22/11/2025
ABIN DA YAKE FARUWA A AREWA BA ƘARAMAR BARAZA BA CE GA MAKOMARMU
Abin da ya sake faruwa a Kebbi da Niger—inda ‘yan mata da yara ‘yan makaranta s**a ƙara fadawa hannun ‘yan bindiga—ba labari ba ne kawai. Tona asiri ne na irin koma bayan da yankin Arewa yake tafiya a ciki, kuma alamar cewa gaba ɗayan rayuwarmu tana cikin barazana.
A yau, a ƙarni na 21, ace mutane masu bindiga za su shiga makaranta cikin dare su ɗauke yara a kan babura su yi gaba ba tare da an k**a ko mutum ɗaya ba… wannan abin kunya ne, kuma cin mutunci ne ga Arewa gaba ɗaya.
Yara waɗanda ya k**ata su zama shugabannin gobe, suna zama ganima a hannun Yan ta’adda. Makarantu—inda ake koyar da ilimi—sun zama wurin tsoro. Kuma mu ne matasa, za mu fi shan wahala daga sak**akon irin wannan bala’i:
⛔ 1. Rashin Ilimi = Rashin Makoma
Idan makarantu suna rufe, idan iyaye suna tsoro su tura ‘ya’yansu, to gobe ba za mu samu injiniyoyi, likitoci, malamai, masana ko shugabanni daga Arewa ba. Za mu dawo daidai gurin da muka fito shekaru da yawa baya.
⛔ 2. Ƙarin Talauci da Rashin Aiki
Matasa da in basu sami ilimi ba, ba su da abin yi. Talauci zai ƙaru. Rashin aikin yi zai ƙaru. Kuma wannan yana ƙara jawo tawaya, banga, da lalacewar tarbiya.
⛔ 3. Ƙarin Cin Mutunci da Tsangwama daga Duniya
A yanzu wasu ƙasashen waje suna sa baki a lamuran mu. Suna magana akai, suna yin taro akai, suna yanke hukunci akai. Ace har sai Amurka ko Majalisar Dinkin Duniya suna gaya mana abin da ya k**ata mu yi domin kare yaranmu? Wannan babban abin kunya ne ga Arewa da Najeriya baki ɗaya.
Idan muka yi shiru, za mu dinga zama labari a jaridu:
“Yara 50 sun ɓace,” “Makaranta ta faɗa cikin hannun ‘yan ta’adda,” “Iyaye sun gudu da daddare”…
Wannan ba shi ne Arewar da kakanninmu s**a bar mana ba.
⛔ 4. Barazana ga Rayuwar Matasa
matasanmu ne ake kashewa a t**i. Na mu ake sacewa. Na mu ake yunƙurin lalatawa makoma da tunaninmu. Yanzu in zaka fita t**i da tsoro, sai ka yi tafiya da addu’a. Wannan halin ya isa.
Arewa ba za ta ci gaba ba idan iliminmu yana cikin hatsari.
Ba za mu samu gobe ba idan yaranmu suna bacewa yau.
Ba za mu samu mutunci ba idan kasashen waje suna koya mana yadda zamu kare kanmu.
Mu tashi mu yi magana. Mu tashi mu kare yankinmu. Arewa tamu ce, ba ta ’yan bindiga ba.
Mustapha Salisu ✍🏼