16/06/2025
MATSALAR DANNAU YAYIN BACCI - [SLEEP PARALYSIS]
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Dannau wani yanayi ne da mutane kan samu kansu ahalin bacci, yakan iya faruwa sau daya ga wasu a rayuwa, yayin da wasu kuma kan rika fuskantar yanayin akai-akai. Yanayi ne me kama.da mutuwa duk da yakan kasance mutum na acikin hayyacinsa farke saide sam yakan rasa ikon motsawa ko magana.
Wani lokacin ma yakan zamo idon mutum abude zahiri duk da cikin bacci yake; abunda wasu kan kira da bacin zomo... toh saide hakan duk baisa mutanen dake kusa ko yake jin muryarsu fahimtar cewa yana cikin mawuyacin hali ko yana bukatar dauki an maquresa.
Shiyasa ga duk meson fahimtar me ake nufi da FIRGICI toh dannau shine cikakken misalin firgici ko ince ihunka banza domin ko ihun kayi ba'a ji, ba'a san ma kanayi ba 🌻
---------------------‐-------------------------------------------
ALAMOMIN DANNAU
---------------------‐-------------------------------------------
Mutane kan fuskanci ma bambantan alamu; Saide duk yana daga alamun dannau ya zamto:
■- Mutum yaji kamar annan-naɗesa cikin wani bargo me nauyi, ko kamar anɗaure hannuwa da kafafunsa a mike kamar gawa, wasu kuma suji kamar anshakesu sun kasa numfashi, wasu kamar wani abu ya kakare musu a mokogoro sun kasa shakar iska, wasu kanji sun kasa magana, wasu kuma su akaran kansu sunji suna maganar amma kuma babu wanda yake jinsu, sukan katsa motsa komi nasu, wasu kan rikajin tamkar mutuwa ce ta kusantosu🌻
---------------------‐-------------------------------------------
MEKE HADDASA HAKAN
---------------------‐-------------------------------------------
Daya daga manyan ababen dake haddasa hakan shine; Karancin bacci, wato mutane masu fama da larurar rashin bacci, ko kuma wadanda suke kin kwanciya su samarwa da jikinsu isashshen bacci,
Haka nan samun canjin lokutan bacci kai tsaye watakil saboda yanayin aiki ko tafiya zuwa wata kasa da lokaci ya bambanta sosai
Haka nan shan wasu magunguna dake aiki a kwakwalwa; kamar a mutane masu ciwon farfadiy