20/06/2023
Falalar Kwanaki Goman Watan
Dhul-hijjah
Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Falalar Allah ta na da yawa ga bayinsa, sabo da haka ne ya samarwa bayinsa lokuta na musamman don yawaita ambatonsa, da ayyukan kwarai, suna rige-rige a cikinsu, suna neman kusanci zuwa ga ubangijin su.
Kwanaki goma na Dhul-Hijja suna daga cikin mafi girman daraja a cikin lokuta na muasamman. Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya tabbatar da cewa sun fi sauran kwanakin duniya girman daraja.
Babu wani aikin ibada da yafi girman daraja fiye da a cikin wadannan kwanaki goma na Dhul-Hijja. Kenan bawa zai jajirce don yawaita ayyukan alhairi don
ribatan wannan kwanaki goma.
Ayyukan Ibada da Bawa zai yi a cikin kwanaki Goman Dhul-Hijja
Lallai ne bawa ya fuskanci wadannan kwanaki da ikhlasi a cikin ibadunsa, kuma yayi kwadayin raya kwanakin da ayyukan alhairi kamar haka:
1 – Tuba: Duk musulmi ya tuba ga Allah tuba na gaskiya, Allah ya ce : ku tuba ga Allah baki daya ya ku muminai lallai za ku ci nasara. (Nur:31)
2 – Nisantar Zunubai: Bawa ya nisanci sabon Allah, sabon Allah da zunubi suna nisartar da bawa daga rahamar Allah da yafiyar sa. Kuma Allah yana kuntatawa bayi sakamakon zunubai.
3 – Zikiri: kamar kabarbari, tahmidi da hailala, da sauran dukkanin ambaton Allah.
4 – Karatun Al-kura’ni.
5 – Biyayya ga iyaye, shugabanni, da malamai da sauran nagaba.
6 – Sulhu tsakanin mutanen da suke da sabani ko gaba.
7 – Kyautatawa marayu, makwabta, ‘yan-uwa da sauran al’umma.
8 – Ciyarwa da biyan bukatun talakawa da masu rauni.
9 – Ziyarar marasa lafiya.
10 – Azumi
11 – Sallah.
12 – Sadaqah.
13 – Layya.
14 – Hajji da Umra.
15 – Addu’a.
16 – Sada zumunta da sauran dukkanin ibadu.
FALALAR KWANAKI GOMA NA DHUL-HIJJA
1) Allah ya yi rantsuwa da kwanaki goman Dhul-Hijja a cikin suratul fajari sura ta 89 aya ta 1-2.
2) Sune kwanakin da ake kira “AYYAMIN MA’ALUMAT” (kwanaki sanannu) : Allah yayi umurni ga muminai da su ambace sa a cikin kwanaki sanan