04/08/2026
Jama'a A Kula 😢
JAMA'A A YI HATTARA DA SABUWAR DABARAR BARAYIN BABURA!
Ana samun rahotannin cewa wasu barayin babura sun bullo da wata sabuwar hanya ta yaudarar mutane.
Daga misalin 10:00 na dare zuwa tsakar dare, s**an je tsakiyar hanya su zubar da kuɗi k**ar N10,000 ko fiye domin su ja hankalin masu wucewa.
Da zarar mutum ya tsaya domin ɗaukar kuɗin, sai su fito ba-zata su kai masa hari da sara, duka ko kwace dukiyarsa. A wasu lokuta ma lamarin kan kai ga rasa rai.
⚠️ Idan ka ga kuɗi a tsakar hanya musamman cikin dare, ka guji tsayawa domin ɗauka. Rayuwarka ta fi kowace dukiya muhimmanci.
📢 A taimaka a yaɗa wannan saƙo domin wayar da kan jama'a. Idan ka ga wani abu mai k**a da haka, ka sanar da jami'an tsaro mafi kusa.