
21/05/2025
Wani mutum bayan ya karanta "my story" a page nawa yaga na sanya: Allah ya bayarwa iyayen Annabi Sallallahu alaihi Wasallama abinda yafi aljannah!
Sai ya tambaye Ni : Menene Allah ya bayarwa iyayen Annabi Sallallahu alaihi Wasallama wanda yafi aljannah???
Sai nayi masa ƴar hali! Kafin in bashi amsa na fara da tambayar sa:
1. Shin aljannah halittar Allah ce??
Yace:eh!!
2. Shin tsakanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da aljannah wanne ne yafi girma(matsayi) a wajen Allah??.
Yace: Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ne yafi girma.
Sai nace masa to yanzu ka fahimta! Yace :lallai kuwa.
"Bayan Allah subhanahu wata'ala ya gama zaɓe a cikin bayin sa game da su waye s**a cancanci zama iyaye ga wannan babban shugaba! Sayyidina Abdullahi da sayyidah Amina (A.S) sune Allah ya amince da cancantar su, wannan zaɓe ne na tun fili azal."
Allah ya bamu albarkacin iyayen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama duniya da lahira.
Ameeen bijahi Rasulillahi
صل الله عليه وسلم
Dr. Abdull A Ango