10/11/2023
: IN BAKI SAN GARI BA SAURARI DAKA.
Kalamanta dukkan su dariya s**a bani , nafi dauka cewa tana irin marisar Soshiyal Midiya ne domin jawa kanta ihun tayi marisa . Jihar Kano tamkar jan itacen marke ne , in kai garaje da gangancin sara shi lalle za kai kwaliya.
Wasu kalaman basa bukatar raddi saboda Wasa ne , wasu kuma kalaman nata kwaliya ne .
1- Cin wake da shinkafa : Wato rashin zurfin iliminta ya sanya ta gaza gano cewa abunci na cikin al'adu ( Allah ya sa ta san mai ake nufi da al'ada ) don haka duk al'ummar da take da cigaba da tarihi zaka same ta da wani nau'in abunci da ta ginu akan sa , wanda kaduna bata daga cikin masu wannan wayewa don bata da wani abunci da ta ginu akan sa.
2- Mata basa tuki a Kano : Wannan na nuni da tarbiyar addini da al'adar mai tsari , yawon mata saki ba kaidi na daga rashin kunya da tarbiya al'umma , Mata ashirin din da tace ta gani babu musu masu lalurar hawa motar ne .
3- Zuwa cin abunci restaurant : Matan Kano masu aure da Yan mata suna kan waccar tarbiya da na fada a sama , duk abun da suke bukata mazaje da iyayensu ne ke sama musu a gida basa bukatar zuwa gidan cin abunci , don haka duk macen da take zuwa irin wajan dole ai mata wani kallo. Allah ya taimake ta ma bata fada hannun Hisbah ba.
4- Bama Turanci : To menene a turancin , yare ne kamar Hausa , Fulatanci , Yoruba da sauransu , ita da take walagilu ita ke ganin turancin wata kaniya.
5- Yaro da kudi : kowa ya ga Barbela da farinta ya ganta . Mutane Kano ba cima zaune bane , ba kamar Yan kaduna Yan Yahoo da jiyar ta fashe.
6- Iya wanka : Shi wanka yana dacewa ne da muhalli , kowa ne irin muhalli akwai kallon wankansu.
Tace " Mu Yan kaduna a komai mun hadu , but we don't have money to spend extravagantly ".
Yakub El-Usman Arzai