23/07/2024
TAYAYA AKA SAN DUK ABINDA YA FARU DA IMAM HUSAINI (A.S) BAYAN AN KASHE SHI TARE DA DUK MATAIMAKAN SA A KARBALA ???
-GYARA FAHIMTA (03)
Da farko dai kuskure ne fahimtar cewa duk wanda suke tare da Imam Husaini (a.s) a Karbala sunyi shahada tare da shi , kuma kuskure ne mu ษauka cewa a wurin iya wanda s**a zo kashe Imam Husain (a.s) aka samu labarin kisan sa da yanda ya wakana daki-daki , bari dai akwai wanษanda sun fito tare da Imam Husaini (a.s) amma basu samu rabon yin shahada a tare dashi ba , ma'ana dai akwai waษanda sun tsira kafin kashe shi wasu kuma bayan kashe shi , haka suma waษanda s**a zo a rundunar makasan Imam Husain (a.s) ba dukkansu bane suke da zuciya iri ษaya ta nasibanci misali , wasu tilas ce tasa s**a fito a matsayin su na sojojin Gwamnati , don haka amsar wannan tambayar itace : An sami labarin kashe Imam Husaini (a.s) da mataimakan sa da duk abinda ya faru a filin Karbala daki-daki ta hanyoyi k**ar haka :
1 . Waษanda s**a tsira daga rundunar Imam Husaini (a.s) saboda wasu dalilai mabanbanta bayan anyi musu rauni , k**ar Al-Hasanul Muthanna ษan Imam Hasan (a.s) da dangin babarsa s**a ceceshi a hannun makansa wanda su sun kasance suna cikin rundunar makasan , inda aka yi masa magani daga baya ya warke ya rayu , haka irin su Muwaฦฦa'u ษan Thumatatul Asdiy da aka ji masa rauni a rundunar Imam Husaini (a.s) daga baya danginsa Banu Asad s**a neman masa amana aka ribace shi zuwa Kufa daga can kuma Gwamnan Kufa ya koreshi daga Kufa.
Haka nan Dahhak ษan Abdullahil Mashriฦi shima yayi tafiyarsa ya bar Imam Husaini (a.s) , dama shi tun farko sharadi s**a yi da Imam Husaini (a.s) akan zai taimake shi idan yana da mataimaka a tare dashi in kuma ya zama shi kaษai ne to zai tafi ya bar shi a Karbala , haka nan irin su Uฦbatu ษan Sam'an duk sun tsira kuma akan idon su komai ya faru daga baya s**a bada labarin komai .
2 . Kashi na biyu kuma sune mata da yara da waษanda s**a rage aka ribacesu na daga Ahlul Baiti (a.s) k**ar su Imam Ali Zainul Abidin da Sayyida Zainab (a.s) da matan Imam Hussain da ฦดaฦดansa da matan wasu mataimakansa , suma sunga abinda ya faru tun daga fitowar su daga Madina da zaman su a Makka har zuwa Karbala.
3 . Sune wadanda suke rundunar Umar bin Sa'ad (L) Wanda suma sunga abubuwan da s**a faru , bari ma su suna da labaran da wata ฦila har wancen ษangaren basu dashi na abinda ya faru tsakanin kwamandojin su na yaฦi da wasiฦu da aike da aka dinga yo musu daga Kufa da duk irin abinda s**a aikata , shi yasa dayawan waษanda Mukhtar Assaฦafi (R) ya kashe daga cikin su yana fara tambayar su duk abinda s**a gani a Karbala da irin laifin da s**a yi kan ya kashe su irin su Harnalatu bin Kahilil Asdiy (L).
Kuma dama dai k**ar yanda muka faษa bawai duk wadanda s**a fito cikin rundunar yaฦar Imam Husaini (a.s) bane nasibawa maฦiya Ahlul Baiti (a.s) , akwai waษanda dole aka musu s**a fito a matsayin su na sojojin Gwamnati , akwai wanda son abun Duniya ne da waษanda kuma aka musu alฦawura na muฦamai akwai kuma wamda dama zamu ce ta tadda muje mu .
Daga waษanda s**a bada labarin waki'ar Karbala a cikin su akwai irin su Hamidu ษan Muslim wanda shi ya kasance k**ar ษan Jaridar labaran yaki ne shi yasa ya hakaito abubuwa dayawa da s**a faru a rundunar maฦiya Imam Husain (a.s) da Abdullahi ษan Ammar ษan Ya'aฦub, ฦurratu ษan ฦais , Zaidu ษan Ruฦฦad , Muhajiru dan Aus da Sa'adu ษab Ubaidah , wanda dukkansu sun bada labari na abubuwan da s**a faru da yanda s**a faru akan idon su .
Daga baya ne kuma Malaman tarihi irinsu Abu Mikhanaf , Asbag bin Nubatah da Aษษabariy d.s s**a dinga bi suna rubutawa har yazo garemu a yau .
Kenan hanyoyin da labaran waฦi'ar Karbala s**a zo har garemu yau suna dayawa sun wuce matakin tawaturi in akwai .
โ๏ธ Khadimul Ashrรฃf Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
https://t.me/tafarkintsiratv
15 / Al-Muharramul Haram / 22 / 7 / 2024 Miladiyya.