16/09/2026
Remi Tinibu Ta Ba Maryam Ɗan-Azumi Da Ya Lashe Gasar Al-ƙur'ani Kyautar Miliyan 20
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yaba wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi bisa lashe gasar karatun Al-Qur’ani ta mata a matakin ƙasa da ƙasa ta Sarki Abdulaziz karo na 46 da aka gudanar a Makka, Saudiyya.
A yayin taron da aka gudanar a Abuja ranar Talata, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bai wa Maryam Dan’Azumi kyautar kuɗi har Naira miliyan 20.
Maryam ta halarci taron tare da mahaifinta, Ibrahim Dan’Azumi, da Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, da sauran jami’an gwamnatin jihar.