09/08/2025
Ji nan, Ustazu.
Wallahi duk wani uzuri da su Musa Asadussunnah zasu kawo akan yin sulhu da azzalumin da bai fi ƙarfin hukuma ba, k**ar Bello Tirji, ba uzuri bane karɓaɓɓe. Bal ma wani nau'in uzurine na ɗaurewa zalinci gindi da nuna karaya da gazawa; sarayar da jinanen bayin Allah, da rarrashin azzalumai, da goyon bayan aikinsu a fakaice.
2. Uban me aka yiwa su Bello Turji da har s**a samu uzurin kashe al'ummar Annabi ba gaira babu dalili? Wane uzuri ne suke da shi na aikata ta'addanci akan mutanen da basu taka musu ba, basu zubar musu ba? Don me yasa za a sarayar da haƙƙoƙin bayin Allah Musulmi da s**a kashewa 'yan'uwa, s**a yiwa matansu fyaɗe, s**a ƙwace musu dukiyoyinsu haka kawai ba dalili wai da sunan sulhu? Ina hankali da ilimi yake a cikin irin wannan hukuncin?
3. Bana musu fatan musiba amma Irin su Asadussunnah, da zasu ɗanɗani ciwon da 'yan'uwan waɗanda su Bello Turji s**a yiwa ta'addanci s**a ɗanɗana, bilLahil Azeemi ba zasu so ko maganar sulhu a yi ba. Ku tambaye shi, yaya zai ji idan (Allah ya kiyaye) aka ce Bello Turji ya kashe masa ɗan'uwa, ya yiwa matarsa fyaɗe, ya sace masa ɗa ya riƙe sai da aka biya kuɗin fansa miliyoyi, sannan a ce yau gashi can an yi sulhu da shi yana yawonsa a gari yana sharholiyarsa ba a yi masa wani hukunci ba?
4. Wai su su Asadussunnah da suna da irin wannan ra'afar amma suke kasa yinta ga waɗanda suke kira 'yan bidi'a, waɗanda basu kashe kowa ba, basu sace kowa ba? Sau nawa ka taɓa jin suna neman sulhu da malaman da firƙarsu ba ɗaya ba? Wallahi irin zaƙalƙalewar da suke akan yin sulhu da 'yan'ta'addan dajin nan, da ita suke yi akan haduwar kan Musulmi da malamai da s**a sha bamban a fahimta da su, da tayi tasirin da a yau kan al'ummar Musulmi ya haɗu.
5. Idan ina kallon bidiyon yadda yake maganar yin sulhu da 'yan'ta'addan nan sai naji dama ba ba a malami yazo ba. Don wallahi maganganunsa sun fi k**a da na Data Boys din 'yan siyasa fiye da na malamai masana Allah. Yana bayanin tsigar jikina har tashi take yi saboda ƙyamar abinda yake faɗa. Ji nake k**ar na fuzgo shi na toshe mai baki. Eh! zage ni iya iyawarka, Ustazu, wallahi kasan gaskiya nake faɗawa uban dabarka.
6. Ga gaskiya da adalci ƙiri ƙiri amma idonsa ya rufe wajen samarwa da gwamnati da jami'anta dalili da hujjar tauye haƙƙin bayin Allah. Sam kalmominsa basa nuni da tausayi da adalci ga waɗanda su Bello Turji s**a zalinta. Ya karkata son zuciyarsa zuwa ga maslahar waɗansu mutane ya watsar da maslahar al'ummar Ma'aikin Allah. Tir wallahi.
7. Abin da ya dace da malamai na Allah a irin wannan lamarin a ji su da kaifi da gilza kwatankwacin yadda Malam Bello Yabo yake yi. A ji muryarsu tana ƙarfafa gwamnati da al'umma akan yadda za a yi maganin waɗannan azzalumai ta yadda nan gaba wani ba zai ji sha'awar aikata irin nasu ba. Amma kaico su Musa Asadussunnah ba su ɗauki wannan layin ba.
Wallahi sai Allah ya sakawa al'ummar Annabi matuƙar su Asadussunnah s**a jawo aka yi sulhu da su Turji ba a ɗauki matakin bin haƙƙin bayin Allah da s**a cutar ba. Idan ta yi maka zafi Ustazu, ka iya fifita zuciyarka da zage-zage. idan ma baka iya ba kazo Kango na baka training.
Mamman Naso