15/01/2025
LABARI MARA DADIN JI: A daren jiya, 'yan bindiga sun kai farmaki Asibitin Kankara da ke Ƙaramar Hukumar Kankara, Jihar Katsina, inda s**a harbe Dr. Murtala Sale Dandashire sannan s**a yi garkuwa da mutane biyar a asibitin.
Wajibi ne a ɗauki matakan inganta tsaro a asibitoci cikin Jihar Katsina. A cikin watanni uku da s**a gabata, an rahoto cewa 'yan bindiga sun kai farmaki asibitoci uku: Asibitin Kurfi, Asibitin Mai Tsani da ke Ƙaramar Hukumar Dutsin-ma, da Asibitin Kankara.
NB: Dr. Murtala Saleh Dandashire, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Kankara, shine dalibin likita mafi ƙwarewa da ya kammala karatunsa a shekarar 2019 daga makarantar koyon aikin likita ta jami'ar ABU Zaria mai daraja.