Muryar Malamai

Muryar Malamai Muna dora Nasiha da Fadakarwa kullum. Kuyi Following din mu Za ku anfana.

ABINDA YASA NABAR AQIDAR SHI'A😡Sunana Alh Dan Adam Amma anfi sanina da (ADAM) Ni mutumin kadunane ina wata anguwa maisun...
26/07/2025

ABINDA YASA NABAR AQIDAR SHI'A😡

Sunana Alh Dan Adam Amma anfi sanina da (ADAM)

Ni mutumin kadunane ina wata anguwa maisuna Unguwar rimi, Nakasanche Mai wannan AQIDAR tun tuni har nakai mastayin shugaban HURRAS na yankinmu.

Ma'ana Unguwar Rimi da kewaye.

Wallahi Wallahi Wallahi!!! Wannan maganar dazan fada babu kage chikinta Narantse da wanda Yake masanin gaibu ALLAH SWT, Ni Mai haline Masha Allah. Nabiyama kaina zuwa aikin hajj.

Anrage saura kwana kadan zamu tashi abokaina wanda basai nak**a sunan suba saboda tsaro, su s**ayi rakiyana zuwa Airfot, Bayan zamu tafi wajen shiga chikin jirgi sai s**a chemin wane zamu baka sako idan kun sauka a madina idan kaziyarchi ANNABI SAW. Ka La'anchi wane da wane. (wa'iyazu billahi) 😭. Sai banche musu komaiba nayi murmushi natafi nashiga jirgi.

Bayan munsauka a madina mukaje gida mukayi wanka muka shirya sai natafi masallachi kafin naje ziyara sai na dan zauna nahuta a Masallachi take sai bacci ya daukeni.

Nan take sai nayi mafarkin ANNABI SAW, Wallahi sai naga mutane biyu a tare dashi damansa yacemin SAYYADI ABUBAKAR ne. hagunsa yachemin SAYYADI UMMAR NE. sai yache sune akabaka sako Ka jefesu Ka La'anchesu ko? To kafin kafara dasu kafara dani 😭😭😭

Wallahi sai nak**a magiya inachewa ya rasullullah kayi hakuri Wallahi ban amsa musuba ni bazan iyaba hakanan dai sai yachemin kalli chaan, duban dazanyi saiga abokaina a wata irin WUTA wacce bazan iya misalintaba.

Yachemin to chaan shine makoman Mai zagin SAHABBAINA. 😭 Nafarka daga bacci gabadaya nahada gumi nayi zufa, Sai nakira waya gida inatambayan ina abokaina nayi takiran wayansu baya shiga.

Sai akachemin ai das**a raka Ka kafin sudawo s**ayi hastari s**a mutu kuma dukan su yan Nan chikin kaduna NE.

Nadimauche sosai Nan take nafita daga AQIDAR nayi Allah wadai da ita 😡

To Alhmdllh nadawo lafiya kuma yayana da matana sunfita saidai yayana su2 narasa yadda zanyi nashawo kansu sunyi nisa. Saidai Addu 'a. ...
Don Allah idan kasamu wannan katura wa jamm' a saboda katayi isar da wannan sakon.

Wallahi babu kage chikin wannan zanchen nawa, Kuma karya da ANNABI SAW shine karshen BALA'I.

ALLAH KASTARE MANA IMANIN MU.

Vanguard Hausa

19/07/2025

Allah Ya Jarrabe mu da Masifar 'Yan Bidi'a... Allah ya tsare mu da Iyalan mu🙏

1.. In tak**arka mulkii ne bakakai President Muhammad Buhari ba. 2… In tak**arka Arziki ne baka kai Alhaji Aminu dan tat...
16/07/2025

1.. In tak**arka mulkii ne bakakai President Muhammad Buhari ba.

2… In tak**arka Arziki ne baka kai Alhaji Aminu dan tata.. Dukiya ba.

3..In tak**arka ilimin addini ne da kuma gudun duniya bakakai Dr Idiris Abdul aziz Dutsen tanshi ba.

4. In tak**arka ilimin Boko da sanin duniya ne baka kai professor jibril Amin ba..

Duk kuma daga karshe sai Allah yakarbi rayikansu acikin wata 6..

Dan uwa kazama mai kankan dakai a wajen ALLAH 😔

ALLAHU AKBARShikenan fa Shugaba Buhari ya shiga gidansa na gaskiya, babu fita sai ranar tashin AlkiyamahInnalillahi wa i...
15/07/2025

ALLAHU AKBAR

Shikenan fa Shugaba Buhari ya shiga gidansa na gaskiya, babu fita sai ranar tashin Alkiyamah
Innalillahi wa inna ilaiHi raji'un😭

Don girman Allah jama'ah kowa ya yafe masa

Yaa Allah Ka hada Buhari da dukkan rahama, Ka bashi Aljannah don rahamarKa🙏

Rayuwa kenan! A daidai inda BUHARI ke zama yana hutawa a gidansa na Daura, a daidai nan ne ƙabarinsa yake. Babu wanda ya...
15/07/2025

Rayuwa kenan! A daidai inda BUHARI ke zama yana hutawa a gidansa na Daura, a daidai nan ne ƙabarinsa yake.

Babu wanda ya san a ina za'a binne shi in ya mutu. Mutum na iya rayuwa a birni, amma a wani ƙauye ko wata ƙasa da bai taɓa zuwa ba za'a binne shi. Rayuwa kowa da ajalinsa, kuma kowa da hisabinsa.

Fatanmu Allah yaji ƙan BABA BUHARI! Allah ya gafarta masa, ya sa ƙabarinsa ya kasance lambun Aljanna.

Naxeer Kaoje

Duk Mai Rai MAMACINEInnah lillahi Wa Innah Ilaihir Raji'unMuna Sanar Da Rasuwa Daya Daga Cikin Malaman Mu Sheikh Dr. Abd...
15/07/2025

Duk Mai Rai MAMACINE

Innah lillahi Wa Innah Ilaihir Raji'un

Muna Sanar Da Rasuwa Daya Daga Cikin Malaman Mu Sheikh Dr. Abdullahi Yankaba, Ya Rasu yana Tahiyya a Sallar Asuba.

Muna Mika Sakon Ta'aziyyar Mu Ga Iyalan Sa Da Shugabanni Da Al Ummar Duniya Baki Daya

Muna Rokon Allah Ta'ala Ya Bashi Aljannah Firdausil Aalah Amin

Muna Rokon Allah Ta'ala Ya Yimana kyakkyawan karshe Amin

Ga waɗanda suke tambaya game da jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Baba Buhari, na samu tabbaci cewa za a dauko gawarsa daga...
14/07/2025

Ga waɗanda suke tambaya game da jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Baba Buhari, na samu tabbaci cewa za a dauko gawarsa daga Landan da misalin ƙarfe 6 na safe gobe Talata, kuma za ta iso filin jirgin sama na Katsina da misalin ƙarfe 12 na rana in sha Allah. Saboda haka, ana sa ran jana’izar za ta gudana daga ƙarfe 2 na rana gobe a Daura in sha Allah.

Allah Ya jikansa Ya saka shi a Jannatul Firdaus tare da iyayenmu da dangi da masoya da s**a rigamu gidan gaskiya.

— Prof. Isa Ali Pantami ya rubuta

BANYI NADAMAR GOYON BAYAN BUHARI BAAllah Ya sani ni Datti Assalafiy sai da na sadaukar da rayuwata akan Buhari ba don ko...
14/07/2025

BANYI NADAMAR GOYON BAYAN BUHARI BA

Allah Ya sani ni Datti Assalafiy sai da na sadaukar da rayuwata akan Buhari ba don komai ba sai don yakinin da nake dashi a kansa cewa mutumin kirki ne, ga kuma dalilaina
👇
Baya neman matan banza
Baya Luwadi
Baya shan giya
Baya shan sigari
Baya shan miyagun kwayoyi
Baya cultism
Baya karya

Ba mutumin banza bane
Ba dan iska bane
Ba maciyin amana bane
Ba mayaudari bane
Ba azzalumi bane
Ba maha'inci bane

Yana da kirki
Yana da kawaici
Yana da son wasa
Yana da raha
Yana da hakuri
Yana da yafiya
Yana da kawar da kai
Yana da son talakawa
Yana da tausayin talakawa
Yana son zaman lafiya
Yana da tsananin kishin Nigeria

Zai yi wahala mutum yayi aikin Soja ba'a sameshi da wa su miyagun dabi'un da na lissafa a sama ba, amma Buhari ya kubuta daga wannan

Buhari ya mulki Nigeria a Soja da farar hula amma ba'a taba k**ashi da laifin satar kobo ba

Idan ka tara dukkan 'yan siyasar Nigeria, kai da dukkan al'ummar Nigeria gaba daya da wahala a samu mai kyawun hali irin na Buhari

Saboda gaskiyarsa har ana masa lakabi da mai gaskiya, sai dai ya hadu da mummunan cin amana daga wasu makarrabansa da s**a tayashi mulki

Kamar kowani dan adam, Buhari yana da nasa ajizancin da kura-kurai wanda muke fatan Allah Ya yafe masa

Yaa Allah Ka tsunduma Shugaba Buhari a cikin Aljannah Madaukakiya don rahamarKa🙏

ZA’A GUDANAR DA JANA’IZAR MARIGAYI MUHAMMADU BUHARI A DAURA ~~Inji GWAMNA DIKKO RADDAGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko ...
13/07/2025

ZA’A GUDANAR DA JANA’IZAR MARIGAYI MUHAMMADU BUHARI A DAURA

~~Inji GWAMNA DIKKO RADDA

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa jana’izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari (GCFR), za a gudanar da ita ne a garin haihuwarsa, Daura, da ke Jihar Katsina.

Gwamnan ya bayyana hakan ne daga birnin London, inda ya ke a yanzu domin jajantawa iyalan marigayin da kuma tsara yadda za a dawo da gawar sa zuwa Najeriya.

A cewarsa:

“Mun yanke shawarar gudanar da jana’izar mai girma tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Daura, inda ya taso kuma ya kafa tarihi. Wannan mataki na da nufin girmamawa da karrama rayuwarsa da gudummawar da ya bayar ga ƙasa.”

Shirye-shiryen Jana’iza:
• Za a dawo da gawar Buhari daga London zuwa Najeriya cikin kwanaki masu zuwa.
• Ana sa ran shugabannin ƙasa, gwamnoni, ministoci da manyan jami’an gwamnati za su halarci jana’izar.
• An tsara taron addu’o’i da yi wa marigayin addu’ar rahama a Daura.

Muna roƙon ALLAH ya gafarta wa Marigayi Muhammadu Buhari, ya sa kabarinsa ta zama lambun Aljanna, ya kuma bai wa iyalansa da al’ummar Najeriya hakurin jure wannan babban rashi.

TSAKANI DA ALLAH NI DAI NA FARA YIN SHAKKU AKAN ILIMIN MALAM IBRAHIM MAKARI, HASALIMA INA TUHUMAR SHI AKAI.   Dalilaina ...
13/07/2025

TSAKANI DA ALLAH NI DAI NA FARA YIN SHAKKU AKAN ILIMIN MALAM IBRAHIM MAKARI, HASALIMA INA TUHUMAR SHI AKAI.
Dalilaina kuwa sune, dukkannin malaman Allah magada annabawa, k**a daga kan malaman Izala, Tijjaniyya da kuma Kadiriyya, kowa yana kokarin bawa daliban shi/mabiyan shi ilimin addini mai kyau, mai tsarki da tsafta, suma daliban suna diban ilimin addini, k**a daga kan babban kundi, wato tafsirin alkur'ani, zuwa manyan-manyan littattafan koyon addini da ibada, ga misalan su k**ar haka:-
1.Sahihul Bukhari
2.Sahihu Muslim
3.Muwadda Malik
4.Tirmizi
5.Ibn Maja
6.Sunanu Nasa'i
7.Sunanu Abi Daauwd dss, domin sanin yadda za'a koyi addini da ibada a bautawa Allah, al'ummar musulmai suna fahimta, suna amfana, sannan kuma suna bautawa Allah lami-lafiya, cikin aminci da nutsuwa.
Sai dai KASHHHHHH, shi malam MAKARI abin ba haka yake a gurin shi ba, idan kuka/muka lura da shi da kyau sosai-sosai, zamu ga cewa shi yafi karfi kuma yafi daukar bangaren "Mutashabihaat", ma'ana duk wata mas'ala da zata kawo wuswasi da kokwanto, rudu da rudani a cikin addini, ayita ceceku akai, to shi yafi karfi a nan, hasalima shine yake kirkiro su, ga misalai k**ar haka:-
1.Yace ya halatta mace ta bada kanta (Fasikanci) domin ta samu na abinci
2.Yace daren mauludi yafi daren lailatul kadr
3.Yace duk wanda baya yin mauludi, to shi a ganin shi (Makari), ba musulmi bane ba
4.Shine ya kawo rudun hadithin (Khabaru ahaad, Zanniyyut thubut)
5.To gashi kuma yanzu ya dawo da gawar mas'alar Abduljabbar, wadda malamai s**a jima da yin Jana'izarta, wannan fa iyaka abinda na iya tunawa kenanfa, domin kuwa suna nan tuli/birjik
Gaskiyar magana, akwai tuhuma da zargi masu karfi a al'amarin karantawar wannan bawan Allahn.
Allah dai ya kyauta kawai, Allah kuma ya raba mu da birge mutane (Fans) domin neman yardar mutane, ya Allah ka raba mu asarar Imani saboda son yin Shuhura/trending.
MD Wadata Gama (Abu Abdurrahman)

الكلمة الطيبة صدقة

13/07/2025

Gagarumin Nasiha Ga MATASA Maza da Mata Tare da Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya

Sulaiman Nasidi ke nan, mabiyin Abduljabbar Kabara. Duk wani rashin tarbiyya da za ku gani daga wani shafi mai suna bege...
13/07/2025

Sulaiman Nasidi ke nan, mabiyin Abduljabbar Kabara. Duk wani rashin tarbiyya da za ku gani daga wani shafi mai suna bege TV to shi ya wallafa.

Ya ƙware wajen ƙagar ƙarya ya yaɗa, bai tsoron Allah bai jin kunyarsa.

Jaridar Alfijir da ta ƙirƙiri wata magana ta ce Sheikh Lawan Triumph ne ya faɗa duk daga wajensa suke kwafowa.

Babu wani malami da yake ganin kima a ƙasar nan ko a ɗariƙa ko a izala. Wannan ne yasa nima ba zan ji nauyi kafe hotonsa na bayyanawa mutane su san shi ba.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Malamai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muryar Malamai:

Share