01/11/2025
(Minhaj al-Muslim) wanda Sheikh Abu Bakr Jabir Al-Jazairi ya rubuta
Shekara 12 da s**a wuce Baban mu Allah yagafarta masa ya bani shi Yana Daga Cikin muhimman litattafa da Mahaifina ya Dauka ya bani dakansa
Littafin Minhaj-Muslim yana koyar da cikakken tsarin rayuwa na Musulmi daga dukkan fannoni — addini, zamantakewa, da ɗabi’a.
1. Aƙeeda (I'tiqad) – Yana koyar da imani da Allah, mala’iku, littattafai, annabawa, ranar lahira, da kaddara.
2. ‘Ibadat (Ibada) – Yana bayyana sallah, zakka, azumi, hajji, da sauran ibadodi cikin sauƙi.
3. Akhlaq (Hali da ɗabi’u) – Yana koyar da kyawawan halaye, kamar gaskiya, tawali’u, haƙuri, da adalci.
4. Mu’amalat (Mu’amala) – Yana bayani kan mu’amalar yau da kullum, kamar kasuwanci, aure, ma’amala da mutane, da adalci.
5. Adab (Ladabi da Hanyoyin Zamani) – Yana nuna yadda musulmi zai rayu da mutane cikin ladabi da hikima a duk inda yake.
Manufar Littafin:
Sheikh Al-Jazairi ya rubuta shi ne domin ya zama jagora mai sauƙin fahimta ga duk musulmi — ko malami ne, ko ɗalibi, ko talaka — domin ya san yadda zai yi rayuwa bisa tafarkin Musulunci na gaskiya.
Sannan Wannan Littafi yayi Cikakken Bayani akan Zamantakewar Aure
A takaice:
Minhaj al-Muslim” yana koyar da cikakken tsarin rayuwa na musulmi daga akida har zuwa mu’amala, yana mai da hankali sosai wajen tarbiyya da tsaftar zuciya tare da fahimtar shari’a cikin sauƙi.
'Yan'uwa na Matasa mu Nemi Ilimi na Gaske
Mu Koma gun Malaman mu na gida Masu Sahihiyar Karantawa Ilimin ka Shine ke doraka Akan akidar da ta Dace
Allah Yajikan iyayen mu
Allah yasa mu wanye Lafiya.
Yakubu M Ibrahim ✍️