09/09/2026
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa Ya Gabatar Da Daftarin Kasafin Kuɗin Shekarar 2027 Na Naira Biliyan 828.64 Ga Majalisar Dokokin Jihar.
Kasafin, mai taken “Building Your Future IV”, an gabatar da shi ne ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026, inda Katsina ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Daga cikin jimillar kasafin, Naira Biliyan 637.91 an ware su ne domin ayyukan raya ƙasa, yayin da aka ware Naira Biliyan 190.73 domin gudanar da ayyukan gwamnati.
Manyan fannoni da aka bai wa fifiko sun haɗa da ilimi wanda aka ware wa Naira Biliyan 83.82, manyan ayyuka Naira Biliyan 71.60, noma da kiwo Naira Biliyan 65.88bn, kiwon lafiya Naira Biliyan 53.64, raya karkara Naira Biliyan 50.51.
Gwamna Raɗɗa ya ce an tsara kasafin ne bayan tuntuɓar jama’a a faɗin gundumomi 361 na jihar, inda kowace mazaɓa ta bayyana aikin da ta fi buƙata, wanda aka shigar cikin tsarin kasafin 2027.
Ya ce gwamnatin ta kuma ci gaba da zuba jari a fannonin ilimi, lafiya, noma, ruwa, ababen more rayuwa da tsaro, tare da kashe sama da Naira Biliyan 7.5 kan harkokin tsaro a shekarar 2026.
A fannin ilimi, gwamnatin ta ware kuɗaɗe domin gyaran makarantu, tallafin karatu da biyan kuɗaɗen jarabawar SSCE, yayin da a fannin lafiya aka ci gaba da samar da kayan aiki da inganta cibiyoyin kiwon lafiya.
Gwamna Radda ya ce kasafin “Building Your Future IV” zai ci gaba da mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziki, raya ɗan Adam, samar da ababen more rayuwa, inganta ayyukan zamantakewa da ƙarfafa tsaro a Jihar Katsina.
Me za ku ce?