
09/06/2025
Technical Analysis 101: Charts.
Charts 📊 📈 wata hanyace da masana lissafin mathematics suke amfani da ita wajen isar da wani sako cikin taswira.
Duk da cewa akwai rabe-raben charts da dama da ake amfani dasu a yau a fannin lissafi..
A kasuwancin cryptocurrency ana amfani dasu wasu daga cikin charts domin fahimtar halayya, dabiu, da yanayi na chanjuwar farashi a kasuwar cryptocurrency.
Kamar yadda a post namu na baya munyi bayani akan ma’anar technical analysis..
Charts ana amfani dasu ne domin kai tsaye dan kasuwa yayi nazari akan halayyar farashi yayin da zai yanke hukunci akan alkiblar da kasuwa ta dosa ko ka bari ko kuma take shirin dosa..
Cikin charts da aka fi amfani dasu a kasuwancin cryptocurrency akwai.
1. Line charts (hoto na farko)
2. Histogram charts (hoto na biyu)
3. Pie charts da kuma
4. Candlestick charts (hoto na uku)
Charts da yafi kowanne muhimmanci wanda ake amfani dashi wajen fahimtar halayyar yan kasuwa (masu saye bulls 🐂 da masu sayarwa bears 🐻) shine candlesticks chats.
A post namuu na gaba in sha allahu zamu fara duba akan candlestick charts, ma’anar sa, dalilin samuwar sa, anatomy nasa da kuma psychology nasa.
Allah ya taimaka.
Gida Digital Hub.