12/03/2026
ABABUWA 10 DA KOWANE NAMIJI DOLE YA SANI IDAN HAR YANA SON GINA KANSA.
Maganar gaskiya wacce dole ka hadiye ta; duniya bata girmama Namiji sai idan yana da amfani. Kafin ka ci gaba da kukan cewa an tsane ka ko ba a taimakon ka, ajiye son zuciya ka karanta wadannan gaskiyar guda 10:
1.Koyi Tsayawa Da Kafafunka:
A matsayinka na Namiji, kwanaki da yawa zasu zo wanda babu wanda zai tambayi lafiyarka. Koyi yadda zaka zauna kai kadai ba tare da kaji kewa ba. Mutumin da ya saba da kadaici, ba ya tsoron faduwa.
2. Daina Bin Mata, Fuskanci Makomarka: Yawan bin mata zai tsotse maka kuzarinka, natsuwarka, da kuma kudinka. Namijin da ya kashe kuruciyarsa wajen neman matan banza, zai manta da gina rayuwarsa. Gina kanka, mace ta gari ita zata neme ka da girmamawa.
3. Shekarun 20s Na Gina Rayuwa Ne, Ba Na Karya Ba: Wannan shine lokacin koyon sana'a da tafka kuskure. Daina kashe kudin da baka da su don ka burge mutane a Intanet. Wadanda kake kokarin burgewa, ko a jikinsu.
4. Koyi Sarrafa Kudi Da Wuri: Koda N1,000 kake samu a rana, koyi yin tattali. Maza da yawa ba talakawa ba ne don suna samun kadan, talakawa ne don ba su san yadda zasu sarrafa abin da s**a samu ba.
5. Kula Da Abokan Huldarka: Idan abokanka babu abin da suke magana a kai sai mata, c**a, da yawon banza, kai ne na gaba da zaka lalace. Koma cikin masu maganar kasuwanci da ci gaba.
6. Sarrafa Dabi'unka Tun Kafin Su Sarrafa Ka: Shaye-shaye ko C**a (Betting) suna farawa ne a hankali har su sace maka natsuwa da tarbiyya. Mutum mai kwarjini shine wanda yake kare kwakwalwarsa.
7. Yi Tafiyarka A Boye: Baka bukatar fada wa kowa shirinka. Ba duk wanda yake tafa maka ne yake son ci gabanka ba. Bar nasararka ta yi magana da kanta.
8. Koyi Sarrafa Fushinka: Rayuwa zata jarraba ka, mutane zasu ba ka haushi. Amma Namijin da ya iya hadiye fushinsa zai tsallake komai. Namiji mai karfi baya yawan surutu idan an bata masa rai.
9. Kula Da Lafiyar Jikinka Da Kwakwalwarka: Idan wani abu ya same ka, duniya zata ci gaba da tafiya ba tare da kai ba. Nemi halas, amma ka huta idan ka gaji.
10. Dogara Ga Allah Ka Ci Gaba Da Aiki: Akwai ranar da zaka ji k**ar ka hakura da komai. Yi addu'a a lokacin da kake jin rauni, ka yi aiki koda baka ganin riba a yanzu.
Dan uwa, gina kai ba abu ne mai sauki ba. Yana bukatar hakuri da horon zuciya. Amma watarana, rayuwar da ta wulakanta ka a baya, ita zata yi maka biyayya. A ranar zaka yi alfahari da cewa baka yanke kauna ba.
Allah yasa mudace.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️