
28/09/2025
Sponsored.
DA ƊUMI-ƊUMI: Dan Majalisa Nalaraba ya Raba Tallafin Karatu ga Matasa 500 a Jihar Nasarawa.
Kamar yadda masu iya magana ke cewa gina matasa shine gina ƙasa, ɗan siyasa Nalaraba ya sake nuna ƙoƙarinsa da bajintarsa wajen bunƙasa ilimi da ci gaban al’ummar Mazaɓarsa na jihar Nasarawa.
Dan Majalisa Nalaraba, wanda ya zage dantse ganin ya kawo Federal College of Education zuwa jiharsa, yanzu ya raba tallafin karatu ga ɗalibai 500 daga sassa daban-daban na jihar Nasarawa, Kowane ɗalibi ya samu ₦100,000 domin tallafa musu wajen ci gaba da karatu.
Ya bayyana cewa, manufarsa ba ta ta’allaka kan ƙabila ko jam’iyyar siyasa ba, domin ɗaliban da s**a ci gajiyar tallafin sun fito ne daga kowane yanki na jihar.
Nalaraba ya jaddada cewa, bai k**ata matasa su ci gaba da zama kayan aikin Yan siyasa ba, inda ya ce: "Ilimi shi ne makamin ci gaba da ya k**ata dukkan matasa su riƙe, Gina matasa shi ne gina ƙasa." in ji shi.
Manazarta kan lamarin siyasa na ganin cewa irin wannan aiki na aikin bajinta na da Alaƙa da jagoranci na gaskiya. A cewarsu, mulki ba wai kawai ayi alkawura ba ne, Cika alkawari shine ginshiƙin jagorancin k**ar yanda Nalaraba yake yi ma jama'a.