‎
‎Tarbar jama'a na iya nuna farin jini, tasiri da ƙarfin tsarin siyasa, amma zaɓe yana buƙatar abubuwa da dama. Dole ne a tabbatar da rajistar masu zaɓe, fitowarsu ranar zaɓe, haɗin kai tsakanin manyan jiga-jigan siyasa, da kuma yadda jama'a ke kallon manufofi da ayyukan gwamnati.
‎
‎Matawalle dai ya sha bayyana cewa yana da yakinin Arewa za ta nuna goyon bayanta ga Tinubu a 2027, yana mai cewa ayyukan gwamnati a yankin za su iya ƙara wa shugaban ƙasar farin jini.
‎

TIRKASHI: Shekarun Rayuwarmu Ba Mu Taba Ganin Jami’in Gwamnati Ya Zo Kauyenmu Don Samar da Makaranta, Asibiti Ko Wutar L...
15/08/2026

TIRKASHI: Shekarun Rayuwarmu Ba Mu Taba Ganin Jami’in Gwamnati Ya Zo Kauyenmu Don Samar da Makaranta, Asibiti Ko Wutar Lantarki Ba — Mazauna Kauyen Boje, Daura

Wani dattijo mai suna Usman Dauda, ɗan asalin Kauyen Boje da ke Daura, Jihar Katsina, ya bayyana cewa ya shafe shekaru 75 a duniya, amma bai taba ganin wani jami’in gwamnati ya zo kauyen nasu da nufin samar da makaranta, asibiti ko wutar lantarki ba.

Usman Dauda ya ce tun tasowarsa yana da burin yin karatun zamani da na addini, sai dai rashin makaranta a kauyen Boje ya hana shi samun damar cimma wannan buri.

Ya bayyana cewa matsalar rashin makaranta ta dade tana addabar al’ummar yankin, musamman yara da matasa, wadanda ke fuskantar matsaloli wajen samun ilimi.

A nasa bangaren, wani mazaunin kauyen mai suna Ibrahim Iliyasu, ya bayyana cewa akwai tazarar kusan kilomita 20 tsakanin Kauyen Boje da makarantar da ta fi kusa da su.

A cewarsa, wannan nisa ya sa yara da dama ba sa iya zuwa makaranta, lamarin da ke haifar da karuwar yawan mutanen da ke tasowa ba tare da samun cikakken ilimin zamani ko na addini ba.

Mazauna Kauyen Boje sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da suke ciki, inda s**a yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da Gwamnatin Tarayya da su duba matsalolin da suke fuskanta tare da gina makaranta a yankin, da kuma samar da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.

Sai dai a nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Daura, Bala Musa Daura, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina na kokarin bunkasa harkar ilimi a fadin jihar.

Bala Musa Daura ya yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda, bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa harkar ilimi, ciki har da samar da kujeru da gyaran makarantu a Daura da sauran sassan jihar.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da daukar matakan inganta harkar ilimi tare da samar da abubuwan more rayuwa a makarantu, domin tabbatar da cewa yara da ke yankunan karkara sun samu damar samun ilimi kamar sauran al’ummar jihar.

TIRKASHI: Bayan Ficewa Daga Tafiyar Atiku Abubakar, Dr. Aslam Aliyu Ta Kai Wa Tinubu Ziyara.A wani sabon salo da ya ɗauk...
03/08/2026

TIRKASHI: Bayan Ficewa Daga Tafiyar Atiku Abubakar, Dr. Aslam Aliyu Ta Kai Wa Tinubu Ziyara.

A wani sabon salo da ya ɗauki hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya, tsohuwar ƙawanyar siyasar Atiku Abubakar, Dr. Aslam Aliyu, ta kai wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ziyara jim kaɗan bayan komawarta jam'iyyar APC, lamarin da ya ƙara jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa.

Dr. Aslam Aliyu, wadda ta kasance cikin masu fafutukar siyasar Atiku Abubakar a baya, ta bayyana cewa ta yanke shawarar barin tafiyar adawa ne bayan ta gamsu cewa ba ta ga ingantaccen tsari ko sahihin shirin ceto Najeriya daga ɓangaren da ta fito ba. Ta ce ta zaɓi shiga APC ne domin bayar da gudummawa ga abin da ta yi imanin zai amfani ƙasa.

Masu goyon bayanta na bayyana matakin nata a matsayin "barin duhun siyasar adawa zuwa hasken tafiyar Bola Ahmed Tinubu," suna masu cewa ziyarar da ta kai wa Shugaban Ƙasa alama ce ta cikakken goyon baya ga manufofin gwamnatin APC da shirin Renewed Hope. Sai dai wannan furuci yana nuna ra'ayin magoya bayanta ne, ba tabbatacciyar gaskiya ba.

Masu nazarin siyasa na ganin sauya sheƙar Dr. Aslam Aliyu na iya ƙara ƙarfafa APC musamman a Arewacin Najeriya, duba da irin rawar da ta taka a siyasar adawa a shekarun baya. A nata ɓangaren, ta yi kira ga matasa, mata da sauran 'yan Najeriya masu kishin ƙasa da su haɗa kai domin tallafa wa shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Address

Gaida Makada Layina Taransufuma
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SHURA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share