
23/02/2024
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayar da umarnin raba tallafin abinci ga mutum fiye da 100,000 a birnin Maiduguri da ƙaramar hukumar Jere. Ya bayar da umarnin ne ranar Alhamis a yunƙurin gwamnatinsa na tallafa wa mutanen da ke fama da raɗaɗin talauci sakamakon tsadar rayuwa.